Sashe 78
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kyar ya iya barinsa a tsaye bayan ya rufe idannuwansa kam ya ce da shi yana zuwa yanzu yanzunnan su fita a dakin
Yana fitowa ya kura masu ido gaba dayansu, balema matarda da take dan dingisawa da kafarta da aka daura mata bandeji baba sosai
Dan gyaran murya ya yi yana kallon likitar ya ce" Docter ki yi kokarin sake masa wata allurar barcin ba mai nauyi ba ina dawowa
Daga haka ya juya ya nufi office dinsa sannan ya bada damar a kawo matar
Tunda ta zauna a saman kujera jikinta ke dan rawa, kanta a kasa, gaba daya hankalinta a tashe
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juyar da kansa da yaren buzanci ya ce" Su wanene ku?"
Da sauri ta dago kanta tana kallonsa jin ya yi yarenta sannan yana tambayyarta su wanene su
Harshenta na rawa ta fan girgiza kanta tana fadin" Mu ba kowa bane, mijina mahaukaci ne, ni kuma almajira ce, mun gode da taimako ku salamemu na maida shi wani wajen mu labe, in sha Allahu ba zaku kuma ganninmu a garin nan ba"
Kansa ya gyada bayan ya dasa aya ya ce" a wani dalili ne za'a hanna ku zaman kasa bayan yan kasa ne ku? Ko ku ba yan kasar nan bane?"
Hannayenta ta dan dora saman cinyarta, a yannayi na gajiya ta kale shi tana danne lebenta dake rawa ta ce" Yalabai........"
Da sauri ya kurawa fuskarta ido da sunnan da ta ambata yana kallonta
Da muryar kukan da ta fashe da shi ta dora da fadin" Yalabai ni ban gane komai ba, na kuma kasa gane komai, Yalabai daga fita dan zuwa sallah ta bamu sako wani gida kusa da mu, shikekan sai a nan muka tsinci kanmu, ana gana mana azabar da ban san laifin da muka aikata ba sannan tunda muka sako kafa ya haukace, Yalabai ni Uwa ce, ban san a ina suke ba, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une ina rayuwa a haka ban san a mace suke ko a raye suke ba, a wani hali suke ne?, Yalabai ina son komawa ba hali ba hanya, mijina ba lafia ga hauka a daure yake idan ba haka ba ya ce zai fita da gudu, wayo Allahna na tabata abinda na aikata ke bibiyata, bani da kowa sai Allah , dan Allah kar ka mikamu hannunsu su sake wulakantar da mu su halakamu"......ta idasa tana saukowa daga saman kujerar da ya mata nuni ta tsugunna tana bayaninta tana mai magiya ta fashe da kuka tana hade hannayenta duka biyu tana sake sada kanta
Kasancewar abaya ce da ya kawo mata cikin kayan da Mama ta siya ya saka dan kwalin kanta dan zamewa ya sauka a saman kafadarta
Abinda ya gani a gaban goshinta ya saka shi lumshe idannuwansa hadi da amabatan sunnayen Allah a cen kasan zuciyarsa
Gaba daya dukan wani tunaninsa ke son hadewa waje daya, harma da wani kokari da yake iya yi na rayuwa
A hankali yake kaucewa tunanin, da korar da tunanin da tunanin wannan ai wani kwatse ne irin na tunane tunane marar dadi, wannan ai wani magana ne marar anfani da daraja, shirme ne, ba gaskiya bane, sai dai a lokacin da ta mayar da mayafinta ta sake kallonsa muryarta a raunace ta ce" Yalabai dan Allah ka rufa mana asiri........"
Sai ya samu kansa da saurin mikewa tsaye yana sauke numfashi a jajere kafin ya iya controling din kansa ya dauki waya ya yi kira ya bada umarnin a yi kokari a saka masa marar lafiyan nan a cikin mota, sannan ya sake fuskantarta a nutse ya ce" Bismillah"
Wajen da ya nuna mata ta bi da kallo, kafin ta sake kureshi da kallo
Shi dai a jikinsa shiga ce yau ta sasaukan yadi ruwan madara, sai dai rigar ce ya saka hadi da wandon gine dogo har kasa mai ruwan baki
Hannunsa daure da wata agogon ba ta jiya ba, sannan fuskarsa a gyare take hakama shigarsa shiga ce mai tsafta da class duda ba wandon rigar ya saka ba
Takalmin kafarsa kafa bude ne yau, ba kafa ciki bane, sannan kanshin turaren da yake fitarwa abin har abin mamaki domin turarensa mai naci ne na kanshi, watau idan ya saka shi ko ya bar waje za'a san ya ziyarce wajen sanadiyar kanshinsa da yake bari
A hankali ta sauke wata ajiyar zuciyar tana kallonsa ta ce" Su suka aikoka ka sake maida mu? Ka ga sai da muka yi shekara shida a hannunsu bamu ga hasken rana ba, zafi ko sanyi haka zai zo ya riskemu ya barmu, tun bamu saba da abinci sau daya tak a wuni ba har muka saba muka koyi ragewa mu ci da dare, tun ina kukan halin da yake ciki har na saba na koyi rarashinsa, da ba dan yaron da ya fitar da mu ranar bikin sallah ba, da har yanzu muna cen boye, mayar da mu zaka yi cen su kashe mu? Idan mayar da mu zaka yi dan Allah kafin su kashe mu ka fada mana me mukai masu? Me yasa suke son gannin bayanmu? Me mijina ya masu ne? Meye dangantakarsa da masarautar garin *BIRNAWA?* ..............,"
Wannan karronma bata samu amsa kamar yadda ta yi tunanin zata iya samu
Saima sake kureta ya yi da Ido kamar kurma bayan ta san ba kurma bane
Hakan ya sa ta idasa salamawa cewar wanan rayuwa ta ukuba da suka yi za'a mayar da su, wace ta tabata a yanzu kam idan ta suka koma ba dai su kuma tsira da rayukansu ba
Baban tashin hankalinta tunanin y'ayanta da take kwana take tashi da shi a zuciyarta...............aman a haka tana ji tana gani ta bi bayan wannan katon sojan , domin a yadda ta kulla baba yake a wajen, idan me yace sun yi to fa sun yin ne, idan aka barsu kuma daga su sai shi ta tabata basu da ci a wasan domin dai a kashe zai iya kashe su a tare ya murje banza ba tare da wani ya sani bama, gwara su je, ta rungumi mijinta yadda Allah ya yi da su........
