← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 117

Sashe 55

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safina dai ta samu ganin list ɗin bayan wani dake dubawa a gaban ta ya matsa, ta gani a jere suka ɗauka mutum ashirin ɗin sama wanda ita ce na 19 kafin wata ta fauce takardan a ranar Thursday, kuma bata samu ya dawo mata da sauƙi ba shiyasa Reina ta samu kanta a na 31 sai dai abun mamaki bayan mutane 20 ɗin farko da aka ɗauka ita ta zo a na gaba.

Zargin class rep suke yi da shi ya saka sunan ƴammatan shi a ta gaba-gaba aka dauke su bayan ko shi da kan shi bai samu shiga ba.

"Amma ai na faɗa muku mutane 200 kawai zasu ɗauka! Departments nawa muke da shi a school ɗinnan? Baku gani wasu departments ɗin ma wa'inda aka dauka ko mutane 5 basu kai ba? A hakan ma sun ƙara mutane 51 a kan ɗari biyun da suka ce shiyasa muka samu har haka, idan kuna ganin ban muku ƙoƙari ba ku je da kanku ku saka su dauke ku" ya ja tsaki ya nemi wuri ya zauna, ya barsu su cigaba.

Safina dai da Sauran wa'inda suka ga sunan su sun yi haraman tafiya don karfe 10 za'a fara, sai dai ganin har yanzu Reina bata ƙaraso ba ta roƙi wata da suke mutunci su rike musu seat ɗin mutum biyu.
.
.
Reina tana ɗaukan wayan Safina da a yanzu ranta ya fara ɓaci ganin kowa ya shiga har motan baƙin sun iso bata iso ba ta hayayyaƙo mata "Haba kekuwa! da kika san ba zaki zo ba ai da baki ce in jira ki ba."

"Kai kina da mita wallahi, ai tunda nace miki gani sai ki ƙara hakuri ko? Ummi ne tace na tsaya in ga an ɗauki kayan nan in kira yaya Yaseer ɗin in faɗa mishi kafin in tafi kuma sai yanzu suka zo. In 30 minutes max na iso ina a babaji ne?"

Jin haka Safina ta nemi wurin zama kawai, tunda ta san kafin a gama introduction da bayyana manufar program ɗin zasu ɗauki lokaci amma daga yau shikkenan gobe wucewa zata yi ta barta.

Can kuwa sai ga motan gidan su Yaseer ya ajiyeta. Ta ɗan ƙaraso tana washe ma Safina baki yanda taga take hararar ta.

"Sorry my Feenah" ta rungume Safina da tayi ƙwafa kawai sannan ta ja hannun ta suka ratsa tsakanin manyan motocin da aka yi parking a wurin suka shiga hall din dake gaban su.

Sai da suka bada sunan su ma security da aka saka a waje suka duba suka ga suna cikin list sannan suka basu wani card suka musu izinin shiga.

Wurin ya sha decoration kaman wanda za'a yi biki, gashi ya cika damm babu haufi sune ƙarshen shigowa don haka suka nufi yanda suka hango class mate ɗin su a row na huɗu da empty kujeru guda biyu a gefen ta an ɗaura musu jakakkuna.

Damuwan su suyi su Isa wurin kafin su mayar da hankali a kan abinda ake yi da wa'inda suke yi ɗin, lokacin da Muryar shi ya karaɗe speakun dake duk wata kusurwa na hall ɗin, Tayi saurin juyawa ba tare da ta shirya ba.

Yaya Yaseer ne cikin beige Suit da wani gilashin da yafi wanda ya saba sakawa amsar fuskar shi yana riƙe da mic a saman podium.

Idanun shi a kanta yaci gaba da bada speech ɗin shi da ka, ita kuwa taci gaba da tafiya tana kallon shi bata san ina take jefa ƙafafun ta ba sai ji tayi taci tuntuɓe tana niman kaiwa ƙasa.

"Reina CAREFULL!" yayi shouting ta cikin mic yana niman sauƙowa daga kan stage ɗin baki ɗaya.
Ya kuwa yi nasaran jawo mata hankalin kowa zuwa gareta.
~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*
81

~~~~~~~~~
_Est-ce que tu maimes?
_(Do you love me?)_
_J'sais pas si je t'aime_
_(I don't know if I love you)_
~~~~~~~~~~

Shikkenan daman ta shiga bakin ƴan ajin su wai tayi auren kuɗi, har zuwa ake yi wurinta neman tabbaci, yanzu kuma Yaya Yaseer zai saka ta a bakin ƴan makaranta suce shine mijinta ma ko wani abin.

Daɗin ta ma ba'a santa da Reina sosai a school ba tunda nickname ɗin gida ne, ko Safina ma tafi kiranta da government name ɗinta Saboda haɗuwan makaranta suka yi, don haka Saurin ɗauke kanta tayi ta gyara ta cigaba da tafiya har ta isa wurin zaman ta, masu jakan suka ɗaga ta zauna kafin ta ɗago ta ɗago ta dubi Yaseer dake danna wayan shi cikin waskewa ya ɗaura yanayin damuwa a kan fuskar shi kamar wanda aka turo masa wani abun ɗaga hankali.

