← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 138

Sashe 91

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bayane tsoron masu harin rayuwarsa ke sake bayana daga bakin ranar da suka yarda cewar ya fa san da zamansu, uwa uba hakan ya hadasa rashin yarda mai tsanani a tsakaninsu da makusantansu da suka san da shirinsu a kansa, wannan dalili ya sa da zarar an san ya shigo cikin gidan kowa yake kama kansa, tamkar kowa ne ke labewa, uwa uba matarsa da kanta ta tatara yanata yanata ta bar gidan da kafafuwanta, wadda sai da ta jima gidan yayar mahaifinta kusan kwana biyu sannan iyayenta suka san abinda ake ciki harma suka nemi da sannin dalili? A nan ne Chief of army ya mike da kansa ya same su ya kuma yi masu bayanin da ya girgiza tunaninsu, sunne iyaye na farko da ya rabu da yarsu harma suka san dalilin rabuwar
Tabas sun yi takaici da mamaki n yarinyar da suka haifa suka ba tarbiya, ta kuma fara fuskantar izni a wajensu domin su suka haifeta , ko me ta aikata dole sunne dolenta, Allahma ya sa alkalamin KADARArTA bai karasa goga nata bakin penti ba, da ta kashe mutun kamar wannan da ina zasu shiga suma da suke iyayenta a kasar nan bale ita? A haka dinma sun godewa Allah, adu'arsu bata fadi kasa ba, jarabawarta ta zo da sauki, Allah ya bata wani mijin malamuncinta.........

A bangaren Mama da y'ayanta zama suke yi na zumunci, zama na sannin ciwon dan uwa, zama na kula da rayuwar dan uwa
A kwana takwas din nan da suka shige bayan kwonciya asibitin iyayensu likita ya nemi da su rage zaman asibitin, danma sunne sun kasance a tare da wanda ya isa a wajen, ama duda ya haka ya nuna masu su bashi dama ya yi aikinsa yadda ya dace, wannan dalilin ya saka Oga kwata kwatan ya dauki decision din bama zasu kuma zuwa kai tsayen nan ba su yi ta zama kamar ba gobe, ya yanke hukuncin gabanan tafiya ta kwana bibiyu ce sannan idan an yita za'a shiga ne a ga jikinsu a koma gida

Sosai hakan bai masu dadi ba, harma sun nuna da bukatuwar a dawo da iyayen nasu a kusa da su mana? Sai dai shirun da ya bi a kan maganarsu ya fahimtar da su cewar bai wani yarda ba, a dole suka kama kansu suka yi biyaya wa maganar

Mama, tunda abin nan ya faru bata kuma daga waya ta yi kiran Useina ba, domin ko a da itace ke kiranta, idan ka ga Useina ta yi kiranta to fa zata kawo mata korafin cewa MUHAY baya zuwa ya gaisheta, baya kiranta ne da sauransu, wani sa'in har sai ta yi dan murmushi a ranta tana ayana ko me yasa ita nata y'ayan itama basa zumunci da ita?, Sai dai ta kore tunanin ta fatatakeshi kan zumuncinsa da mamansa, ashe abin mai boyayan al'amari ne, to fa daga yanzun sai ta ajiye kiran nata ta kuma zuba mata ido har zuwa lokacin da zata waiwayeta da wata maganar , a nan zata bata amsa daidai da maganar da ta zo da ita ta hanyar fara kawo gyara a cikin lamuranta

Ta wajen Shuwwa kuwa ba wai shafawa rayuwarsa lafiya ta yi ba kamar yadda yake so, watau rayuwa irin ta kamar wace ba komai tsakaninsun nan?, Aa aa, gaba daya dukan wani abunda zai saka ya daga ido ya kalleta ko me yake idan dai yana kusa shi take yi, wani sa'in da gangan zata zauna da irin zama na daf da din nan wanda zai saka ya dan dago ya daina dukan abinda yake yi ya bi cinyoyinta da kallo da zaman da ta masa na matsewar waje, sai ya dan matsa kadan dan ya dan sama space a tsakaninsu, sai dai ba zai hanna idan ta yi niya tsaf ta dora hannunta a saman cinyarsa ta yi masa hirar da harga Allah shi bata wani dame shi ba ko kadan, sai dai ya kalleta har ta gama ta dan yi dariya tana mai saka yatsotsinta biyu a bakinta da babar da manuniyar ta dan gwala bakin tana masa alamun irin ya yi dariya mana? Shi kuma sai dai ya bi hannun nata da kallo ya kwabe fuska irin abun bai masa ba din nan sannan ya raka hannun nata da kallo irin kazamar nan, ita kuma ta tabe baki itama ta ci gaba da harkokinta da Su mama dake yi tamkar basu gane me aka yi ba

