← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 138

Sashe 23

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga kan takalmin da ya gani na namiji a kofa ya dakata ya so juyawa
Sai dai tunawar da ya yi a message din NAHIDT tana nufin SHUWWAR ta dawo gida da wani tukiten sakin ne ya saka shi tunkaro gidan kai tsaye tun bayan dawo da su da ya yi ranar da aka kai SHUWWAR dakinta
Ya sani sarai irin yadda jama'ar anguwar ke mamakinsa, wasu a cikinsu sukan ce anya kuwaa malan?, Wasun kuwa gwa da gwa suke nyna masa cewar yana iya zubar da mutuncinsa idan har ya ci gaba da dorar da mu'amalarsa da wadinnan yan matan, dadin abin ba su kadai yakr bawa kulawa irin haka ba , kasancewar akoy wasu gugun samari da suka kafa zama irin na rashin da'a suke shuka abubuwan da suka ga dama, sai ya kasance yana shiga cikinsu yana jan ra'ayinsu cikin hikima, domin takanas zai je ya ce da shi za'ai zaman, zai zuba kudi a yi dahuwa a ci sai ya ce me zai hanna yau a yi tilawa koda ta sura biyar ce a cikin Alkur'ani ? Hakan zai sa ko me bawa ke yi Allah zai karre shi
Cikin hikima yake tafiyar da su, cikin dabara suke yin komai su wanye lafia, a yanzu ci gaban da aka samu a wajen samarin nan ba kadan bane, domin sun zubar da makamansu sannan sun daina cutar da y'ayan mutane, uwa uba a yanzun idan wani na cikinsu ya aikata aiki na lalata sunna za'a hukuntashi ne, sannan da abinda Allah ya hore masa yana taimakawa wanda ya ga da gaske zai nema, haka kuma yana kwadaita masu hannu da shinin anguwar sunna talafawa matasan sosai, hakan ya sa yanzu anguwar matasan nan sun zame mata garkuwa, ba dai ba a shigo masu da wani tsageranci, sace sace kuma ba dai a cikin anguwar ba,
Bai san ko dan su NAHIDT na mata bane ake nuna kar ya talafa masu? An cika zurfafa tsanarsu a bayane, fatansa suma su samu mafaka
Sai dai abinda yake tsorata shi she ne ALKALAMIN KADARRAR SHUWWAR din, Allah ya saka mata son yin auren a ranta, samun mazan take yi ta azalzala kan sai an aura nata kamar fitar rai, yanzun dai da kannanun shekarunta aure auren hudu, kuma ana sakinta ne da saki irin na son zuciya

Gyaran murya ya yi kadan ya sake yin salama

Muryar da ta amsa masa ta sake saka shi zubawa mutumen dake zaune wanda ba zai kireshi kai tsaye da saurayi ba, kun san idan farin mutun ya dan fara kwana biyu baya buya, ko yayane ana ganewa shi yasa a bayane ake gane shekarun HAMZA domin Hamza dama ba mutun bane mai kula da lafiyarsa da irin sport da sauransu

Murmushi ya sakarwa Malan yana mikewa hadi da tarbo shi yana mika masa hannu yana fadin" Masha Allah masha Allah, NAHIDT bako muka yi ne?"

Da NAHIDT din, da SHUWWAR din, da Fauziya du sai suka sha jinnin jikinsu jin furucin Hamza, uwa uba kallon da Malan ya sauke masu su su dukansun hakan ya sa Shuwwar yin kiri kiri tana tunanin kar dai ya cr a gidan giya suka hadu da shi, bata san me Aba zai ce ba

NAHIDT kanta sai da ta dan karkata kai sannan ta turo baki tana cire kanta a kuretan da ya yi da kallo kasa kasa sosai tana fadin" Allahn da ya sa mutun ba ubana bane!"

Kallonta yake yi, shi yasa dukan furucinta ya gane ba na zaman lafia ta yi ba, duda ba zai ce ga abinda ta fada din ba domin shi dai bai iya karanta furucin kan lebe ba

Dan Murmushi ya yiwa Hamza yana fadin" Masha Allah, sannu fa bawan Allah"

Hamza abinda yake fadin a kasan zuciyarsa shine'Allah ka sa wannan dai ba saurayinta bane, domin bana tunanin idan wannan a gabana wannan yar budurwa zata dube ni' sai dai a bayane sam bai nuna ba, ya dauke hirar da wasa da daria ta yadda har Malan ya kai zaune yana amsa gaisuwar su biyun dake gaishe shi bai daina dan yiwa malan din sannu da zuwa ba

