Sashe 86
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali Shuwwa ke girgizawa Mama kai tana kallonta ta ringa harhada abinda zata fada mata duda ta san da wahala ta yarda da furucinta, ita kanta wannan abin ya bata mamaki har yanzu kallon jan da ya mata take yi a idannuwanta, da kuma irin kallon da matar ke masu, abin na son ya dan tsaya mata a rai, aman kuma bata ga dalili ba shi yasa ta fuskanci Mama ta ce" Mama ni cikina ne ya murda min har na fara kuka, shine ya rikeni dan na daina kukan, shine maman itama take min sannu"
Mama ta kure fuskarta da ido, kwarai ta san maganar ba haka bace, aman sai ta samu kanta da son yarda da maganar fiye da sake saken banzan da take yi a zuciyarta, dan haka sai ta ringa sauke ajiyar zuciya itama ta sauko kasan saman tabarmar suka zauna suka zubawa hanyar shigowa ido kowace abinda ke zuciyarta ya fi karfin ya barta ta yi hira a bayane koda kuwa da gangan ne
______________________________________
😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍ALK'ALAMIN KADARATAH
Na
*Sajida*
Page
4️⃣9️⃣
Jan hannunta yake , tana biye da shi tamkar zata kifa domin saurin ba daya ba, haka kuma karfin ba daya, a haka a wulakance har ya samu ya samu dogon corridor din da yakan zama idan ya kawo marar kafiya ya buya a nan ya turata har sai da ta daku da jikin garu kafin ya tsatsareta da idannuwansa da sukai jajajir yana kallonta
Da bacin rai yaa shiga magana yana dago hannunsa da ya wara ya jimke yana fadin" Ki kula idan zaki fuskanci mai daraja ki yi mata magana, ki kiyaye harshen ki wajen yi mata furuci domin kalma daya na iya laladan sauran farin cikin da kike tunanin kina da shi a rayuwa!, Useina ki kiyaye tsawarawa mahaifiyata, domin idannuwanta dake akoy a doron kasa ya saka ban daga ki na murzaki a kas na!, Useina kin zubar da dukan wata kima da nake iya daga maki kafa dominta, ina kauce maki irin ranar nan da zan maki irin wannan kashedin!, Ki kiyaye! Useina ki kiyaye ! Kar ki kuma kiran number wayata, kar ki kuma hadani da mahaifiyata cewar bana zumunci da ke, idan kika kuma zan hadaki da yan barikin daa zasu fitar maki da bariki a ranki, Useina idan kika kuma gigin neman haramci da ni zan goge fuskarki a samab kwalta kafin na dauke kanki da bindiga!, Ki karata da kwaratanki sun isheki , da izinin Allah ba zan yi lalacewar nan da kike burin ki ga na yi ba, ba dai da ke UWATA ba!" da karfi ya karashe maganar yana mai doka hannunsa a jikin garun wanda ita da ya doka a kusa da ita, ita ta tsorata da haka harma ta yi gagawar rintse idannuwanta jikinta na rawa a tsorace ta sake kallonsa da idannuwanta da suka cika da hawaye, bakinta na bari ta ce" Muhay, yaya zan yi? Kadarata ce soyayarka"
Da wani bacin ran a amon muryarsa ya ce" Ki saurara haka, da nake daga maki kafa ban titsiyeki ba ba dan komai bane sai dan jin kunyar zumunta, kadara? Ke taki salon kadarar lalle ina jinjinna mata, kadarar taki ce son kowani gara? Ke Useina yara kannana kike mu'amala da su, mu'amala lalataciya, kin dauka ban sani bane? Ki ce MUHAY kai din son zuciyata ne na yarda wanda kike so ki baje a saman bed dinki zan yarda aman ba kice min ni kadararki bane, ni son zuciyarki ne Useina wanda aikata aikin banza ya saka kike jin sha'awata, ilar aikata aikin banzan da kike yi kennan Allah ya saka maki kwadayin abinda yake guba a gareki, Babar matsalar kuma bayan shirme kin fara hauka a kan lamarinki, USEINA ba zan taba kasancewa mai yi maki biyaya ba ko ki fahimta ta laluma ko duniya ta ganar da ke!"
Daga haka ya matsa ya juya ya barta a wajen, wanda barin nata da ya yi ya sakata dukewa a wajen tana cire dan kwalinta hadi da sakin kuka tana mai rukunkume hannun nata a jikinta
Da dan karfi ta ce" Sai dai ka kashe ni, kana tunanin tunda na tunkari kowa da maganarka zan ji tsoron birgarka ne?, Kennan har dauka kake soyayarka da bukatar da nake biyawa kaina da wasu mazan daya ne?, Zaka gani, yadda ka kawo har yanzu baka mu'amalanci mace ba, ba zaka taba mu'amulantar wata ba, ko yar gidan uban waye!"
Sai da ta ci kukanta sannan ta mike da dan kwalin ta nufi ciki ta nemi wajen ruwa ta kunna ta wanke fuskarta sosai ta gyara daurin dan kwalinta sannan ta juya da niyar fara isar da sakonta a yau yau ba sai gobe ba!
A lokacin da ta shigo Mama ta gama sallar la'asar kennan Shuwwa na tsakar yi ta karaso da sauri ta zauna a kusa da yar uwarta ta riko hanneyenta ta fashe da kuka
Kukan da ya saka Mama zabura a tsorace tana kallonta
A gigice Mama ta shiga fadin" USEINA menene? Tun dazu na fita na nemeku sama ko kasa ban ganku ba menene? Kukan me kike? Ina yake ne?"
