Sashe 68
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A yau kuwa taga alfanun karatun da yaya Yaseer yake saka ta a kullum don tana fara bita take jin yana dawo mata tiryan-tiryan, tuni tayi wa Safinah fintinkau, sai handouts ɗin da aka cire kwanan nan ne suke mata a matsayin sabo Amma sauran duk ta riga da ta iya su.
Sai bayan maghriba ta fito daga ɗakin.
Umma sau biyu tana duba ta a tsakani tunda tace bata jin daɗi kada ace da gaske ne dauriya kawai take yi amma sai ta sauƙe ajiyan zuciya idan taga tana karatu, har tambayar ta take yi ko tana bukatar wani abun sai tayi godiya tace babu.
Ta tuna da umarnin Uncle B da ya turo saƙo ya jaddada mata. a maimakon ta tura hotunan yaya Yaseer cikin kwandon shara sai ta samo abun ɓoye hoto ta adana su a can yanda ita kaɗai ta san lambobin sirrin kayan ta.
Bayan an ci abincin dare ta ɗan zauna a parlo suka yi kallo a netflix tare da yaran gidan don ƙwaƙwalwar ta ya huta, tukunna ta tashi ganin Yaseer ya shige study Room taje ta ɗauko kayan karatun ta tabi bayan shi.
Farko ta fara ɗar-ɗar a ɗakin karatun a tunaninta shima sabon yaya Yaseer zata gani Amma sai ta ga tsohon nan ne tsayayye mai tsanantawa bai canza ba. Gashi yayi fuska yana abinda ke gaban shi ko duban ta bai yi ba dukda a ƙasan zuciyar sa yana muradin hakan amma komai yana da lokacin sa, akwai lokacin soyayya mai yawa a gaba yanzu lokacin tallafawa goben Reina ne.
Ganin yanda ya fuske sai itama ta shiga taitayinta tazo ya duba abinda bata iya ba ya koya mata ta koma wurin zamanta tana tisawa. Tayi karatu sosai har sai da barci ya ɗauke Yaseer, sai 12 ta zo ta ɗaga shi ta hanyar ƙwankwasa teburin da ya kifa kai Sannan tayi mishi sallama don itama idanun ta sun fara mata nauyi.
Sai a lokacin ya dube ta da murmushi ya lumshe idanun da barci ne fall a cikin su amma ya san da ya hau kan gadon shi zasu wartsake.
Yace "good night Ma Cherié"
Ta juya da murmushi ta bar study Room ɗin, kuma bata kwanta ba sai da saƙon shi na dare ya shigo wanda yake mata fatan barci mai daɗi da kuma jaddada soyayyar shi a gare ta.
Tayi ƙoƙarin jin daɗin barcin ta kaman yanda yayi mata fata kuma an ci Sa'a Uncle B ya ɗaga mata ƙafa bai kira da daddaren ba. Don haka har da tayi sallan asuba tayi azhkar ɗin safiya ma barcin ta koma sai 8 ta farka tayi wanka ta shirya zuwa 9 ta sauƙo domin karyawa Idanun ta suka sauƙa a kan Aicha zaune a gefen Yaseer.
Shikkenan cingam ta dawo, Ta ayyana a ranta. Gaisuwan da ta shiga yi bayan ta iso wurin ne ya karkato da hankalin Yaseer gare ta daga hotunan biki da Aicha ta saka shi a gaba tana gwada mishi a dole, shi ya ji daɗin zuwan Reina don ceton shi tayi don haka ya miƙe daga kujeran shi yace ta zo ta zauna sannan ya koma ta ɗaya ɓangaren inda ƴan uwan shi maza suke zaune. Da gefen ido Umma da Abbah suka bishi da kallo sannan suka haɗa ido Umma ta ɗan taɓe baki.
Aicha bata bi ta kan Reina ba ta cigaba da gwada ma sauran mutane hotunan tana basu Labarin bikin da taje na wata cousin ɗinta kuma kawar ta a Zinder.
Saida yazo kan Irfan ne ya miƙo ma Reina yana faɗin itama ta gani. Scrolling ɗaya biyu kawai tayi ta mayar wa Irfan ɗin wayar tana faɗin "Masha Allah sun yi kyau Allah ya bada zaman lafiya" daga nan ta mayar da hankalin ta kan abincin ta, Aicha kuma kallon tuhuma take bin Irfan da shi na ganin tabbas fa ya canza party yanzu.
.
.
Babu wanda ya san wainar da ake toyawa tsakanin Reina da Yaseer bayan iyayen su sai Aicha da ta sanya musu ido take gane wasu abubuwan, amma sanin Yaseer daman ba fasa son Reina yayi ba kuma ba bayyanawa zai iya ba sai bata bawa abinda taga ya ƙaru a kan na da muhimmanci ba, wuyanta a bawa Uncle B dama ne ya kawo sadaki ya ɗauke abar shi a basu space su sha iska.
Haka ta fara exams cikin nutsuwa da kwanciyar hankali gashi Allah ya gani basu bata wani wahala Saboda ta san abinda take yi sosai.
