← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 138

Sashe 67

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayewa ta yi ta yi mashine wash da su , sai da ta gama wanke su ta fitar ta fito ta bude dayar kofar da igiyoyin shanyan suke ta je ta shanya su
Har ta juyo zata filo ta samu kanta da kurawa wajen abin fitila ido
Abin ta sake kurawa ido sosai tana kallonsa kafin ta juya ta fito falon daidai ya dasa aya yana rufe alkur'anin ya mike ya nufi wajen ajiyarsa ya ajiye sannan ya juyo yana fuskantarta domin ya tabata tsayuwar nan da ta yi magana ce a bakinta

Ajiyar Zuciya ta sauke tana kawar da kanta gefe ciki ciki ta ce" Am, am, am .............."

Kasa karasawa ta yi, shi kuma ya tsaya ya zuba mata ido har zuwa gaban goshinta da gargasar gashin wajen ke bashi mamaki
Idannuwanta ta dago ta dube shi sai kuma ta dubi hanyar da ta fito da hannunta ta dan nuna kafin ta kale shi ta dan shagwaba fuskarta tana sirintar da dubanta ta sake daukan duban nata ta sauke a hanyar da ta fito, hakan ya saka shi gane da abinda take nuna masa

A nutse ya taka ya zo ya gitata ya shige ciki, ya hara mata sansanyan kanshin turaransa da ya sakata lumshe idannuwanta ta bude ta raka bayansa da kallo sannan ta iya cira kafafuwanta da kyar ta bi bayansa

Wajen da ya fi dauke mata hankali ta yi ta nuna masa da idannuwanta har ya ga wajen shima
Tsakani da Allah zuwa yanzu ya amshi gayatar wannan neman fitina, zai kuma nunawa mai yi cewar ba sani bane bai yi ba so ya yi ya sirinta, aman tunda wulakancin ya kai haka zai kwatanta masa shi riga yake da ita wace ta bashi damar taka wulakantace!

Da idannuwansa ya mata alamun ta wuce

Wucewar ta yi sumui sumui ta fito a dakin gaba daya

Gannin yana biye da ita ya sakata dan yin sauri ta sauka ta nufi dakin Nahidt domin ta gama komai ta zuba abincinta ta yi shigewarta dan dama babu abinda zata yi jira ai, da gangan ta cewa Shuwwa a nan zasu ci, aman me zasu wani ci a nan? Ai du abinta ta san daidai ta san akasin daidan

A nutse ya bude ya biyo bayanta bayan ta shige

Salama ya yi a saman lebensa sannan ya daga kansa ya shiga bin dakin da kallo kafin ya dawo da dubansa kansu sun yi tsuru tsuru sunna kallonsa gaba dayansu a tsaitsaye

Dan gyaran murya ya yi ya ce" Ku shirya mu tafi"

Daga haka ya so ya juya, sai fai tambayar da SHUWWA ta masa da sauri tana kallonsa cewar ina zasu tafi? ya saka shi juyowa a hankali ya ce" Capital "

A tare suka maimaita Capital?, Yana nufin garin iyayensa kennan fa?, Sai kuma Shuwwar ta ce" Aman yaushe?, Kuma da wa da wa? sannan a me? sai nake gannin dare ya yi ai yanzun?"

Nahidt ta gyada kai domin itama so take ta san amsoshin nan har ga Allah

Dubansu ya yi daya bayan daya
Ko dan kwali yarinyar nan bata da shi a kanta, kuma abayar tata daga sama fa ta riketa sosai walahi

Kai ya girgiza yana sake kallonsu ya dubi agogon bangon dakin ya sake dubansu a kausashe ya ce" Now "

Daga haka ya juya ya fice a dakin, hakan ya sa suka kalli junna Shuwwar ta ce" Na ga annabi in na yi hali na gari, ke kuma me yakr nufi? "

Nahidt ta yi sakalau ta ce" Shuwwa ni na sani ne? Kin ga cewa ya yi Now, to yana nufin yanzun yanzu wai zamu yi doguwar tafiyar nan? Ko dai mutuwa aka yi ?"

