Sashe 116
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ta dubi Hajiya Hauwa dake faman tsiyayan hawaye kana ta mayar da idanunta kan takardan hannunta "dukda cewa kin taimaka wajen boye gaskiya wannan kotu ta lura da yanda kika fitar da ita daga ƙarshe da kan ki, saboda nadama da da kuma gaskiya da kika nuna wannan kotu ta rage miki hukunci daga shekara bakwai zuwa shekaru huɗu ko tara na naira miliyan 25.
Sannan za'a biya diyya A bisa dokar VAPP na naira miliyan 15 ga Yaseer saboda shafe shekaru uku a kurkuku ba tare da laifi ba...."
Abinda ya fuskanta yafi ƙarfin Naira miliyan sha biyar ko ruɓin ta, amma Allah ya biya shi, Allah ya kawo shi matsayin da ba don wannan azabar da ya shiga na wani lokaci ba da ba lallai ya taɓa taka makamancin ta ba har abada, shiyasa ga duk wanda yayi imani da Allah every misfortune is a blessing in disguise, sannan kada ka cire rai ga rahamar shi domin jinkirin zuwan shi alkhairi ne.
"..... Naira miliyan 5 ga wacce abinda ya ritsa da ita, saboda raunin tunani da tashin hankali da ta shiga. Kuma wannan kotu tana bada umarni kaman haka; Na farko, a wanke Yaseer Kamal daga duk wani laifi da aka taɓa ɗora masa. Na biyu a buga wannan sanarwan yafiya da ban haƙuri a jaridu, gidan talabijin da kuma kafofin sada zumunta da suka wallafa kamar sa a shekaru goma da suka wuce.
Muryar Umma dake maimaita alhamdulillah cikin kuka mai sauti ya sanar da ni ba zallan zuciyata bace kaman yanda na tsammata.
Yaseer ya kamo ɗayan hannuna ya hada da wanda yake riƙe da shi tuntuni ya riƙe a cikin nasa biyu hakan yayi nasaran karkato da duba na zuwa gare shi.
"Ba laifin ki bane Reina. You're also a victim, ke aka cuta kuma yau na nima mana adalci so you can be rest assured. Komai ya zo ƙarshe" ya sake mun murmushi ba tare da ya lura da kogin hawayen dake taruwa a idanu na ba ya zare hannun shi daga cikin nawa ya miƙe ya nufi mahaifiyar shi ya riƙe ta a jikin shi tana zubar da hawayen daɗi da kuma tunawa da jarabawar da suka shiga kaman ba zasu iya jurewa amma gashi yau ya wuce.
Fuska ta na kife da hannu na, kuka nake yi sosai har saida naji hannun nawa mahaifin a jiki na. "Yanzu zan iya duban idanun ki a matsayin wanda ya cancanci zama uba a gare ki Hafsatu, a yanzu nayi miki gatan da ya kamata kuma ban yi nadama ba ko kaɗan na sani a gaba ma ba zan yi ba."
Sauƙa kasa kawai nayi don bani jin nace zan miƙe kafafu na zasu iya ɗauka na,na kife kaina a kan cinyar shi ina matsar kwalla ba tare da na san abinda kalaman shi suke nufi ba. Amma shi da sauran mutanen da abun ya shafa sun san sadaukarwar da yayi. Ya amince zai kawar da tarin shaidun da suke da shi na cewa Alhaji Salisu su suka tura babbar mota ta bi kan motar shi ta aika shi lahira idan suka amince zasu bada shaida a kan abinda Jamal yayi wa Reina.
Su kuma ganin cewa Daman Jamal ta kare mishi kada suyi biyu babu suka amince, don haka matuƙin babbar motar da suke bin sawun shi na tsawon lokaci da shaidar kuɗin da aka biya shi da sauran shaidu da suka tara duk yanzu zai haƙura da su saboda Yaseer da kuma Reina.
Amma basu san cewa yana da original copy ɗin contract dinnan ba, don shima wani case ne mai zaman kan shi.
.
.
.
"Ko zamu wuce can gidan ne ki zauna tare da daddyn sai dare mu dawo?"
Girgiza kai nayi a hankali idanuna still a kan hanya ban sani ba ko gujewa kallon idanun shi nake yi saboda kunya.
"Toh gidan Ummi fah? Sai in dawo daga baya in dauke ki"
Shima na girgiza kai domin babu da wanda nake son kasancewa a wannan lokacin bayan shi.
Haka muka Isa gidan ya fito ya buɗe min ƙofa kaman ko yaushe yau ko jaka ma ban ɗauka ba na fita. Ya riƙo hannuna muna tafe a hankali har cikin gidan, saida muka yi kaman rabin parlon na ja na tsaya.
It's now or never.
A hankali na sulale a kan guiwowina lokacin da ya juyo ya dube ni. Sai ya gagara cewa komai kawai yana kallona har na samu ƙwarin guiwar motsa fatar baki na. "Kayi haƙuri yaya Yaseer. Kayi haƙuri ka gafarce ni don Allah" tun a lokacin da na samu damar sauƙa daga tudun laifi na domin na dube shi na fara jin sanyi na ratsa zuciya ta. Yau na sauƙe nauyin bakin da nayi tun sake haɗuwar mu Saboda a yanzu ina da yaƙinin na cancanci in nemi yafiyar shi saboda neman afuwa na zai yi amfani. "Ina baka hakurin dukkan laifin da nayi maka kafin da kuma bayan wannan, na tuba, please find a place in your kind heart to forgive me."
