Sashe 30
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuɗin ta fara duba kana ta ɗago ta dube shi a razane, bakin ta ya kasa furta komai, kukan ma a yanzu ya tsaya, ƙoƙari ma take yi ta tuna menene sadaki?. Ta taɓa jin kalmar tabbas amma ta manta ma'anar ta.
"Karɓi mana" ya gyaɗa mata kai yana ɗaura mata kuɗin a hannun ta, ita a yanzu ma ta manta me ake yi da kuɗi, sunan shi kuɗi ta tuna amma ta manta amfanin shi, gani ɗaurin takarda kawai take mishi.
Da ya samu ta ƙarba ɗin sai yace "toh jeki ki huta, mahaifin ki ya saka miki albarka, Allah yayi miki albarka.
Haka ta miƙe tana waiwayen shi ko zai kece da dariya yace wasa ne ta dawo, amma babu abinda ya canza daga murmushin fuskar shi har ta kusan buguwa da ƙofar ɗakin, Maama ta dakatar da ita sannan ta buɗe suka shiga.
.
~~~~~
*Seemahwrites ✨*
63
~~~~~~~~~~
_I Don't blame you_
_But I can't change you_
~~~~~~~~~~~
*Uncle B*
Yau ma haka ya wuni a wurin basu bashi permit ɗin ba, rana na huɗu kenan da yake jigilar su yarje mishi ya tafi sun ƙi, wai sai da abu ya kankama zai buƙaci tafiya. Yana da zaɓin ya ajiye komai amma yana tsoron aiki tuƙuru da yayi ba dare ba rana na kusan shekara ya zama a banza. Sannan a contract da yayi signing na fara aikin akwai dokar cewa duk wanda ya zaɓi ya janye daga aikin zai biya taran wasu maƙudan kuɗaɗe masu yawa saboda asaran da zai jawo musu. Hakan yasa yaga gwamma ya haƙura ya lallaɓasu su bashi hutun kwana uku yaje ya juyo kaman yanda ya buƙata, gashi shi bai wuni a bakin aiki ba kuma basu bashi abinda yake so ba. Kan shi duk ya ɗau caji sannan kunya yake ji, kunyar Reina yake ji kafin Ummi, ko iya ɗaga waya ya kira ta ya kasa don bayi da abinda zai ce mata, don haka ya daina ɗaukan kiran Ummi ma kada itace take amfani da wayan ta kira shi, zuwa yanzu yana da tabbacin wayan ta bayi wurin ta da ta daɗe da kiran shi da ita.
A gajiye ya ɗauki hanyar gida yana ji kaman ya ɗaura hannu a ka yayi ta zabga kururwa ko zai samu sa'ida. Rage gudun motar shi yayi Saboda kiran da ya shigo wayar shi, ya ga numbern Nigeria ne yake yawo a kan screen ɗin, zai iya kasancewa Reina ne don haka yaƙi ɗauka yaci gaba da tuƙi ya barta ta tsinke.
Bayi da uzurin da zai bata.
Saƙo ne ya shigo ta layin, ya samu wurin da ya dace yayi parking kafin ya duba.
'Mahaifin Hafsatu ne, ina son magana da kai' shine abinda saƙon ya nuna.
Ba wai fahimtar abinda ya karanta yayi ba amma sai ya bi kiran tunda ba Reinan bace.
Shi ya kira amma ta ɗaya bangaren aka mishi sallama ya amsa a tsanake.
"Sunana Tahir Kamal. Mahaifin Hafsatu, mahaifin ta Uba"
"Wata Hafsatu?" Ya sami kan shi da tambaya yana ƙoƙarin tuna wacece Hafsatu da yake da hurumi da uban ta har zai kira shi yana jaddada masa matsayin sa.
"Hafsatu Reina, yarinyar da take wurin ƴar uwar ka Hauwa, nine mahaifin ta"
Uncle B yayi shiruu shima Alhaji Tahir bai sake cewa komai ba yana jiran ya gama digesting information ɗin da ya bashi.