Dinkunnansu kuwa an kawo, abin ba'a cewa komai, dinkunna sun dinku iya dinkuwa sun yi kyau sosai, sannan gyara babu ranar da ba'a yi, Mama gyaran yi take na su duka ba na iya Shuwwa din kadai ba, gyaran kuma harda fatarsu, domin farin fatarsu ba shi ya hanna mama sake daukan mataki a kan fatar ba, fatar kanta sai ta sake yin luwaiwai ga kanshi mai daraja da suke bazawa ba lokaci

Nahidht kam tana cike da jin haushin irin yadda du hudubar da take yiwa Shuwwa a daki sai ta wani watsar, gani take yi har yanzu shuwwa bata da niyar zama da mutumen nan, sam gani take yi Shuwwa din bata gane cewar aurenta fa da wannan mutun sai dai hakuri, aure ne ya riga ya dauru, aman kuma ba komai ta mata uzuri

Kwana biyu tsakani da kansa ya yi tafiya kan zai yi kwana uku sannan ya dawo, domin zai je ya daidaita harkar aikinsa na cem ne
ya fada cewar kar su je ko'ina ciki koda asibiti ne har sai ya dawo daga tafiyarsa

Kwana ukun tsakani ne da kansa ya yi kiran mahaifiyarsa yake fada mata cewar yanzu suka gama waya da chief of army, likita ne yake fada masa cewar yau kwana biyu kennan da ya daina masu anfani da maganin dogon barcin da yake yi masu, domin su dukansu cikin ikon Allah jikinsu ya yi yadda yake so, balema namijin a yanzu baya kubtayar nan, sai dai shirunsa ya fi maganarsa yawa, domin a jiya matar yasa ce ta bukaci a bata abin aski da kanta ta bashi madubi ya rike ta yi masa askin da ya bamu mamaki, domin kamar wata mai aski haka askin ya yi kyau du ta kwashe duguzar nan

Aman baya cewa ummm, bale umum, ko rubutun da na fitar a frij na yau ya bashi ya amsa ya sha da kansa sannan ya shige bayi ya sake yin wanka , wai mutumen ba dai ba tsafta da ibada, ya nuna cewar sunna iya tafia gida domin Matar na ta tambayar ina y'ayanta ne? Ko mafarkinsu ne ta yi? Aman wani irin mafarki ne haka ? Ita sai tace sojan da ya dauketa wajen yarenta ya kaita, shin ina sojan yake da suaransu dai, to shine nake cewa Aba a bude gida guda a saka masu kula da su a kaisu kafin na dawo na ga idan na samu zama da mutumen ni ko zai bani amsoshin tambayoyin da ake masa baya cewa komai?......"

Ya fan sasauta dan maida numfashi, Mama ta ce" Ina jinka"

Muhay ya ci gaba da fadin" Shine Aba ya ce bai yarda da a kaisu wani wajen ba, wai idan mai binsu na tare da su fa? Komai na iya faruwa ciki harda siyan masu kula da su din, a nan gida akoy waje wadatace da zasu iya zama har komai ya daidaita .....to Mama da ni......."

"Kai me MUHAY?" Mama ta fada itama a sanyaye💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 5️⃣3️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A hankali ya ce" Dama bana so Hakan ya hadasa wata fitina ne a gidan duba da na kawo Yarinyar nan da yayarta, sannan na karro iyayensu kar............"

Mama ta dan yi tsai ta ce" Kar a ga ka kawo mutane ka zuba?"

MUHAY ya dan gyada kansa hadi da fitar da fan sautin dake nuni eh yake nufi

Mama ta yi dan murmushi ta ce" Wani ya taba nuna maka wani abin ne Son?"

Dan tsai ya sake yi yana sauraronta, gaba daya yanzun Mama bata hawa kan fada a kan abinda ya shafe shi, sai dai ta saurara sannan ta bi abin a laluma, Hakan ya sa shima a yanzun yake doguwar magana kamar sunna a gabanta idan har zai yi mata magana ko wata iri ce

Mama ta yi dan murmushi ta ce"To ai sai dai ka yi hakuri, domin ka ganmu nan mun gama kimtsa bangaren da Abanku ya ce a gyara harma ga matarka cen tana saka ruraran wuta, kai din sai yaushe zamu ganka a gari ne?"

A hankali ya ce" Wani case ne na tarrar a nan sun, sun shiga kotuma, jibi ake yin zaman karshe, matsalar wani mai kudi ne ke son juya abin , in sha Allah da an gama zan dawo Mamah"
Chapter 91 · 0% Book details