Bayan zamansa bakinsa ya ja ya dinke kamar yadda ya dakatar da komai da yake yi
Ido ya zuba masu ta yadda ya karanci kowanensu
Shi dai namiji ne sannan mutun ne mai mu'amala da mutane, hakan ya sa a irin abinda Hamza ke yi ya gane inda akalarsa ta dosa
Sannan ya gane halayan Hamza a dan kankannin lokaci
Warau Hamza irin mutanen nan ne da waje baya masu wahalar shiga, sannan sukan saba da mutun koda yanzu suka hadu
A irrin masu halayan hamza akoy mugwayen cikinsu, daje shiga cikin mutane da dariyarsu da hakaya irin na sabonsu su cutar da mutanen su yi tafiyarsu ta yadda sai dai idan an je lahira ne wata shara'ar zata tabata,
Sannan akoy wa'inda haka suke, su kowa nasu ne, kuma da zuciya daya suke tare da kai
Hakan ya sa ya zubawa Nahidt ido da ya kula lalle lalle wannan bako ya gama siyan yardarta ta yadda take bashi amsa da zarar ya budi bakinsa sannan ta yi daria a dukan shirmen da zai fitto daga bakinsa

SHUWWAR dake tsarge har yanzu ta ce" Aba, wannan Hamza ne"

Malan ya kalli Hamzan a Karro na ba adadi a nutse ya ce" Na gani "

Daga na gannin bai kuma furta komai ba, sannan ya hade fuskarsa ta yadda shi da kansa Hamzan jin ta ce Aba duda da kamar wuya ace wannan mahaifinta ne, aman sai ya sake kama kansa , harma ya ringa sada kansa irin ka zo gaban sirikinkan nan

A tausashe kamar yadda ya iya mu'amalantar mutane ya kalli su NAHIDT yana nunin alamu na son karrin haske ya ce" ABA ne?"

NAHIDT ta hadiye yawu ta ce" Eh to Abanta ne, shine wanda yake........."

"Eh abanta ne ni" ya fada a tausashen shima yana katse bakin yar neman sannan ya sake kure yannayin Hamza da kallo, abin ya dawo daidai da namiji a namiji ne

Daga saman kujerar da yake zaune ya dawi kasa yana sake sada kansa ya ce" Masha Allah, Aba barka da warhaka......am ka yi hakuri dan Allah, Ban sani ba kaine Aban, dama jiya nine na hadu da ita a cikin wani irin yannayin da ya sakata ta je gidan Giyar dake anguwar................"

"Ba ba sai ka fadi nan ba, Aba wannan shine ya taimake ni jiya ya kawoni gida, yanzun dai ban san meye mu'amalarsa da aunty ba na dai farka fitowata kennanma daga daki na same su a haka, daga haka ban san komai ba" ta fada da dan gagawar dake nuni da bata so Aban nata ya san daga ina ya samota, hakan ya sa Nahidt da ta zabura jin ta juye laifin a kanta ita da take ikirarin bata wani Tsoronsa ta ce" Ke ki ji tsoron Allah yarinyar nan a kan me zaki ce kika tardo mu bayan ta dalilinki muka sanshi? Fauziya dan Allah mun sanshi kafin yau ne?"
Daga Fauziyar, har Shuwwar, har Malan din sun yi mamakin gannin yau NAHIDT na gudun aa dora mata laifi har tana kare kanta da dukan karfinta

SHUWWAR kam sai ta sada kanta tana hade yan hannayenta tana sauke ajiyar zuciya

Shima Hamzan sai ya samu Kansa da jin sha'awarsu, ashema sunna da alkibla? Ba kwata kwata bane suka bace? Ashema sunna da wanda ke tsawatar masu?

Malan ya maida dubansa kan Hamza ya yi dan gyaran murya yana fadin" Bismillah malan ina sauraronka a wani gidan giya?"

Sai da cikin Shuwwar ya juya, ta karra sada kanta sosai tana sauraronsa ya dora da fadin" bata sha ba, ta siya aman ta kasa sha, domin koda ta saurari shawarata bata yi niyar shan bane, domin da ta yi niyar sha din ba zara iya tsayawa dan wata maganata ba, daga nan ne na daukota na kawota gida, sai kuma tun da safe da na yi safiya na dawo"

A tausashensa ya ce" Wani abu ka manta ne?"

A hankali ya girgiza kansa ya karra sada kan nasa ya ce" Ka yi hakuro Abanmu, idan har shi ya saketa ni ina sonta, zan kuma aureta na zauna da ita da zuciya daya"

Murmushi NAHIDT ke yi tana gyada kanta ta ce" Kai abu ya yi kyau"

Harare Malan ya maka mata yana cire kansa ya maida kan SHUWWAR ya ga bata dago kanta a yadda yake ba, ya sake kallon Hamza ya ce" Ko zan iya sannin dan tarihin malamin?"

Hamza , mutun ne da bai iya boye waye shi ba, haka kuma baya jin kunyar hakan, Hamza bashi da boye boye nema sam a rayuwa, hakan ya sa ya ce" Ni dai sunnana Hamza, Ni haifafen garin Tanus be, Aba ni dai shege ne, domin bani da uba a yadda marikina baban sojan nan da ya yi retaya aka fada masa da na matsa masa ya fada min gaskiyar lamarin ana cewa ba shine ubana ba bayan ni kadai ya malaka? Ana cewa ni din ai shege ne, sai yake ce min....................

Tunda ya ce shi shege ne, gaba daya dakin kowa ya dago yana masa kallo irin wanda ya zo cikin zuciyarsa, ba ga Malan din ba ba gaa y'ayan nasa ba, shi kuma a nutse yake basu bayani ya ci gaba da fadin"
Chapter 23 · 0% Book details