← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 117

Sashe 42

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aicha ta ɗago zata tanka ta hango Yaseer dake tsaye a bakin ƙofa da kwalin waya a hannun shi don haka taja bakinta tayi shiru.

A jikinta Reina taji kallo ko ince hararar da yake watsa mata, ta juya a ɗarare suka yi ido huɗu.

Bata kai ga buɗe baki ba balle tayi magana yace "Darling ki same ni a office, ke kuma ina jiran ki a waje" da haka ya juya daman nimanta da yake yi ya saka ya shigo kitchen ya bata wayan da ya saka aka siyo mata.

Hankali a tashe ta fice daga kitchen ɗin, Aicha a maimakon taji daɗi sai takaici ya daɗa kamata don sun yi ne a kan a tare zasu fita yau su fara duba masauƙin baƙin Cairo ɗin kafin su wuce YK & CO. Amma gashi yanzu Reina tayi musu sanadin changing plan.

Daga bakin ƙofa tayi ma daddynta sallama, taso tayi ma Umma ma Amma sai ta haura sama kuma kada ta ƙara ɓata ran yaya Yaseer.

Ta same shi har ya shiga mota ya kunna itan kawai yake jira.
Salati take jerawa a ranta hannu na rawa ta shiga gaban motan ta rufo ƙofa, ya fara tafiya ba tare da yace mata komai ba.

"Dan Allah kayi haƙuri yaya Yaseer wallahi ba zan sake ba" tace bayan sun fita daga unguwar cikin muryar da tsoro ya karya shi tana rungume da jakan ta tsamm a ƙirji dukda ba tsananin gudu yake yi ba.

Har ta cire rai zai kula ta kafin yace "wato saboda kin raina ni, Saboda ban isa ba, jiya-jiya na kafa miki doka amma daga wayewar gari har kin saka ƙafar ki kin tsallaketa ko?"

"Wallahi ita ce ta fara cemun wai kowa da matsayin shi menene shine nace mata ni ba gurbin ta nake son cikewa ba, kuma naga tana min wani gani-gani amma wallahi ni ba faɗa naso yi da ita ba"

Rage gudu yayi ya juya ya kalleta da kyau, ya daɗe yana kokwanto a cikin ran shi a lokacin da yake bibiyar ta, amma a haɗuwar su na jiya wani ɓangare na zuciyar shi ya fara ayyana mishi ta canza, ashe dai mai hali bayi canza halin sa.

Ƙwafa yayi suka cigaba da tafiya, ganin ya ɗauko hanyar Awala tayi tunanin ko ajiyeta a bus stop zai yi ta wuce makaranta Amma sai gani tayi sun karyi kwanan Fadaman Mada.

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Dan girman Allah kayi hakuri yaya Yaseer dan Allah, wallahi Tallahi ba zan sake ba kaji na rantse"

"Ba kin ɗauka wasa nake ba?"

Kuka ta fashe dashi wiwi "Wallahi ba zan sake ba dan Allah kayi mun rai, na koma gidan nan yanka ni zasu yi."

Ta riƙo hannun shi ɗaya kukan ta na daɗa ƙaruwa ganin sun kusa yankan layin gidan.

"Ah-ah, zubar da mu zaki yi mu mutu tare?" Yace rabin hankalin shi a titi rabi a kanta gashi ya koma tuƙi da hannun hagu.

"Na shiga uku yaya Yaseer kayi haƙuri dan Allah"

Sai da suka fara hango gidan Alhaji Salisu kafin yayi parking ganin tana niman rikice masa har tana shiɗewa.

Juyi take yi a cikin kujerar ta tana niman yanda zatayi ta samu numfashin ta ya fito tana ƙara runƙume jakar ta a ƙirji.

"Ke Lafiya?" Ya ɗauka shiri ne daga farko don kawai ta samu ya fasa kaita amma kuma gashi ya tsaya ai sai ta dawo dai-dai.

"Hafsat!... Reina!...."

Da sauri ya ɓalle Marfin mota ya fice sai ganin kan shi kawai yayi har ya zago ya durƙusa a gaban ta. Ya riƙo kafaɗun ta amma sai niman zubewa take yi kaman gwate, har idanunta sun fara kakkafewa a sama.

Cikin rasa abun yi ya rungumo ta jikin shi sannan ya miƙa hannu ta ɓangaren tan ya ɗauko wayan shi da ya ajiye a cikin motan ya shiga kiran agajin gaggawa.

"Hafsat stay with me please... Reina!" Ya kira ta a ɗimauce gabaki ɗaya ya rasa yaya zai yi mata domin bai san tana da wani matsala mai kama da wannan ba shi, bai taɓa tashi mata a kan idon shi ba.

Gashi babu waya a hannunta balle ya kira ya tambaya, ya tambayi waye ma toh? Ƙara rungume ta yayi a jikin shi cikin rasa Abin yi ya koma kiran Muhammad.

Yana ɗauka address ɗin da suke ya fara bashi kafin ya shiga sanar da shi abinda ke faruwa sama-sama.

"Babu mota a hannun ka ne?" Muhammad ɗin ya tambaya da mamaki.

"Ba zan iya tuƙi ba Muhammad ba zan iya ba" yace kaman zai fasa Ihu.

"Okay okay gani nan zuwa yanzu"

.....

*Reina*

Sheshsheƙar kukan da ke shiga kunnen ta ya saka ta buɗe ido a hankali, ko ba'a faɗa mata ba nan ɗakin asibiti ne, ba tare da ta juya ba tace "Feenah kin damen"

Ɗaka mata duka Safina tayi, Reina ta saki ƙara, sai kuma ta shiga bata haƙuri tunawa da yanzu ta farka.