Shikuwa ayyanawa yake yi a ran shi Lallai Hauwa taci uwar raina masa hankali. General ya saka an garƙame Jamal ɗin ma ba zata saduda ba ko?.
"Shekarun Mahaifin ta 6 da rasuwa, kai yaushe ka haife ta?" Sai Alhaji Tahir ya saki murmushi don maganar ya bashi dariya.
"Ka san mahaifin nata a fuska?"
"Ɗan Nigeria mai shekaru na ba zai gaza sanin TK kingdom ba"
"Toh bari in kira ka video call" yace tare da converting kiran, uncle B yayi accepting lokacin da Alhaji Tahir ya bayyana a kan fuskar wayan shi, yana zaune a kan keken guragu.
Uncle B bai san hannun shi ya kai kan bakin shi ba, kunnuwan shi dai sun jiyo masa addu'an da ya kama nanatawa cikin kaɗuwa.
"Ka gaskata nine mahaifin Hafsatu a yanzu?"
"Amma how? I mean.. how?" Ya sake maimaitawa domin tambayar da ta dace ɗin kenan ta yaya?.
"Wannan bayani ne mai zaman kan shi amma a yanzu alfarma nake son kayi min na cire hannun ka a cikin abinda yake faruwa, ba taimakon mu kake yi ba, ƙoƙarin wargaza mana shiri kake yi. Don haka ka roƙi mahaifin ka ya sake Jamal, zamu ɗauka daga nan"
Wani irin kallo uncle B yayi mishi, ko kama ce wannan toh ta ƙazanta da Alhaji Tahir ɗin da ya sani duk da yanzu ya rage jiki kuma girma ya kama shi.
"Umm dan Allah malam, i have a lot on my plate right now, bani da lokacin ƙarawa da wani nonesense Please, ka faɗa ma ita wanda ta biya ka kayi putting wannan act ɗin itama bani da lokacin ta a yanzu. Hafsah ne a gaba na kuma duk wanda ya tsaya min a hanya zan taka kan shi kafin na wuce"
Ya katse kiran, Alhaji Tahir ya dubi Yaseer da gane yanayin da yake ciki a kan fuskar shi zai yi wuya, shikuwa ya kasa ɓoye murmushin shi yanda yaji Uncle B yake depending sarauniyar shi yace "sake kiran shi"
Babu musu Yaseer ɗin ya sake kira ya ajiye wayar yanda zata fuskance su da kyau sannan ya tsaya a gefen Alhaji Tahir ɗin duk da ba wai son ganin Uncle B yake yi ba.
Kamar kiran zata tsinke kafin Uncle B ya sake picking wannan karon Yaseer ne yayi magana.
"sunana Yaseer Kamal Jama'are. Ka tura a duba ni a gidan maza a ranar.." ya karanto mishi kwanan watan da barrister yaje duba shi don su sake buɗe case ɗin bisa sadaukarwa da magiyar Meesha. "... Aka sanar maka bani nan an fitar da ni" ya ƙarasa yana tunawa Uncle B rana da lokacin da har ya ɗau hanyar Kd ya juyo ya dawo.
A daren ranan Meesha tayi texting ɗin shi da "Thank you" a tunanin ta shi ya fitar da Yaseer, kuma har yau bata sake tada masa da maganar ba kaman yanda suka yi alƙawari.
Da wannan bayanin Yaseer ya ja bakin shi yayi shiru Alhaji Tahir yaci gaba da faɗin "girman lamarin nan yafi ƙarfin tunanin ka, ba zallan Reina bace a ciki, ba zallan dukiya bane da idan kaji yawan ta sai ka girgiza duk arziƙin ka, munaƙisa ne da ya saka ɗan uwa ya kusan hallaka ɗan uwan shi, ya saka wanda bai jiba bai gani ba sadaukar da ƙuruciyar shi, ya fuskanci horon shekaru 3 a kan laifin da bai aikata ba kuma har yanzu bai huta ba.