A lokacin da ya dauki tukin a hankali ta dora kanta a saman kirjin mijinta da ya rame ya kode ba komai sai kasusuwa ta fashe da kuka mai ratsa zuciya tana fadin" .............. *IBTISAM da NAHIDT* Allah ya sa kun yi hakuri da rashinmu kun ci gaba da rayuwa a cikin amincin Allah, Allah ya sa a duk inda kuke ci gaban rayuwa kuke fuskanta ba ci bayanta ba, Allah ya tsare mana ku, ya sa mu kuma bakin wahalarmu kennan......"
Idannuwansa ya sake lumshewa yana mai jin gaba daya harshensa ya masa nauyi da irin abinda ya ci karro da shi a yau
Tambayoyi ne fall a ransa, aman ko daya ya rasa samun damar furtawa
Ba wai tambayar su waye a yanzu a gabansa ba, din tunda ya ga abinda ke goshin Mahaifiyarta ya ringa tantama da idasa dora zarginsa a bisa mizani, har ya ga haza ya kuma ji abinda ya kawar da zarginsa , a yanzu abinda ya fi tsaye masa shine masarautar garin da ya baro mai sunna BIRNAWA wanene azalumin fa suka takawa ya kasa hakura ya hukunta su da hukunci mai tsanani haka?, Sai kuma bawan Allahn nan da yake kallo da Abinda yake tare da shi, shi dai soja ne, wanda ya jima a gidan sojoji, ya kasance mutumen da ya san abubuwa da dama domin dole soja sai da tsari, wannan dalilin ya saka shi ya kure mutumen har ya gane me ke dawainiya da shi.............................ya kuma fuskanci ita kantaa iyalin nasa bata san takamaimai laifin da suka aikata ba, aman idan har hakaa ne, zai so gashi ga mahalukin da ya aikata haka........ko ba komai ai cutarsu aka yi, bale da yar alaka ta dan takaitacen lokaci a tsakani.............................
________________________________
Gyara suka gani mai sunnan gyara , domin basu san cewa wannan waje nada bukatar gyara irin wannan ba sai a yau, kuma abin mamaki gyaran nan da akai masu su da kansu wabi iri suke jin kansu, duda gyaran ya bambanta kansa domin ita NAHIDHT gyara ne ta amsa na wace ta san d'a namiji, ita kuma Shuwwa ta amshi gyara ne irin na cikakiyar budurwa mai dauke da iskar duniya
A lokacin da suka gama daka kananfarin nan, sai mama taa juye tafasashen ruwan sasaken bauran nan ta zuba a Po din nan biyu sannan ta kawo Detol ta zuba marfinsa daidaya ta umarce su kan kowace ta shige bayin dake dakinta ta zauna a sama, kadancewar bayi biyu ne
Sun dauka abin mai sauki ne, harma sunna tunanin wai wannan ne gyaran? To menene anfanin hakan? Basu san cewa baban gyara ne mai zaman kansa ba sai da suka kai duwawunsu sukka ne agajin sunna iya tashi ne? A lokacin da zafin ke mintsininsu yana shigarsu ba ji ba ganni, sai dai abinda Mama ta ce cewar kar wace ta tashi su zauna ya ratsa su sosai, domin wannan din maganin zahi ne fa sanyin dake kama jikin mutun, du mutumen dake dauke da zahi to fa dai ya ji irin wannan, aman da zarar ka yi kwana uku kana yi safe da yama siracin nan na hawa yana ratsa jikinka, to fa Zaka jika sakayau ba wannan zafin ko kadan,
Kasnacewarsu masu dauke da zafin ya saka suka ji ciwon abin sosai a jikinsu, aman kuma sunna jurewa har suka ji nutsuwa na shigarsu
Bayan sun gama ta saka suka zubar suka darwaye tass ta saka Shuwwa barin nata a bayin ta kilace shi aman ita NAHIDt sai ta hada mata wannan hadin kamar haka *Tafasashen ruwan sasaken baure, dakakiken kananfari, cristaux de menth* a cikin ruwan dan madaidaici sannan ta sakata komawa ta hau ta ce da ita komai zafi kar ta ji ta tashi har sai ruwan ya silace