Basu fasa wayan tsawon lokaci da Uncle B ba Amma ta samu ya ɗan ɗaga mata ƙafa shima saboda jarabawa.
Yaseer ya kan kirata a waya amma sai ya duba lokacin da ya dace yanda ba zai shiga hakkin ta ba, bayi kiran ta lokacin barci, lokacin Sallah, lokacin da yake da yaƙinin tana karatu ko zata shiga zana jarabawa sai dai yayi mata text na addu'o'in nasara da kalaman sanya nutsuwa domin ta samu nasarar rubuta abinda ya dace.
Sannan ko zasu yi wayan duk zaƙin labari sun gama dadewa minti 30 ba wai don yana isar shi ba sai don yana ganin hakan shi yafi dacewa a matsayin da suke yanzu, idan ta tsayar da shi a gurin iyaye toh nan zasu iya zarcewa zuwa awa kuma zai iya ƙara yawan kiran ta da yake yi a rana zuwa biyu ko uku amma ba za'a taɓa asarar awa biyu da rabi sau bai san adadi ba da shi, wannan ai hauka ne.
Sai dai fa lokaci yana niman ƙure masa ba tare da ƙwaƙƙwaran amsa daga wurin Reina ba. kwana 3 kawai a rage mishi a sati biyu, gashi bayi son takura ta kuma bai ɗaura ɗamarar jurar rasa ta ba. Zai yi iya ƙokarin sa wajen ganin a kwana ukun nan komai ya canza ya tafi yanda yake so, kuma duk son da yake ganin yana yiwa Reina bai saka ya fasa addu'ar alkhairi a wurin ubangiji ba har yanzu.
.....
Driver ɗin Yaseer ne ya zo daga office ya ajiye ta a gidan su Safina da ta sanar da shi zata je su yi karatu tare a can ba wai don wani abu ya samu malam Nuhu ba.
Aminiyar ta tazo ta tarbe ta tun daga bakin gate suka rungume juna sannan ta rike mata jakan bayan dake ɗauke da kayan karatunta suka shiga ciki.
Kamar kullum mahaifiyar Safina tayi maraba da ganinta sannan suka wuce ɗakin ta suka rufo ƙofa bayan ta shigar musu da abun motsa baki.
"Menene abun rufe ƙofa mu da zamu yi karatu?" Reina ta tambaya tana dariyan mugunta don ta san dama gulma ke cin Safina kuma bata da ƙwarin guiwar zuwa gidan su yaseer ta ji kanun labarai domin ido da ido ya fi mata daɗi, ga Maama ma a gidan sannan ba zata iya jira sai zasu rubuta jarabawan gaba ba saboda an samu tazara sosai a tsakani wannan karon.
Safina ta harare ta sannan ta dawo kan gadon tana ture takardun da Reinan ta fara bazawa cikin ƙaguwa tace "shafa mun don Allah mai ake ciki?"
Dariyan ƙeta reina tayi ganin yanda Safina ta matso kaman zata shige cikin ta tace "ke ma zan saka ki bawa Yaya Yaseer haƙuri don ba zan iya da kaina ba Allah."
"Ban...gane ba!"
~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
90
~~~~~~~~~~
_Afin de te voire_
_(So that I could see you)_
_même dans un sommeil eternal_
_(even during an eternal Slumber)_
~~~~~~~~~~
"Ina nufin zan amince na auri Uncle B kawai, yaya Yaseer ya je ya nemi wata daban"
Safina ta sha kunu "Amma baki cikin hayyacin ki ko? Idan wasa kuma kike toh dan Allah ki bari"
Dariya kawai Reina ta cigaba da mata kaman zautacciya, Safina kuma darajan gidan su tazo ya hana ta kai mata hannu.
"Ba zan ce baki da wayo ba don Abinda kike ƙokarin yi yafi kama da rashin hankali idan har da gaske kike, kuma Wallahi kika kuskura kika bari Yaseer ya kuɓuce miki sai kin yi kukan jini saboda nadama. Yo me aka yi aka yi ki Hafsatu? Kin ɗauka ke ɗin na musamman ne da idan nagartaccen mutum kaman Yaseer ya rasa ki ba zai samu wanda suka fi dubun ki da komai ba? Ni banda makanta irin na so ma na rasa mai ya gani a jikin ki Wallahi.."
Sauyawan dariyan Reina da kuka mai zafi ya saka Safina tsayawa da kurkure ta da take yi, ga hawayen dake bin kuncin ta yana ɗiga a gaban rigan ta wanda ɓacin rai ya makantar da Safinah bata lura da fara zuban su tun tana sheka dariya ba.
Lokaci daya yanayin ta ya koma na damuwa, ta ƙara matsowa, ta riƙo hannun ta cikin nata tana share mata hawayen da basu fasa zuba ba.
"Wani abun yayi miki ne? Daman maza kina ganin su duk halin su ɗaya babu kirki a cikin lamarin su, sai kina kallon mutum na Allah a fuska Amma idan ya zuba miki duniyanci sai kin ɗaura hannu a ka kince wayyoo Allah, amma Yaseer ya bani mamaki Wallahi" ta ma since masa rawanin yayan da take ganin shi da shi.