← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 138

Sashe 97

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa kasa ta yi maganar sosai, hakan ya sa Fauzy din dungure kanta itama kasa sosai ta ce" Ni zan baki mamaki ko matar malan, kin ga Nahidt wai? Sai da ta duka har kasa ta gaishe da Malan, gaskiya ta ji tsoron Allah kar ta haukata bawan Allah"

Dariya ta kubuce mata a fili da sukai ido hudu da NAHIDT din ta balla mata harara

Gaishe da jama'ar dakin ta yi a jumulce tana dan bin kowa da kallo har ta kai idannuwanta saman fuskar yayansu dake murmushin ganninta shima

Wajensa ta karasa har kamar zata zauna daf da shi sosai ta miko masa hannu tana fadin" Me yake damun yayanah ne?"

Murmushi ya saki wannan karronma mai fadi ya saka hannunsa cikin nata a sanyaye ya ce" Ba komai autanah....."

Itama yar dariya ta saki ta nemi zama gaba dayanta , sai dai bata kai da zaman ba muryar Maman Muhay ta katseta ta hanyar fadin" IBTISAM zo dauki jus din mijinki ajiyr masa kafin ya tashi, ga abincinku cen ki bari idan zaki je ki je masa da shi"

Daga shi har ita din maman suka kalla kafin ta juyo a hankali wajen da tunda ta shigo ya fi wartarta, watau wajen da idannuwanta suka yi ta daukanta sunna kaita aman tana kin kallo ta dora dubanta a kai

A hankali ta sauke ajiyar zuciya sakamakon kallonsa da ta yi tun daga kasa har sama
Zata iya cewa bata taba ganninsa da manyan kaya haka ba ko a ranar da aka daura masu aure
Ba wai manya gari da yar ciki bane ya saka , no, dinki ne dai na shada akai masa mai zubi mai kyau, gashi shadar ruwan madara ce kal kal, hakan ya sa kayan suka amshe shi sosai suka kuma fitar masa da annurin fuskarsa da jikinsa baki daya

A hankali ta cire idannuwanta sannan ta dan janye hannunta daga cikin na yayanta ta nufi wajen abinda aka ce ta dauka ta kai masan

Daga wajen da Maman take ya dauke idannuwansa a hankali ya dora saman kanta a lokacin da ta dauko mg na kwalba ta nufo shi da shi
Idannuwansa ya cire a hankali a cikin nata sakamakon tsayawar da ta yi dan ta ga ya saka idannuwansa cikin nata ya dora saman hannunta sannan ya yi kasa da kallonsa saman kafarta mai sanye cikin safa fara kal

Sai da ta karaso ta ajiye ta kuma kallon fuskarsa, wannan karronma ido hudun suka yi ya sake daukewa da dan sauri ya maida gefen da Malan ke fadin ya dace su je masalaci lokaci ya gabato

Ajiyar Zuciya ya sauke ya rakata da ido har ta karasa kusa da yayarta da Fauzy da suka kile suke magana kasa kasa sai dai ka ga sun tuntsire da dariya ya dan karra kallonta na yan sekwani kafin ya mike yana sauke dubansa kan Mamansa

Dan tsai ya yi dan gannin Maman na kallonsa, sai kuma ya gimshe fuskar ya yi gaba yana fadin" Allah ya bamu alkhairi"

Mama ta dan daga murya ta ce" To ka kaisu masaukinsu cen bangaren bakin abanku fa an gyara"

Dan turus ya yi ya sake kallonta, domin shi ai ya zata a bangarensa zasu sauka, sai kuma ya amsata ya fice yana dan kalle kallen gidan da wani tunani daban na shigar yarinyar nan da tunanin bata saka hijab ba ta ratso kartin naj, uwa uba ta gaishe da kowa banda shi a falon cen ko?

Ba su su dawo ba sai da karfe goma ta bada baya, domin dogon zama ne suka yi sakaninsu , zaman da aka yanke daurin auren NAHIDT da Malan, wanda ya nuna bukatar hakan da kansa, Mahaifinta kuwa ya nuna ya ba Dad wuka da nama, Dad ya nemi shawarar MUHAY shi kuma ya ce ya bashi, daga nan ne kowa ya nufi wajen da aka bashi masauki suka je dan hutawa

Tunda ya shigo ya ga kayan abincin da aka jera masa da irin gyaran da bangaren nasa ya dauka ya cika da mamaki sosai

Da sauri ya nufi dakinsa na barci har kamar zai ci tuntube ya shiga kunna computersa da kayan da ya boye na bincikensa
Yana ganninsu sai da ya sauke wata wawuyar ajiyar zuciya sannan ya sake rufe wajen da kyau ya dan sake bin shinfidar gadonsa da kallo hakama yannayin dakin barcin nasa

