← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 138

Sashe 30

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina hannunta ta janye tana karra kallon NAHIDT da gaba daya duniyar take neman yi mata zafi da mugun tsoro da fargabar kar a kuma fasa auren kanwarta
Daidai Fauziya ta fito da Shuwwar tana rike da hannunta ita kuma tana sanye da doguwar farar riga mai laushi sai hijab dinta fari dogo sosai har kasa wanda ta sha wankan ruwan turare da na wuta ya kasance shigowarsu ya sake harmutse kanshin falon sai dadadan kanshinta ya sake dauke dakin gaba daya , a lokacin ne kuma matar ta sake zuba mata ido itama tana kallonta

Kanta ne ta ji ya fara juyawa, harma ta fara tunanin ko ta haukace ne da yan matan nan biyu daya ke kama da yar uwarsu da ta bace masu bat, dayar kuma, wannan din kuma bata yi maki kama da hoton sarkin garin nan marigayi ba? Har farin fatarta? Hoton dake kafe a falon Aba wanda bayan ya rasu aka dora kanninsa da suke uba guda domin d'ansa na cikinsa an wayi gari ba shi ba labarinsa? Hajia duba ki gani ko dai yau na tashi a haukace ne? Ko kuma gajiya ra saka nake hade haden nan?

Hajiyar ta juya wajen da NAHIDT ta ja su Fauziya jikinta na rawa tana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une kin ga Shuwwa abinda na so na fahimtar da ku cewar anya zuwan nan namu nan alkhairi ne kuwa zai tabata, kin ga matar cen ta malan ce take son kwatanta kamar zaman kanmu muke yi kin ga matar cen da suka kawo kayan ta kafemu da ido har ana son zaunar da ita ta ki zama mun shiga uku"

Hankalin Shuwwar ne ya yi kololuwar tashi ta juya zata kalli matar daidai matar ta fice da mugun sauri, hakan ya sa ta dora hannayenta bibiyu a saman kanta tana fadin" Idan aka fasa auren nan shikenan, shikenan aunty , idan aka fasa walahi ina iya rasa raina, wayo Allahna na tafi wajen Aban na fada masa ya rufa min asiri ya daura kin ina son Hamza, walahi ina sonsa idan ba'a aura min Hamza ba ina iya mutuwa"

Da mugun sauri ta juya itama har bata gannin gabanta hakan ya sa suka mara mata baya sunna son tsayar da ita aman ta kasa sauraronsu ta nufi falon da ta san a cen Aban yake

Tunda matar nan ta shigo kanta je kasa jikinta na dab rawa ta sake maimaitawaa yayansu wanda yake shine baba a dakinsu gaba daya ta ce" Allah ya karra maka lafia walahi, walahi kamanin sun bace, yarinyar tamkar an zaga karra da *TINANA* , sai dai kuma kamanin yar uwar tata ne suka sakani a rudu, me hadin kamanin marigayi sarkin garin nan da nata? Har farin bayan kar duniya mun san d'a daya ya malaka har ya koma ga ubangijinsa, yarinyarma ta yi kankanta ace y'arsa ce gaskiya idan aka auna mutuwarsa da yanzu"

A guje ta sake warce hannunta ta fado dakin tana neman fuskan Abanta dake zaune shika hankalinsa a tashen yana son jin karshen maganar nan
Da sauri ta idasa gabansa ta duka tana hade hannayenta ta fashe da wani kukan da ya saka kowa juyowa kallonsu ciki harda CHIEF of Army da iyayen Hamza , daidai NAHIDT ta karaso ita dinma tana kukan ta tsuguna a gabansa itama ta hade hannayen nata hakama Fauziya ta shigo itama nata hankalin a tashe

A gigice take son yin magana aman ta kasa hakan ya sa Nahidht farin" Sun ce sun fasa auren su dinma ko MUHAMAD ? zasu daina aurenta ne ko? Shikenan haka zamu kare rayuwarmu dan bamu da iyaye?, Menene laifinmu?, Dan Allah ku rufa mana asiri kar a fasa domin ko ni idan aka fasa auren nan da Hamza na shiga uku, dan Allah ku dubi maraicinmu ku bari a yi aurennan, idan har dan maganar amaryar malan ce kar ku dora hakan a kan Shushu, mu mune bama jin magana aman shushu babu abinda ta sani , burinta ta yi aure, burinta ta je ta bautawa aure, burinta ta samu kanta a dakin mijinta, ku yi hakuri a yau a daura auren nan, ko a nan ne a daura kawai ba sai sauran sun zo ba....." Ta idasa da fashewa da kuka daidai Aban Hamza ta mike yana karra kallonsu muryarsa har rawa take wajen furta" *TINANA?*"