Useina ta sake waigawa wajen da SHUWWA ta kai sujadarta ta karshe ta ce" Yanzu Hasana dama SON zai yi auren matar da saboda ita zai nuna min komai na iya faruwa idan har ban fita a harkarta ba?, Dama zan ga irin ranar nan?"
Mama ta kalleta a hankalce ta ce" Useina kin ga, ki nutsu dan Allah ki fada min me yake faruwa yau kuma?"
Useina ta sake yin yadda ta saba dan ta hauda Maman da sirikanta, ba kunya ba jin tsoron Allah bale na Muhay da ya gama ja mata kashedi ta ce" Tunda na shigo dakin nan yarinyar nan ke kin wani irin kallo, tunda ta ji kin yi maganar rigar jikina ta dameni tana gannin kin fita ta ce da ni kamar yar bariki?, Ta dora da fadin bama kama bane yar bariki ce ni, raina ya bace na budi baki da niyar yi mata magana shikenan Son ya tare ya hanna, hakan ya bani mamaki na tsatsareshi da ido uwa uba a gabana ya rukunkumeta ya shiga kissing dinta, Hasana da kika shigo ya saketa ya jani ya gindaya min kashedin a kan matarsa yana iya yanke zumunci da ni kwata kwata, cewar a kanta babu abinda ba zai iya yiwa kowa ba ciki kuwa harda ke da kika haife shi, ya ce yana iya zabarta ya bar kowa, in ina gardama na tambaya ina tsohuwar matarsa?, Hasana kina kallo ya sake auro mana masifa?"
Irin kallon da Mama ke yi mata dole ya saka mutun a cikin tunanin fasarar kallon
Mama ta tsareta da duban nan ne tamkar tana son gane ita din wata irin halita ce?
Tsoro, tashin hankali kala kala suka ziyarceta,
Tabas abinda Shuwwa ta fada bata yarda da shi ba domin maganar da ta fada sam karyar bata tsaru ba, ta dai hakura ta bar maganar a haka ne dan ta cire wasi wasi da shakun dake cikin zuciyarta
Sai dai a yanzu wanda kanwarta ta fada ya sakata a cikin tashin hankali
Gaba daya maganar da ta fada tana iya zamtowa gaskiya duba da a saman Shuwwa din ta shigo ta same shi, sannan a gaban idannuwanta ya damki hannun yar uwarta ya fita da ita, bayanma wannan a kan wani dalili zata yi masu karya ne? Shin da gaske ne abinda ta fada cewar MUHAY ya fada a kan Yarinyar nan?
Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi har kunnayenta suka jiyo mata salamewar sallar Shuwwa ta juyo da sauri baki da hanci a bude tamkar zata hadiye su da su tana kallonsu da mahaukacin mamakin da ya ki buya
Ta san bata da bakin da zata taro maganar nan, da farkoma ita ta saka kanta a cikin ramin nan, anya kuwa tana iya fitar da kanta?
Mama dake kallonsu jin zuciyarta zata buga ya saka ta mike da sauri ta nufi hanyar fita ba tare da ta yiwa kowa magana ba, wanda hakan ya daka Shuwwa mikewa da sauri da niyar bin bayanta, sai dai riko mata mayafi da akai aka dawo da ita ya sakata juyowa da sauri tana kallon matar nan da fuskarta ta zame mata tamkar ta kumurci
Yar dariya ta yi tana kallonta ta ce" Dama kin yi hakuri kin anfani kyanki ta hanyar da ta dace da ke, da kin guji zakin da ba mahadin Barewa ba to da ina iya yi maki hanyar da zaki mori kyan naki......kina neman yiwa al'amarin da baki da ci a cikinsa shishigi? Meye mahadin hanyar mai cin ciyawa da mai cin nama? Uban dawa yake sai zakanya zata iya da shi ba ke ba!"
Tana gama fada ta zo da niyar wuceta ta tafi, sai dai abinda ya dakatar da ita jin muryar Shuwwa wace ta cika da mamaki da bugawar zuciya tana kallonta ta ce" Ji mana?"
Dan dakatawa ta yi ta juyo tana kallonta da cikaken rashin tsoro irin na rikakiyar yar bariki tana kallon Shuwwa din da jin wata magana ta rainin wayau tana neman yi mata wai ji mana?
Shuwwa ta dan sake dubanta tana kiyasta shekarunta a zuciyarta a nutse ta ce" Mama?, Sorry wacece zakanyar? Wacece barewar?"
USEINA ta yi wani yannayi na ta dan shaka kadan kafin ta dan girgiza kanta a kausashe ta ce" Kece Barewar, da kike nama a gaban zakanya, watau ni!, Da zaki yi biyaya zaki iya tsira da mutuncinki?"
Tabas bata yi hasashen jin cewa Useina ce zakanyar ba, ta zata ko y'arta take YIWA yaki, sai dai da ta fadi hakan kamar ta gaura mata mari ne, domin sai da ta ji kamar zata kifa kafin take iya rike kanta tana kallonta ta ce" Mama, wai ke Zakanya a matsayin uwar zaki kike nufi bakya so danki zaki ya rabi Barewa ko yaya fahimtar da ni?"
Haushi ya saka Useina nunata da yatsa ta ce" Ke saurara min, ba shirme ya tsayar da ni a nan ba, idan baki fahimta ba zaki gane !"