Sashe 71
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
A sanyaye Father ya ce" I'm sorry "
MUHAY ya kalle shi da mamakin jin furucinsa
Father zai sake yin magana wani yaro almajiri ya shigo da salama ya duka ya ce" Aba wai maman su Ummi ce ta ce ka zo da gagawa ana fada a gida."
Da mamaki suka kalli almajirin sai kuma zunbur Father ya mik'e yana maimaita" Fad'a kuma?"
Kafin yaron ya bashi amsa har ya kusa fita a masallacin inda MUHAY ke take masa baya saidai tafiyar a yannayi na takama yake yin ta da k'asaita.
Suna shiga gidan idonsu ya sauka kan Umma babar yar Chief of army da uwar gidan MUhay sun kacame junnansu suna dakuwa, wanda ba komai ya jawo haka ba sai labarin da ta ji a bakin mahaifiyyarta cewa ai yau wani wulakancin da suka tashi da shi a gidan nan Muhay jiya ya shigo da matar da ya aura a cen harda yayarta, wannan lamari ya tunzurata ta fito a shiryenta dan ta je ta ga sabuwar yar shigen sauri a fadar da ba tata ba
Had'ewa sukayi da uwar gidan Muhydeen wacce ta shiga jifanta da wani mugun kallo, bata damu da ita ba dan ba ita ce a gabanta ba, har ta d'an wuce cike da izgili tace "Iska dai na wahalar da mai kayan kara, sai rashin zuciya kamar kazar da bata jin as"
Tsayawa tayi tare da dawowa baya ta shiga kallonta a kausashe tace "Bana jin ni da ke muna da bambamci indai a wajen MUHAY ne, dan ga dukan alama ke ma iskan wahalar dake yake sakamakon dakon kayan karmami da kike yi"
A hassale kamar mai jiran tab'i tace "K'arya kike wallahi, dan ko ba komai ni ina amsa sunan matarsa, ke fa ? A cikin gida kike ke ba karuwa ba kuma ba cikakkiyar mace ba mai daraja ba, ke kulun kina jira ki ga motsinsa"
Cike da neman fitina da rashin wayo Umma tace "Sai dai in uwarki ce karuwar amma ba ni ba, jaka kawai, ita matar so d'in ai gashi ya taho da ita har nan, ke fa ballagaza kina zaune ki.."
A tsiyace ta dafe k'irji tace "Ni? Uwata kike fad'ama karuwa?" Ta katse maganar Ummar
Cike da rashin aji da d'aukaka martabarsu ta 'ya'ya mata sai kuwa suka had'e jikinsu da sunnan dambe wanda sam ba tsari a hakan face zubar da mutumci, musamman ma a wajen uwar gidan Muhay wacce da ta san darajarta da kimarta ba za ta yi fad'a da wacce ma ta amsa sunan matarsa bare kuma wannan.
Uwar gidan Father ce ta fara fitowa tana neman rabasu da kwaroroton zancen tana daukaka maganar har maman su Ummi itama ta fito wace ta kwana bata rintsa ba itama da nata kalar bacin ran ta ce "Kai! Kai me kuke yi hakane? Ku saki junanku."
Ba wacce ta san tana yi in banda dambatuwa da suke, sake bud'e murya tayi tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Na shiga uku na lalace, wannan wace irin masifa ce ? Ku kenan kullum a haka akan namiji...wai za ku bari ko sai na had'aku da Chief?"
Duba da babu wacce ta kula da ita yasa ta kada daya daga cikin sojawan dake bada tsaro kan maza ya kira mata CHIEF duda ta sani sarai dokar gidan ba'a aikensu ko nan da nan
Maman Ummi na gannin haka ta hanna ta nufi almajirinsu mai yiwa yaren dan aika wanda sunne suka dauke shi yana ta faman share wajen flowers d'in nan ta turashi ya kira Father.
Father na k'arasowa a tsawace yace" Kai meye wannan kuma!"
Umma ce ta fara kiciniyar raba jikinta da ita tare da dafe kunnenta daya had'e da rigarta, a hankali suka raba jikinsu sai huci suke uwa wasu zakuna suna ta k'ok'arin gyara kayan jikinsu duk sun cimimiye.
Matsawa Father yayi saida ya je gaban Umma ya d'aga hannunshi ya wanke fuskarta da mari, razananniyar ihu ta saki tana d'agowa ya kuma zuba mata wani marin, cikin tsananin b'acin rai da takaici ya juya ga sojawan dake tsatsaye suna kallon ikon Allah, tun farko sun so raba fad'a to amma duk mata ne ba zasu iya kama jikinsu ba, bare fad'an mata da kan k'asa ake kai nushi sai a samu d'an rabo ba gaira ba dalili ga cizo da yakushi, nuna musu Umma yayi a hassale yace "Kai ku d'auke ta ku kai min guardroom d'in nan, sai na tabbatar tayi hankali koda zata fito."
Ya k'arashe da kallonta yana zabga mata harara yace "Yar iska kawai."
Uwar gidansa da abun bai zo mata yanda ta so ba rufe baki tayi jin ya b'aro wannan zagin, dan a saninta da shi ba ma'abocin haka bane, ga kuma wani tashin hankali wai a kai Umma guardroom, to a kan me?