Rai a hargitse SHUWWA ta💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 3️⃣7️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

*AUNTY SAJIDA NI FARA CE, MATSALATA BAYA KYALI, HAKA KUMA INA DA YARINYA DA NA HAIFA ITA KUMA TANA DA DAN DUHU KASANCEWAR MAHAIFINTA BAKI NE, DU IRIN SANYIN AC DA CIMA MAI KYAU BAMA KYALKYALI IRIN NA YAN GAYU, GAMU A GARI KUSA DA SHUGABAN KASA.......*
😂.............................................................................
Amsa " Dan gwada shafa madarar ruwa peak a fuskarki idan da hali har hannayenki, sannan itama ki gwada shafa mata kadan ba da yawa ba, da zarar kin bude ki saka a frij bata komai, idan kun shafa ku barta ta bushe sai ku wanke da ruwa kadai marar sanyi karara sannan marar dumi...........kyalin fata kike so? Zaki bani bayani yar uwa🥰🥰🥰🥰🥰🥰

Rai a hargitse Shuwwar ta ce" Koma menene ai sai a yi hakurin gannin safiya ko? Ni tsorona Allah tsorona kar cen zai kaini ya kashe ya birne ba tare da aj masa komai ba, kin ga tunda Allah ya hada hanyata da shi nake haye masa nake nemansa da fitina, ta yiwu na kaishi bango ne"......... Ta idasa da yannayi na son ta fashe da kuka , dukkan tsoron tafiyar na bayana a tatare da ita

Nahidt da ta juya ta fara harhada yan kayayakinta ta juyo ta ce" ki yiwa Allah ki daina fadin haka, yo idan ya kasheni ban auri Malan ba ina zan saka raina, kin kuwa san yadda nake tunanin gani gashi a matsayin mata da miji? Ki rufan asiri na mutu maza su kaini ba mata ba"

Kai Shuwwar ta girgiza tana tsaki tare da bala mata harara ta juya ta bara mata dakin ta nufi dakinta tana gunaguni

Cikin jerin akwatunnanta ta janyo wata galeliya ta ajiye ta bude ta firfitar da kayan ciki sannan ta shiga bude sauran akwatunnan tana duduba kayan da take gannin su suka dace da zaman cen, watau rantsatsu yan kasa da kasa wa'inda zata iya zama a kusa da kishiya da su

Haka kawai ta samu kanta da tunanin wai yanzu wajen da yake da wata matar zasu je su zauna?
Sai kuma ta yatsina baki tana ayana 'dadin abin ba damuwata bace , Allah ya sa uku zan tarda matsalarku ce kai da su'

Da gudu ta fada bayi ta yi wanka a gagauce, ta dauko brosh da su sabulu da maclean ta hado da tawul, da su abin busar da gashinta, kai su kayan kwaliyarta, su turarenta, ita dai abubuwan da ta tsaya yi sun dauketa lokaci mai yawan gaske domin sai da ta kusan awa biyu a ciki hakan ya sa dare ya karra yi, harma tana tunanin tabas an fasa tafiyar domin sun yi dare ai

Wando dogo ta saka ta dora farar riga mai dan dogon hannu sannan ta saka abaya mai botira a gaba marar kyalkyali ta dauko mayafinta ta yafa bata nada ba ta shiga wanke jikinta da sansanyen turarenta sannan ta dauki su cazarta, da turaran da take shafawa lokaci zuwa lokaci du ta zuba a jakar sannan ta shiga kiriniyar janyo sauran akwatunnan biyu ta fitar ta koma ta tofe dakin da adu'a ta janyo ta rufe ruffff da ky dinta ta jefa a jaka ta dakata tana kallon dakinsa
Gannin Ky dinsa a jiki sai ta bar akwatunnanta ta je da dan gudu gudu ta bude ta leka kanta
Gannin ba kowa ciki sai ta samu kanta da shigewa tana lelekawa
Ba kowa, ga abincin da ta kawo kamar an zuba tea din aman abincin ba'a ci komai ba

Leda ta shiga nema ko Allah zai sa ta samu
Ai kam ta ga irin ledojin nan na kampani wada ya sayi wani agogo a wani kampani ko agogon bai cire a ciki ba, hakan ya sa ta saka agogon a jakarta ta zo da ledar ta juye gashin nan tsaf da soyayen dankalin turawan nan sannan ta juyo da sauri ta fito bayan ta kule ta cusa a jakarta suma ta fito ta kuma janyo akwatunnan giri giri dadin abin daya ne takalmin da ta saka kafa ciki ne mai dan karamin tallon sosai, kuma ya yiwa kafar tata cif da cif hakan ya sa bata shan wahalar tafia da shi ta ringa saukowa da dan sauri ta juya ta janyo jaka daya sannan ta janyo daya da haka har ta idasa saukowa dana nishi ta janyo su ta nufo falon da take jin muryar NAHIDT na yar daria

Turus ta yi gannin Nahidt zaune saman kujera tana labari tana daria abinta shi kuma kamar ya samu TV sauraronta yake yana kuma kallonta sai a ransa da yake fasara dukan kalamanta
Chapter 67 · 0% Book details