← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 117

Sashe 99

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta saki murmushi ganin yanda yake mata kallon rashin fahimta, bai san mai taji ya tsarga mata bane shiyasa.
"Ina Lafiya kawai nauyin kai nake ji, wataƙil don nayi barci mai tsayi" bata tsaya kuma ta ji daga bakin shi ba ta fara sauƙa daga gadon ta ɗaya bangaren tana faɗin "Zan fara wanke baki na" bata samu indoor slipper ɗinta ta wurin ba ma haka ta taka ƙasan babu takalmi har saida ta isa ƙofar bathroom ɗin ta saka na shiga ciki.

Itama har da wanka tayi ɗiyanin, ta fito lokacin da yake gunguro cart ɗin breakfast ɗin su da room service suka kawo.

"Zamu fara karyawa?" Ya tambaya idanun shi na sauƙa zuwa ƙafafuwanta ba tare da ya ankara ba, ta tabbatar kuma ta ga sanda ya haɗiye ƙishirwar shi, amma dake yunwa take ji a lokacin sai ta amsa mishi da "Toh"

A dining mai kujeru huɗu a zagaye da shi suka zauna, shi yayi serving ɗin su ta zauna da towel a ƙirji suna cin abinci shiru ya ratsa tsakanin su na wani lokaci kowa da abinda yake tunani a ran shi.

"How do you like my surprise" ya yanke shawarar katse shirun.

Tana shirin ta yi murmushin jin ya ƙare yayi magana sai jin hannun shi tayi a cinyarta ta ƙasan teburin. Numfashinta ta riƙe idan ba haka ba ƙwarewa zata yi kuma bata son ya janye.

Breathing technique da doctor Fahad ya koya mata ta fara practicing a hankali, bata bar shi ya lura ba dukda tana jin idanun shi a kanta amma sai tayi kaman hankalinta na ga abinda ta cika bakinta da shi ne take son haɗiyewa kafin ta amsa tambayar shi.

A hankali kuma taji ya fara yawo da hannun yana shafa cinyan a hankali da yanayin da yake ɗaga mata tsigar jiki.

Ta sha ruwa sosai tana mayar da numfashi kana ta daura murmushi a kan fuskar ta.
"I love it, in fact wannan abu ne da ban taɓa mafarkin shi ba. Ka faɗa min abinda zan yi maka domin kawai in gwada maka farin cikin da nake ciki. Turkey is my dream country!" tace ƙwalla na taruwa a idanunta don da gaske saida taga jirgin su ya daga a daren jiya ta tabbatar ba wasa Safina take mata ba.

Ya ajiye fork da knife ɗin shi ya riƙo hannunta dake dafe da nashi ya riƙe yana kai bakin shi ya sumbata. "Just ki samu lafiya, shikkenan kin biya ni"

Miƙewa tayi a hankali yana binta da ido har ta sama ma kanta wurin zama a cinyar shi sannan ta zaga da hannunta ta bayan wuyan shi tayi nasarar kwantar da kanta a ƙirjin shi.

"Whats wrong Reina?" Ya tambaya tana jin hannun shi a gadon bayanta.

Murmushi tayi jin yau ne karo na farko da ya kira sunan ta tun kafin auren su. Da siriryar murya tace "Nothing, kawai dai ina sonka ne yaya Yaseer, da dukkan zuciya ta, duk abinda nake da shi ko na mallaka naka ne, na baka kaina ko baka so, kuma zan bika duk daɗi duk rintsi, da akwai da babu duk zan yi maka biyayya ,da fatan wannan zai zama silar da zan wanke baƙin fentin da nayi ma kaina a cikin zuciyar ka..."

Saurin ɗago ta yayi sai ganin hawaye yayi sharr sharr a idanunta, cikin tashin hankali ya tallafi fuskar ta amma sai faman sheshsheƙa take yi. "Reina?..."

Ya miƙe da ita a jikin shi suka koma bakin gado sannan ya ajiye ta shima ya zauna. Shi da ya ɗauka idan suka zo murna har sai ta rasa inda zata saka kanta amma sai ya samu tukuicin kuka?.
"Umry kin san idan wani abu yana damun ki ni mai sauraren ki ne right? So ki min magana Please"

Ta buɗe idanunta a kan shi "ba gudu na kake yi ba?"

Dukda yana cikin damuwa da yanayinta amma sai ya samu kan shi da murmusawa domin tambayar tan bai kama hankalin shi ba. "Gudun ki kuma? Ni?"

Ta ɗaura da "tun bayan wannan daren ka canza, ko dan baka same ni yanda kake so bane? Saboda..." Maganar ta ya katse ba don ta gagara ƙarasa kalaminta ba sai don shi ya hanata ta hanyar da yake ganin yafi masa sauƙi. Bai kawo a kansa cewa irin waswasin da shaiɗan yake raya mata ba kenan.

A hankali jikinta ya fara sakewa, tana sassauta riƙon da tayi ma rigan jikin shi, har saida yaji kukan nata ya tsaya kafin ya ɗago yana kallon yanda take sauƙe numfashi idanunta a rufe, shima numfashin yake mayarwa a hankali ya shiga share mata hawayen da yabi fuskarta sannan ya fara magana.
"Da na san irin tunanin da zai shiga kan ki kenan da ban fara ɗaukan wannan matakin ba. Because nayi tunanin kina buƙatar space and zan iya miki komai ciki harda kawar da kaina daga kan ki a lokacin da nafi buƙatar ki. Na azabtu da rashin ki a kwanakin da suka wuce duk da kuwa kina kusa da ni, amma for your safety and happiness it was worth it Umry. zan iya cigaba da jira har lokacin da zaki shirya, har lokacin da zan iya gwada miki irin ƙaunar da nake miki a aikace, na baki tabbacin kece duniya ta."

