← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 138

Sashe 73

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tausashe da rikaken yaren buzancinta ta ce" *"Elishe jehadine itamatak, yara atunaso agrawadah, tunane tuta wulih*"............. Da sauri ta dafe gaban goshinta ta kuma dauko harshen larabci dan ta tabata ba gane yarenta zai yi ba, yanzunma a kidime ta ce" Subahannalah , *Innahu zauji, sa ya mutu hunaka, alaina an nazhab, laqag intiqalal yaum*"

Sai kuma ta yi kwalkwal da idannuwanta tana sake rike damatsunnan hannayensa domin ya dafata ne yana kallonta a wani rikicen wannan karron da yaren turancinta gangariya ta ce" *My husband, he is dying,he said we have to go,His condition is critical* "

Sai kuma t samu kanta da yin shiru na dan lokaci tana kallonsa, kamar kurma, ta rasa gane yana gane yarenta ko baya ganewa? Wani yare ne shi? Me yake ji? Kwata kwata ta manta da yana mata maganar zai kaita asibiti, kai tama manta da wani yare ne ya yi mata magana, yanzun ta dauki yaren karshe da fatan Allah ubangiji ya cidata ya ganeta a raunane ta ce " *Mijina ne, gayacen zai mutu, wai sai mun tafi, yau abin ya tashi sosai*"
Ta cika shi ta hade hannayenta ta ce" Ka barni na koma gare shi, ta yiwu idan na bashi maganin ya koma barcin"

Sakinta ya yi yana kallonta a lokacin da ta sake rage tsayinta sosai tana dafe gwuiwarta ta kwashe sauran magungunnan nan ta maida cikin robar irin ta almajiran nan ta sake juyawa ta komaa wajen da ta nunaa masa tana dingisawa haka kuma jinnin na diga a kafarta domin ta bugu sosai, aman abin mamaki ba buguwarta ce a gabanta ba, hasalima fama take ta karasa wajen da tai masa nuni

A hankali ya ringa juyawa yana karewa wajen kallo kafin ua sauke ajiyar zuciya ya nufi wajen da ta bi aa hankali

Sai da ya shige wajen sosai sannan ya saka hannunsa ta bayansa ya ciro bindigarsa a hankali yana sake kusanta kansa da wajen yana hankalce da yannayin wajen
Shi kam bai ga komai na suspect ba, hasalima wajen shirunsu ya yi yawa sosai

Sai da ya karaso ya dan saurara kunnansa ya dan hada kunnen nasa da jikin zanar yana sauraro

"Ki kunceni babu inda zan je , ki kunceni mu gudu kin ji, ki kunceni bakya jin zafin da nake ji ko? Zafi nake ji a jikina kamar zan mutu, gaba daya duniyar nan garin mai zafi ce, so nake na ji na tashi sama na gudu, mu tafi so nake na tafi"........... Muryar wani namiji ke fada a rikice kamarma kokowa suke yi da matar

A hankali ya samu ya dan daga rufar buhun da aka yi a kan kofar, hakan yaa tsorata su gabaa dayansu, saima ya kasance namijin ya fi macen tsorata domin gaba daya ya nemi cumuimuyeta a cikin abin rufar da take lulubi da shi

Jikinta na rawa itama cike da tsoron kar dai asirinsu ne ya tonu haka take kallon MUhay

Shima dan bukar tasu yake bi da kallo, wace da gani baa sai an fada ba wanda ya yi bukar nan ko macen ce ko kuma wani ne da bai iya ba domin abin a jirkice yake gaba dayansa
Irin robar da ta zo da su ne biyu ajiye kowace ba komai a ciki, haka kuma a dakin ba komai daa zai nuna maka sunna dan samun na ci a bakansu ko yayane

Ba abin sallah, kai datin dake tare da su din nan anya ruwan alwallah na hawa jikinsu kuwa?

Sake maida kallonsa ya yi jikinsu yana mai tabatarwa kansa cewa hali ne na rayuwa ya mayar da su haka, dan haka sai ya samu Kansa da fitowa ya tsaya yana sake kallon Wajen ya dora numbobin ambulance tasu ta sojoji ya danna kira

Magana ya yi a takaice daa kwatancen hanyar ya fada cewar zasu ga motar dake dauke da number CHIEF OF ARMY a wajen sai su masa magana

Dan zagaya wajen ya ringa yi yana hankalce da matar nan ta leko da sauri kuma ta yi wuf ta koma dukan alamu na tsoro na tatare da ita, haka kuma muryar mijinta duda a shake take kuma a kasa take sosai aman ta karra amo yana ta ihun dake nuni a tsorace yake shima, hakan ya saka MUHAY a matsanancin mamakin abinda ya tsorata su dan sun ga mutun ya rabe su haka

Motor ta karaso tana jiniya irin na ambulance 🚑, da gagawa suka fito , likitoci ne uku sai soja biyu, a cikin likitocin kuma harda mace daya wace ta hau yau itama sojan ce

Sai da ya yi dan tsam kadan kafin ya juya wajen da dakin yake
Ky din motar da ya fito da ita ya mikawa daya daga cikinsu ya masa umarnin ya bisu da motar , sannan ya saka suka fitar da gadon tura marar lafia suka nufi dakin, kowane cikinsu na mamakin waye ba lafiya a nan?? Me ya kawo Lieutenant Ganaral nan?