Uncle B sai ya kalli Yaseer ta cikin wayar, hakan ya fahimtar da Alhaji Tahir ya san wani ɓari daga cikin gaskiyar abinda ya faru, Reina ta faɗa mishi. Shima Yaseer tunanin da ya shiga kan shi kenan sai kawai ya juya ya buɗe kofar ɗakin ya fita tare da janyo musu ya rufe a bayan shi.
......
Yanzu hawayen Reina sun kafe ya koma Safina da Maama ne masu kuka su da basu yi ya ishe su ba kenan.
Yanzu ma kofi ne a hannunta ta ƙura ma madarar ciki idanu tun yana da ɗumi aunty Zeenat ta miƙa mata amma take ta kallon shi har ya huce ƙalau.
Aunty Aina ce ta shigo da kwanon farfesun kayan ciki ta ga yanda Safina da Maaman suka jibgu mata a jiki.
"Wani iskanci ne wannan? Safina Ba zaki je ki karɓo su cake da donut ɗin souvenir a gidan mama ba (ƙanwar Ummi) sai dare yayi? Kema Zainab ba cewa nayi ki raka ta ku tafi tare ba?"
"Ni Wallahi a nemi wata taje" cewar Safina tana daɗa shigewa jikin Reina, duk sun takura ta amma bata ma jin shi a kan takuruwan da zuciyar ta yayi ya motse a ƙirjin ta yana yawo da duk motsin da zata yi shiyasa bata motsawan ma sai ya zamo dole.
Tsaki ta ja ganin da gaske ɓata mata lokaci zasu yi ta miƙa ma Reina roban hannun ta bayan ta saka hannu ta ɗauki hanta ɗaya ta kai baki. "Ungo karɓi kici, kafin ki bari yunwa ya kashe ki"
A duk cikin muhimman tambayoyin dake kan ta da kirjin ta, kaman su mai yasa zasu yi mata aure ba tare da sanin ta ko amincewar ta ba? Tambaya ta farko ma shine me yasa za'a aura mata Jamal? Her attempted rapist. Mutumin da ace ta aure shi gwamma ta mutu a rufe ta a kabari amma gashi suna kallo tana shirin mutuwan ko a jikin su.
Sai ta samu kanta da tambayar "me yasa zaku saka min abinci a rubber kaman almajira? Babu bowl ɗin cin abinci ne?" Hawaye suka rufa ma kalamin bakin ta baya.
"Tohh" Aunty Aina tace tana taɓe baki, ta ajiye mata rubbern a kan mirror ɗin Ummi idan taji yunwa da kyau zata ci ita bari taje ta aiki ɗaya cikin yaran ta ko mazan ma, sannan ta saka hannu ta sake ɗaukan hanji zata kai baki lokacin Ummi ta shigo tana juya kai, wannan mugun hali na Aina tayi nisan da ba zai iya barin ta ba, shiyasa babu cikin al'ummar da zata shiga hidima ya haɗa su basu yi Allah wadai da halin ta ba, gashi zubar da girma yake yi a gaban kowa har wanda suke ƙasa da kai suka lura baka iya dauke ido daga abunda ba naka ba basu baka girman da ya dace.
Mayar da hanjin cikin kwanon Aina tayi kafin tazo ta wuce ta gefen Ummi da ta haɗe fuska, tana dariyar yaƙe.
Sai da Aina ta rufo ƙofa kafin Ummi ta ƙaraso jikin gadon ta zauna, tana jin yanda Safina da Maama suke sheshsheƙar kuka.
"Ku tashi kuje ku ɗibo abinci, itama ku kawo mata kuma ku saka taci"
Yanayin muryar Ummin ya saka basu musa ba duka suka miƙe domin a dake tayi maganar.