"Daman hankali na bai kwanta ba tunda kika tafi naji shiru, yanzu kuma zaki ƙara min wani tashin hankalin" cewar Safina cikin muryar kuka tana zungurin hannun Reina.

Yunƙurawa tayi zata tashi Safina ta miƙe domin ta taimaka mata ta zauna sai a lokacin idanunta suka sauƙa a kan Yaseer dake zaune a ƙuryar ɗakin ya zuba mata na mujiya.

Ɗauke dubanta tayi daga cikin nashi.
"Ai gani ban mutu ba, hankalin ki ya kwanta"

Ta sake kai mata duka "Ina maganin ki? Ba Uncle ɗin Zaheera yace kina yawo da shi a jakar ki ba?"

"Wayyo Feenah hannun ki akwai zafi fah! Ai yana cikin jaka na ɗin ki duba ki gani ma"

"Toh sorry sorry, ina ta shirin zan zo sabon gidan ku mu haɗu ne ma yau idan baki zo school ba sai kuma Daddy ya kira ni wai kina asibiti, wallahi ana tsaka da lectures na fito hankali na ya tashi idan kika mutu yaya zan yi da saurayin ki da ya bani amanar mmmm" Reina tayi saurin saka tafin hannu ta rufe mata baki tana kai duban ta kan Yaseer da dariyar yaƙe a fuskarta kada idan ma ya fasa kaita gidan Umman Zahran ne Safina ta saka ya kaita.

Miƙewa yayi ko a jikin sa tunda ya san da zancen Uncle B kuma ya san ba zasu kai labari ba koda bai katse musu hanzari ba Saboda soyayyar yarinta Reina take mishi, shikuma ya samu yarinya ba wayo shine zai yi ta brainwashing ɗinta.

"Yanzu Yaya kike jin daɗin jikin?" Ya tambaya yana maida wayar sa cikin aljihu.

"Garas nake jina zama mu iya wucewa school yan.."

Hararan da ya watsa mata ya saka ta ja bakin ta gimtse.

Ya ƙarasa inda aka ajiye mata jakanta ya buɗe, cikin tarkacen ciki ya ɗauko containern maganinta sannan ya cire sabon wayan ta da ya saka sim ya kunna daga aljihun wandon shi, ya saka a cikin jakar suna kallon shi, sannan Ya fice da goran maganin a hannu.

~~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

72

~~~~~~~~~~
_Pour te faire comprendre_
_(To make me understand you)_
_Tavais juste à lever le cil_
_(all you had to do was raise your eyelashes)_
~~~~~~~~~~

Saida ya fice Safina ta magantu, harda ƙara matso da kujerar ta kusa da gadon Reina tayi ƙasa da murya kana ta tace "Wannan shine Yaseer ɗin?"

Da murmushi a fuskar ta Reina ta gyaɗa kai.

Safina tace "ya rabb, ya haɗu" ta juya tana sake kallon ƙofar da ya rufo musu. Kana ta miƙe ta buɗe jakan Reina ta ɗauko wayan da ya saka mata a ciki.

Juya wayar take yi baki buɗe "Hajiya kin faso gari, wannan ko ban gane wani model bane tabbas ya girmi nawa nesa ba kusa ba"

Ta miƙa ma Reina ta gani.

Karɓa tayi itama da bayyanannen murmushi a saman fuskar ta, ashe abinda yake cewa zai batan kenan? "Ai ina ta son in kira ki muyi hiran amma na gagara tambayan Daddy na aron waya."

"Gashi ai Allah ya kashe ya baki. yanzu kuna ina ne keda Daddyn?"

"A Gidan su muke zaune"

Safeena ta waro idanu "A can zaki cigaba da zama kenan?"

Gyaɗa kai Reina tayi alaman tabbatarwa "Idan ma zamu tashi hala sai gaba, don Daddy bayi da lafiyar da zamu zauna mu kaɗai" ta ƙarashe tana kai mayafin ta jikin hancin ta don kaman har a jikin shi take jin ƙamshin.

Da farko ta ɗauka zaman da yayi a ɗakin ne ya saka har bayan fitan shi take iya shaƙar ƙamshin sa, amma yanzu ta fahimci daga jikinta yake fitowa.

Safina taci gaba da cewa "Nifa na shiga ruɗani da Abinda ya faru, da wani ne ma ya bani labari ba yarda zan yi ba, amma ina taya ki murna ƙawata"

"Lamarin akwai ɗaure kai. Amma yaya aka yi nazo nan Feenah?" Ta ɗago idanu ta zuba mata.

"Ta ina zan sani? Ban fi 30 minutes da zuwa ba fa amma ba zai wuce shine ya kawo ki ba"

"Yanzu ƙarfe nawa ne?" Sai bayan ta tambaya kuma ta tuna da wayan hannunta ta danna shi ya kawo haske idanun ta suka sauƙa a kan lokaci ƙarfe 10:14 ta waro ido. "Kuma a nan kika samu yaya Yaseer?" Cikin ranta tace Shi da ake jiran shi a office?.

"Eh, shi da wani a waje, ɗayan ne ma ya je ya shigo da ni" sai kuma ta saka makirin murmushi tana ɗage mata gira "ko dai ko dai? Dukda lokacin da nake kuka naji yana waya da matar shi, amma na lura ke farin jinin masu mata da yara kike da shi, hakan ma babu komai"

"Yaya Yaseer bayi da mata, kuma Kuka kike yi ko dai gulma?"

"Kukan nake sai kunne na ya ɗauko min maganar shi ba tare da na so ba. Amma yana da wata budurwan don naji yana kiran Darling"
Chapter 42 · 0% Book details