Bai tsaya wata wata ba ya yi salama kasa kasa ya shige
Yanzunma a cure suke waje daya sun yi tsuru tsuru
Hakan ya saka shi bada damar a dauke mijin nata da ita din kanta a shiga motar da su
Zo ka ga dambatuwa, domin yaki ta shiga yi ba ji ba gani tana sambatun kalaman da basu gane makamarsu ba, fada take yi ba ji ba gani tana doke doke ido rufe kan ba zasu tafi da su ba
Hane hakan da suka yi sai suka fi bada hankali kan mijin suka gigibe shi suka dora saman gadon nan
Kwarai sun yi tunanin samun zaurin fitsari a jikinsa, sai dai du uban datin nan na jikinsa karnin dauda ne kawai ke tashi a jikinsa irin mai saka juwar nan, haka itama matar
Sunna fara tura gadonsa a hankali ta ringa binsu dan kanta tana kallon yadda aka daure shi a jikin gadon watau hannayensa da kafafuwansa fan kar ya fado ya raunata kansa ko ya yi ta doke doken da zai raunata kansa
Tsananin tashin hankali ya saka ta fara gannin dishi dishi
Tsoronta Allah tsoronta kar tafiyar da suka jaba kafin su yi nesa da garin ne ta tashi a banza yau tsal aka gano inda suke, tausayin mijinta da halin da yake ciki ya fi karfin tunaninta
A hankali take jan numfashi tana sake bin motar har suka kusa karasawa sai kuma luuuuu ta tafi da niyar jirtuwa a kasa sakamakon sumewar da ta yi
Dama a daf da ita yake, tunda aka fito da mijin yakr hankalce da yada take layi, ga kuma kafa tana ja da kyar, kasantuwarsa tsoron ma'aikaci da ya jima yana damawa da mutane kala daban daban ya saka shi gane cewa abinda ya koro kura daga raminta ba karamin balaki bane, hakan ya sa yake ji a ransa ya zama wajibi ya mika su asibiti sannan ya san su waye su, ba kyankyamin datin jikinta da warin da take yi ya talabe faduwarta kasa ta fada a jikinsa ya cicibeta yana hanna likitar da ta zo dan amsarta, amsarta ya kaita cikin Ambulance din suka saka gadon nasa sannan suka rufe direban ya ja motar su kuma suka shiga kokarin fara fahimtar damuwar mutanen harma suka farfado da ita tun kafin su karasa

Sunna karasawa suka shige da su ciki
Da gagawa likitoci suka shiga basu dukkan kulawar da ta dace da su, da gwaje gwaje kala daban daban ciki harda na su HIV, domin yannayinsu ya kwantsame da yawa abin sai hamdallah ga rama ga ramewar fata ga rashin kyan kama

Barci suka saka su mai nauyi kafin wasu likitocin su shiga kokarin tsaftace masu jikinsu inda suka raba maza na yi masa, mata na yi mata ka'in da na'in, aiki na zuciya daya domin mai gidan ya kawo su babu wanda zai yi wasa da aikinsa ya kwana ciki

Dukan bayanan da likitar tai masa yake karra taunawa a zuciyarsa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya amsata da yi mata godiya sosai , wanda hakan ya bata mamaki ainun duda ta san dama idan ka yi magana da shi na kurewar waje zaka fahimci mutun ne mai furuci a tausashe , aiki a nutse, sannan dan ya fika ba yana nufin shi ya haliceka ba, yana mu'amalantarka da darajaka, ko kiranka zai yi baya yi maka kiran wulakanki, ya sha bamban da wasunsu sosai, yana anfani da sanninsa na adinin musulunci hakan ya sa da zai tafi kasar nan har na tsayin shekara biyar suka taru suka nuna basa so, sai dai an fi karfinsu ne an nuna masu aiki ne , gaba daya kasa yake yiwa ba gari daya tak ba, a kan dole suka yi masa fatan alkhairi, rakiya kuwa da zai daga har sai da aka hanna wasu shiga wajen jirgin kamar ba za yana zuwa week-end yana komawa ba

Ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya nufi office din da yake malakinsa a baban gifan sojojin
Sai da ya zauna ya dauki wayarsa yana dan jujuyawa da tunanin wanda zai saka aikin nan?
A nutse ya yi kiran number mahaifiyarsa, a lokacin kuma sunna cikin makeken shagon takalma tana kwasa tamkar zata bude dan shagon stillllllll, ta amsa

Dan hayaniyar ya saka shi tambayar ko ana ina haka?
Murmushi ta yi ta ce" Gamu a babar kasuwa lefe muke hadawa"

Dan jim ya yi jin wai lefe suke hadawa yana tunanin kar dai wani auren zasu sake yi masa ?, A hankali ya ce" Wani zai yi aure ne?"

Kai ta girgiza ta ce" Matarka nake hadawa mana, ai ba'ai mata lefe ba, kuma baka yiwa dayar matarka kayan fadar kishiya ba, kai anya kudin asusun nan nawa zai isa kuwa? Ka dan kara turo wani abin ta ciki dan Albarka ka san siyayar mata akoy yawa inaga yau kadai ba zata ishemu ba"
Chapter 73 · 0% Book details