Umma kam fashewa tayi da kuka uwa jiniya ta durk'ushe tana fad'in "Dad ka yi hak'uri dan Allah ba zan sake ba, wallahi ba laifina bane."
A harzuke Father ya nufi part d'in shi ba tare daya kula kowa ba dan idonshi a rufe suke da b'acin rai, ita kanta ba dan yana kallonta a matsayin sarakuwa ba, da sai ya falla mata marin dan ta gane ba'a masa haka.
Shuwwar da Nahidt da ke tsaye kusa da juna wannan hargagin ne na uwar gidan Father ya fito da su dan ko baccin su basu gama ba, dan Shuwwar ma kayanta na jiya ne da ta cire doguwar rigar da ta kwana da ita ta saka su domin sun bushe yanzun watau farin dogon wando da farar riga mai dogayen hannu kanta ko d'an kwali babu sai ribom d'inta daya kusa fita a kan ta.
Mama ma na gefe tsaye da carbinta a hannu dan tana kan sallaya ta ji wannan tashin hankalin ta fito, kallonsu take ranta na k'ara b'acewa da tunanin me yasa suke aikata haka? Me yasa suka kasa zama mata ne? Me ye anfanin banzatar da mutumci da kimarsu akan wanda ko damuwa ta ainihi baya nunawa a kan muradinsu ? Ribar me za su samu yanzu bayan k'ara tusa masa tsanarsu da d'abi'unsu, dan a yanda ta san d'anta ba mai hayaniya ba abinda sukayi yanzun zai sa ya musu kallon hadarin kaji ne sannan ya ba banza ajiyarsu
Ai kam dai abinda Mama ke rayawa ne ke faruwa, dan tunda suka shigo tare da Father idonshi ya sauka a kansu da k'alak'antan da suke da maganganun da suke fad'a, sai ya fara jiyo k'amshin dalilin fad'an kam shi ne, sam a zuciyarsa ya ji hakan bai dameshi ba, sai dai abu d'aya da zai iya cewa bai ji dad'i ba a matsayinsa na namiji mai kishi shi ne, yanda matarsa ta aure ke dakuwa da wacce zai iya cewa k'anwarsa a gaban wasu k'arti masu kaki, sai yake hango da fa wata ta cirewa wata kayanta? Idan fa sun yaga tufafin junansu? Bayan ba shirin fad'an sukayi ba, shikenan asirinsa ya tonu kenan, duk da bai da tabbacin gaurayarsu amma dai ai tana amsa sunan *mallakinsa*.
Tun wuri ya gaggauta d'auke idonsa a kansu, sai dai me? Idan har ya fahimci rayuwa daidai zai iya cewa duk tashin hankalin da ya sameka a bazata, sannan ya zo maka a baibai ya fi d'aga maka hankali fiye da komai, dan kuwa wacce aurenta ya zo masa a bagatatan, sai gashi ita ce ta fi tsone masa ido a tsayuwar da ta yi da kuma tufafin jikinta.
Lokaci d'aya ya samu kansa da rarraba ido kamar marar gaskiya, yatsina fuska yayi ya sake kallonta amma ko a jikinta, to dama ta ya zai dameta bayan da gangan ta fito? Amma dai ko ya ya ta tayasa kare martabarsa mana, yanzu idan sun gama k'are mata kallo fa? Kenan shi ya tashi a sakarai d'an a bi yarima a sha kid'a?
Guardroom d'in da Dad ya ambata ne ya dawo da shi daga duniyar b'acin ran da ya tafi na tunani, ganin Dad d'in ya nufi b'angarensa ya sa ya ma d'aya daga cukin sojojin da yake tunkaro Umma dan son cika umarnin Chief d'in alamar ya tafi ya barta,
Da kai ya amsa masa shi ma alamar "Ok sir."
Ratsawa ya yi tsakanin Umma dake durk'ushe da uwar gidansa dake tsaye tana ta gyara rigar shaddarta wacce ita a shirin had'uwarsu ne tayi da sanyin safiyar nan. Ta tsakiyarsu ya bi ya wuce fuskarshi a mugun d'aure ba tare da ya ko had'a ido da ita ba
Baki bud'e ta bi k'eyarshi da kallo sanda ya isa kusa da Shuwwa ya damk'o wuyan hannunta ya kuma fizgeta ya jata zuwa b'angaren Mama, har saida Mama da Nahidt suka bi bayansu a dan guje dan a yadda ya damki hannun nata ta yiwu bai fahimci ba da ita ake damben ba, ita kuwa matarsa ba ta daina kallon hanyar da ya bi ba, wato a banzar bazara ya d'auketa? Ko ya ma kalli fuskarta kamar dai babu halittarta a wurin? Me kenan?
Uwar gidan Father ce ta fara k'are mata kallo kamar ta fashe da dariya sannan ta juya ta bar su nan, Umma ma mik'ewa tayi tsaye ta kalleta tana share hawaye, wani murmushin mugunta ta mata tace "Kin gani ko? Ke da banza duk d'aya, gwara ma ni tunda na samu alfarmarsa, kuma baki ga an min auren ba tukunnan, komai na iya faruwa tunda bai cikashe ta hudu ba "