Iska ya dan furzar da tunanin ko Mama ce ta yi aikin nan da kanta ne?, Dan haka sai ya tube ya shige bayi ya yarda karamin wandon nasa nan saman gado

Wanka ya yi sosai ya dauro alwallah ya fito yana shafa mararsa hadi da nufar wajen da maganinsa yake ya bude jakarsa ya ciro kwaya biyu

Da tawul din nan a daure a tsatsonsa ya fito falo dan zuwa ya hadiyi maganin nan ko mararsa dake ta dauran niyar kulewa ta warware abinta, sai dai abinda ya gani ne ya saka shi ja da mugun sauri yana kallonta, domin ta shigo kennan ne falon itama ta juya tana leke dan ta ga sun tafiyarsu ne? Ko ta iya fita ta yi tafiyarta

A hankali ta juyo jin kamar an fito ta sauke Idannuwanta a saman kansa

Ido ta kwalalo da dan karfi ta ce" A'UZUBILAHI Mina SHAIDANNIN RAJIM !"

Da mamaki yake kallonta kafin a kule ya ce" Ke ce shedaniyar ai ba ni ba , Meye kuma?"

Idannuwanta dake rufe ruf ta dan bude , sai kuma ta mayar da karfi ta sake rufe su , jikinta na dan rawa kadan ta ce" Meye me?, Wai ina rigarka ne zaka fito tsirara dan girman Allah ?"

Ido ya kwalalo da mahaukacin mamaki ya sake bin kansa da kallo, da yar dabara ya saka hannunsa ya gyara tawul din da kyau sannan ya saka abinda ya fara kumbura a matse matsin kafarsa ya dan matse kadan ta yadda ba zai ji ciwo ba yana kallonta ya ce" Ke me kika zo yi dakina?"

Kadan ta dan bude idannuwanta tana kallonsa kadan ta maida ta rufe ta girgiza kanta tana fadin" Cewa suka yi wai na zo nan a nan zan kwana, inaga ko na tare a nan dinma suke nufi? Wai dan Allah yalabai baka jin kunya jiki a waje kana tsaye gaban yar cikinka?".............

😳😳😳😳 Wollah ba luwana😳😳😳😳😳💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 5️⃣7️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Wani mamakin ne ya kusan kume shi, har ya bude bakinsa ya kankance idannuwansa zai biyata su raba hali , sai kawai ya juya yana damke da tawul dinsa ya yi cikin dakinsa

Direct wajen kayansa ya nufa ya bude ya ciro yana waigawa kar aje ta shigo ta same shi a asalin zigidir din, domin idan da ta rufe ido yanzun bai san wani kalar tashen haukan zata nuna ba!

Dan tsaki ya ja yana jan wandon ya saka , ya saka rigar da ya janyo du yana dan dagawa yana leken kofar da ya rufe, aman ya gama sani ne yar nan bata cikin tsarin masu hankali, tana iya shigowa nan din dan wata fitinar da bai san farkonta ba bale karshenta

Neme nemen maganinsa ya shiha yi domin ya wurgar da shi wani wajen
Da kyar ya same shi saman tawul din da ya cire ya dauke shi ya fita dan cin abinci da kuma shan maganin yana tunanin yadda zai yi da Mama dake son karfi da yaji sai taa hadasa masa ciwon kai da yarinyar nan

Wani idon ya sake zuba mata gannin ta zuba soyayan dankalin turawa ta kuma dora soyayan namaan kaji a sama ta koma gefe guda ta yi zaman makaranta ta fara ci

Itama kallonsa ta yi sai ta yi dan murmushi tana fadin" gani na yi da kaza a kusa me ake da gurzajiyar kubewa? Aman Mama ta dage a yi ta yiwu ta birgeku, zo dai ka dandana ka ji ta yiwu ta birgeka , ni kam Alhmdulilah walahi ga nama bana son bak'ar miya!"

Cire kansa ya yi a kanta ya karasa da dan hanzari ya dauki kopin kwalbar nan dake ajiye ya aha magungunnansa biyu ya dago ya kora da ruwa gaba dayansu kafin ya sake saike idannuwansa a kan fuskarta da ta yiwa takwaf takwa takwaf kamar a bakinta ne ya zuba maganin ba a bakinsa ba

Wani takaicin ya sake shaka na rainin wayon yarinyar nan, da wani uban haushin ya nunita da yatsarsa yana fadin" Look!, Ki tashi ki bara min falo ni bana son saka ido, dan kin raina ni sai ki ringa shigar min waje kai tsaye, kuma kika shigo waje kika gaida kowa harda namijin da saura kiris a daura maki shi kika cafe ni ga dan iska ko kallo ban ishe ki ba ?"
Chapter 97 · 0% Book details