DIF Nahidht ta yi da ihun kukanta jin an ambaci sunnan mahaifiyarta wada ba zataa taba manta wani lokaci ta taba gannin takardar mahaifiyarsu da sunnanta na usil banda Buzuwa da ake kiranta da shi

A rikice ta juyo tana kallonsa, shima kuma ita din yake kallo hannunsa still na rawa ya sake fadin" *TINANA?*"

Zabura ta yi ta........

*GARABASA GARABASA, DUKAN WADDA TA BIYA KUDIN ALKALAMIN KADARRATA ZATA SAMU GARABASAR WATA KOKOWAR KYAUTA IN SHA ALLAH, WANNAN GARABASA CE🥰*

Domin samun ci gabansa in sha Allah ki garzayo ki biya kudinki yar uwa, a kan farashi mai sauki ..........domin a gaba ne zamu gane kaifi irin na ALKALAMIN KADARAR bayin Allahn nan
Me yake shirin faruwa da su
Ina zasu dosa?
Yaya maganar gagarumin daurin auren nan da ake shirin daurawa?

Su SHUWWAR da NAHIDHT su wanene su?

Me dangin Hamza suke nufi da maganar ambaton Nahidt da sunnan yar uwarsu?

Meye gaskiyar maganar kamanin SHUWWAR?

Dukan wannan zai zo a bayane a tsare ta yadda mai karatu zai karanta cikin shauki in sha Allah

Daga alkalamin SAJIDA😍🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

+22793811618💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣6️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Zabura ta yi ta mike daga tsugunen da take a gaban Malan har sai da daurin dake saman kanta na dan kwalinta ya fadi kasa warwas tana kallon Aba
Muryarta ce ita dinma ta dauki rawa rawa ta ce" Ba, Ba , mamanmu ce *TINANA*"

A bayane Aban ya karaso da sauri yana rike hannunta yana fadin" Hasbunnalahu wani'imal wakim, mamanku? Ke da wa? Inna take? Inna TINANA take Hawau itace, kin ga itace wannan din jinninmu ce, yarinya ina TINANA? Ke din ke da waye kika ce mamanku ce TINANA?"
Sai kuma ya yi shiru da gagawa ya juya wajen baban Hamza da suma gaba daya hankalinsu ke kan su SHUWWAR din balema Chief of army da yake kallon yarinyar da tausaya

Yana zuwa ya ce" Elhaj, ka ga wannan ai jinnin Hamza ce, yar mamansa ce, ko ba haka kike nufi bane yarinya? Dan Allah ki fahimtar da mu kamanin nan naki da kanwarmu"

Gannin du a rikice suke ya saka Ganaral fadin" Bismillah, Elhaj ka zauna ka ga yarinyar du ta rikice kana gannin kanwarta itama du ta shiga a halin rudu, ku zauna mu yi magana a tsanake dan Allah".......daidai nan kira ya shigo a wayar Ganaral hakan ya saka shi dagawa yana mai amsawa

A nutse ya furta" Masha Allah, ka sa abokinka ya kula da baki ka shigo a nuna maka falon da Malan ya sauki baki muna ciki, ai da dan saura lokacin daurin auren bai cika ba, ba za'a tsayar da mutane ba, ka shigo "

Daga haka ya katse yana fuskantar mutanen dakin shima ya kasa yin magana

Malan da Shuwwar ta yi karkadab da hannunsa ne ya samu a hankali ya janye yana sauke ajiyar zuciya a nutse ya furta" alhmdulilah, in sha Allah dukan abinda Allah ya yi a yau alkhairi ne, domin zabinsa muka nema, shi muka fadawa, koda na tsayin sati takwas ne kadai muka dauka muna fada masa zamu iya cewa Alhamdulilah sannan mu yi hasashen cewar ya ji mu ya kuma amsa rokonmu, NAHIDHT da SHUWWAR, shin zaku iya saka nutsuwa a firgicin dake tare da ku ku bamu labarin abinda ya faru da iyayenku har kuka samu kanku a kasar nan?"
Chapter 30 · 0% Book details