Yayi yunƙurin sauƙa daga kanta sannan ya ɗagota su zauna Amma sai ta riƙe gefen wuyan rigan shi, tana kallon shi cikin idanu dake karanto saƙonni masu yawa.
Dakatawa yayi ya dubeta "Wifey are you sure?"

Bata iya amsawa ba sai lumshi idanunta da tayi hannunta still riƙe da collar ɗin shi har saida taji hannun na dawowa jikinta alamun yana ranƙwafowa kusa da fuskarta.

"If you want me to stop, tap me three times okay?" Yace yana riƙe hannunta da babu sauran karsashi a jikin shi ya bubbuga ƙirjin shi da babu riga a jere sau uku.

Gyaɗa kai tayi amma ta saka ma ranta zata jure, zata yi jarumta itama.
......
*Aicha*

Ƙarfe 8 kiran Rafeeq ya shigo wayanta yana katse mata daddaɗan barcin da ta samu ta maida, ta saka wayan a kunnenta tana daga kwance domin ba isanta barcin yayi ba balle ta miƙe zaune.

"Hello" tace cikin muryar barci.

Shiru taji daga ɗaya ɓangaren har saida ta sake maimaita hello ɗin sannan taji yayi gyaran murya kana cikin muryar shi ta da kowa ya san ta mecece ko bata ce ba, wato isa da taƙama yayi magana, "har yanzu kina gado? Baki da aikin yi ne a gaban ki?"

Kai tsaye ta amsa "Babu ina hutu"

"Hutu? Da wa ya baki?"

Sai ta sauƙe wayan daga kunnenta tana sake duba sunan mai kiran. 'Majestic Annoying Mr French' shine abinda tayi saving ɗin numbern shi a daren jiya.

Bayan Yaseer ya tafi ya barta da karyewar zuciya da disappointment, domin koda babu soyayya akwai darajan ƴan uwantaka bai kamata ya tafi ya barta haka ba, kuma ko mahaifinta bai nime ta ba tunda ya sakankance da Yaseer ɗin zai riƙe mishi amanar ta. Mariama ne ma ta kira kuma itama da Aichan ta kawo mata zancen Yaseer ne yace ta zauna a wurin Rafeeq da sunan aiki sai tace mata toh shikkenan Allah ya tsare sai ta dawo, ta kashe wayan ta. kuma ita da sigan ƙara ta sanar mata.

Miƙewa tayi zaune tana hamma da miƙa ko zai saka taji ta wartsake. "Yanzu zan shirya in fito" tace kawai a wuce wurin, don ba zata jure yayi ta gaya mata magana ba ko kuma yace ta yi masa wani abun.

"Da yafi" ya amsa "amma ki karya da kyau kafin ki fito, domin ni ba kaman Yaseer bane, ba'a min son jiki" ƙitt ya ƙatse kiran. Baki sake tabi wayan hannunta da kallo, lallai ta kusa tayi editing sunan shi ta ƙara ɗan rainin hankali a kai.

Ƙarfe 10 ya same ta a gaban ƙaton ginin mai hawa a ƙalla 12 zuwa 15. Ga sunan da bata son ji kwanan nan manne a saman shi yanda yake shiga idanunta kaman an maƙala ne don kawai ta gani ta shaƙi takaici.

Ɗaga waya tayi ta kira shi. "Ina na nufa?" Ta tambaya bayan ya amsa.

"10th floor, finance department"

Ta ɗauka shi zai turo a shigo da ita ai ko nasu kamfanin babu tsari ne? Ko kuma da ID din YK & Co zata yi amfani su barta ta wuce kai tsaye?.

"Amma ka san bani da ID ɗin ku"

"Kada ki damu ki shigo kawai, duk wanda yayi ƙoƙarin tsare ki ki faɗa masa ke wacece"

Wannan karon ita tayi saurin katse kiran shima yaji abinda ake ji sannan ta wuce ta cikin rotating doors zuwa ciki.

Gashi nan dai hanyar da zata sada ka da elevator akwai guntayen na'urori masu ƙananun ƙofofin nan da sai ka manna ID ɗinka a saman shi kafin su buɗe su baka daman wucewa, amma ko kokarin tsallakawa kayi zai fara ƙaran danger, kuma ga security tsaye a wurin, mai ma zai saka ta tsallaka?.

Sauƙe numfashi tayi ta fara takawa, tun kafin ma a kai ga tambayanta ta ciro ID ɗinta na YK & co tana gwada wa ɗaya daga cikin security ɗin tare da karanta mishi sunanta.
"Aicha Abdou Hamissou"

Sai taga ya danna wani abu ƙofar tayi green ta buɗe har sai da ta wuce tana mishi godiya kafin ya sake suka rufe. Ita da wasu ma'aikata uku suka shiga elevator din, biyu mata ɗaya namiji.

Matan suka fara sauƙa a floor na 6 Sannan ta sauƙa a yanda ya kamata namijin kuma yaya wuce sama.

Office-office take wucewa da ma'aikata cike kowa a cabin ɗin shi yana abinda aka tara su ake biyan su domin shi, a ƙofan kowanne an rubuta rukunin team ɗin da suke ciki, daga Team A, Team B har saida taje wuce na Team C kafin wata ma'aikaciya ta fito daga office ɗin sanye da jan blouse da straight skirt iya guiwa. da murmushi a fuskarta take tambayan ta "Ma'am ina zuwa?"

"I'm here to meet Sir Rafeeq" ta bata amsa.

"Okay this way" tace tana wucewa gaba Aicha na binta a baya tana ayyana ashe ganin shi ma mugun sauƙi gare shi.
Chapter 99 · 0% Book details