Ya ɗan ciza bakin shi cikin rashin sanin abun yi yana jin sauran abun da ya tokare shi yana karasa bajewa yabi iska, kana ya saka Hannu biyu ya ɗago ni tsaye, sai kawai ya shiga min cakulkuli kuma ya riƙe ni babu halin guduwa. Yayi nasarar tsayar da kuka na lokaci guda amma jirin da naji ya fara ɗiba na ya saka nayi saurin riƙo rigar shi na ƙanƙame. "Babyn ka Bae, ka bari dan Allah babyn ka!" Nace ina dariya.
Cakk ya tsaya amma ban lura da kallon rashin fahimta da yake aika mun ba saboda idanu na dake rufe, har saida naji jirin ya ɗan sake ni sannan na buɗe idanu na a cikin nashi, na saki murmushi ganin irin kallon da yake mun.
"Wata na na biyu kenan abinda kayi Research a kai bai zo min ba, shine na sayi strip na duba yau da safe"
"So you mean to say..." Sai ya riƙe baki kawai yana kallo na.
"Ya zuljalalu wal ikram!" Idanun shi ya kai kan ciki na, sai ya saka hannu ya zare hijabin wuya na ya ɗaga rigana yana kallon fatar ciki na, ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah ko hango cikin zai yi daga nan ban sani ba.
"Alhamdulillah alhamdulillah! This is the best day of my life Umry, the very best" yace hannun shi a kan ciki na, idanun shi a cikin nawa. "Allah ya raya mana abinda ya adana mana a nan da rai da lafiya, Allah ya gwada mana ranar da zamu riƙe su a cikin hannun mu"
"ameen ya rabbi" nace ina kwantar da kaina a ƙirjin shi, shikkenan kuma wani Jamal da iyayen shi duk sun fice daga cikin tunanin mu mun sauya su da abubuwan da suka fi muhimmanci.
.....
A tafiyar mu jama'are tare na farko bamu nemi izini bane Saboda kuskure amma a yau bamu nema bane saboda bamu buƙata. Ina zaune a seat ɗin gefen shi a maimakon na bayan shi hannun shi ɗaya a kan sitiyari ɗaya a saman hannuna yana shafawa a hankali.
"Are You comfortable?"
Na gyaɗa kai ina lumshe idanu saboda barcin da yake so ya fara ɗauka na naji iskan hanya.
"Baby na fa?" Yace hannun shi na zuwa kan ciki na amma sai na matsar ina gwada mishi hanya.
"Kada ka zubar da mu babe please."
Ya ɗaga hannun ya mayar kan tuƙin shi. "Kada ki damu ban yi shirin asaran rayuka har uku ba"
"hmm". Na murmusa ina ɗaukan dabino guda ɗaya na saka a baki.
Bayan ciye-ciyen su nama da duk wani abu da na gani a hanya mun Isa Jama'are cikina damm amma ba shi ya hana ni samawa abubuwan da aka kawo mun wurin shiga ba.
Ina gamawa kuma nabi lafiyan gado saida na tashi kafin muka zaga gaisuwa da godiya a mota wannan karon. Da yawa kallo ɗaya zasu yi mun su fara yiwa Yaseer barka da kuma fatan Allah ya raba lafiya kuma nafi bada laifin hakan ma kumatun da nake kan ajiyewa.
A lokacin da na shiga cikin gidan gandun ne goggo take tsokanan Yaseer wai Abidah har yanzu tana jira, ƴan uwa suna ganin ya haɗa biyun ba matsala zaima fi. Yanda ya turbune mata fuska ta sha dariya sosai, yace a faɗawa abidan idan ta samo miji tazo zai yi mata kayan ɗaki amma shikam ko zai ƙara aure bai san a wata shekaran ba.
Bamu taso ba sai bayan Isha yau ma don har na saka ma raina kwana zamu yi oga ya kasa ya tsare.
Muka musu sallama muka ɗau hanya sai na dube shi. "Da yanzu kawai sai muje mu samu Umma da Abbah suna ta jira a gidan mu."
Yayi dariya "sai a sake miki tayin aure na kawai a ƙara ɗaurawa"
Nima dariya nayi ina ƙoƙarin tuna wani shashanci ne ya saka na ambaci sunan Uncle B. "Ranan Umma tayi mun gata, Allah ya saka ma uwar da babu kamanta da ɗumbin alkhairi."
Yaseer yayi murmushi a zuciyar shi yana amsawa da ameen sannan muka cigaba da hira har barci ya sake ɗiba na.
.....
*Bayan watanni shida*
*Abuja*
"Daddy.... Daddy... Daddy are you there?!" fitowa Aicha tayi riƙe da jakar makarantar Najma da snickers ɗinta, a tunaninta ko Rafeeq ya fita ne amma sai ta hango shi zaune a kujeran dining da mug a gaban shi, ya ɗago idanu ya dube ta ba tare da yace komai ba yana dai jira ne ta faɗi cutar ta ya bata magani.
Takaicin shi sosai ya kamata ga frustration ɗin tsohon ciki sai take jin kaman ta jefe shi da snickers ɗinnan daga wurin amma dai tayi ma kanta faɗa ta ƙarasa a hankali ta ajiye masa takalmin a gefen coffee ɗin shi ta juya tayi tafiyar ta. Idan ƴan shirun ne ma suke kusa yau tana daidai da shi. Yabi bayan ta da kallo yanda take tafe tana tura ciki murmushi na suɓuce masa.
Yana zaune a wurin ta fito da yarinyar bayan ta rataya mata jakar sannan ta wuce kitchen zata ɗauko lunch box ɗinta.