Tana shigowa ya ɗaura idanun shi a kanta ya manta a inda yake, bayi ganin kowa sai ita, a hakan wai yayi alƙawarin fara kallon ta a matsayin ƙanwar shi kawai. shaff ya manta da Mic a kusa da bakin shi, kuma ɗaga muryar da yayi saboda ya ankarar da ita ne sai kuwa ya ankarar da kan shi.

Mayar da wayan cikin aljihu yayi sannan ya taka a hankali ya koma kan stage ɗin, ya juyo zai ɗaura daga inda ya tsaya amma yanda suka zuba mishi idanun niman karin bayani ya saka shi sakin ƙaramin murmushi, kafin su je su fassara shi da wani abun gwamma yayi bayani "She's my sister Ina tsoron ta faɗi ta karya ƙafa a bar mom da jinya, Sorry Idan na firgita ku"

Sauƙe kai Reina tayi tana kare fuska kafin duban su ya sake dawowa gareta, Abinda ta guda ɗin dai, hala gobe kam sai dai ta ganta a ATBU Amebo.

Ta ranƙwafa kunnen Safina "Feenah don Allah mu tafi"

"Mu tafi ina? Sai da na zauna zan fara kwankwaɗan madarar ilimi? Idan zaki iya tafiya ke kaɗai tohm"

Sai ta koma ta kifa kanta a kan desk, ita da ta san shine da ba zata zo ba, hala shiyasa yaƙi faɗa mata event ɗin na makarantar su ne koda ya haɗa ta da aikin souveniers, kuma ya tura wani mota da drivern da bata sani ba aka je ɗaukowa a gidan Ummi. All for what?.

Daga haka Yaseer ya tamke fuska ya ɗaura da bayanin shi daga inda ya tsaya yana ji a ran shi yanzu kam dole ra'ayin shi ya canza tunda ya buɗe baki ya kira ta da ƴar uwanr shi a bainar jama'a.
.....

Daga farkon da aka fara ƙoƙarin matsan bakin Jamal sai yayi yunkurin kashe kan shi sanin cewa wannan azabtarwan ba komai bane a kan wanda za'a masa idan ya buɗi baki ya furta sunan wani, zasu kama shi ne su yi filla-filla da naman jikin shi su watsa ma karnuka.
Kuma don yana hannun jami'ai ba wai ya tsira bane, har prison za su iya turawa a kashe shi.

Jinya suka yi mishi sosai ba don rayuwan shi yana da amfani ba sai don mutuwar shi asara ce babba, suka tura shi bangaren gyaran hali don sauya yanayin azabtarwan da suke masa.
Sai su ƙulle shi a kujera su saka mishi electric shock, gashi ya fara gwada withdrawal signs tunda bayi samun shan kayan maye a yanzu, ya ƙara tsomarewa ga rawar jiki da tsananin ciwon kai.

daga farko sai ya kwana yana ihu haka babu mai kula shi tunda ba a kanshi farau ba idan yana yi ma yana samun ƴan uwan shi masu taya shi, da ƙarfin Ihun ya ƙare sai ya koma dalalar yawu da fitsari a jikin shi.

Har lokacin basu waiwaye shi ba saida suka tabbatar ya kai maƙura a galabaita sannan suka turo ɗaya daga cikin jami'an da cocaine su kuma suna ganin abinda ke faruwa daga control room.

Tsugunawa jami'in yayi yana kallon Jamal da ya nutsu ya kama kan shi saboda rashin ƙarfi da kuzari yanzu ko damuwa da ƙulle shi basu yi don bayi da ƙarfin yin wani abun, Amma duk yanda ya kaɗa ya rawa bakin Jamal yaƙi buɗuwa, don haka ya ciro Cocaine ɗin aljihun shi ya kawo kan fuskar shi, ai kuwa ya shiga binta da ido kaman wanda aka sakawa mayen ƙarfe, sai da yayi yunkurin faucewa jami'in yayi saurin mayar da hannun shi.

"If you're ready to talk wannan naka ne"

Hannun shi na karkarwa kaman na gajiyayyen tsoho ya haɗe su wuri ɗaya bakin shi da ya bushe ya tsatstsage yana furta kalman roƙo Amma bayi iya fitar da sauti.

Miƙewa jami'in yayi "cewa nayi idan ka shirya magana, idan ba haka ba kuma ka manta kawai"

Jamal yayi hanzarin rarrafawa ya riƙo kafar shi. "Zan faɗa, idan ka bani zan faɗa"

Ya sake tsugunawa a gaban shi "ta yaya zan yarda da kai? Talk first"

Ya sani daman tun da suka kawo shi nan rayuwar shi ta ƙare don ko bai faɗa ba ace ya samu ya kuɓuta ba za su bar shi da rai ba.

A hankali ya shiga zayyano musu sunayen wa'inda suke aiki tare a Nigeria, Ghana da Italy....

Tun a secondary ya fara taɓa ƙwaya da sauran su a wurin abokai har aka zo kan giya, amma ko da Alhaji Salisu ya gane bai ɗauki wani mataki ba koda na canza mishi makaranta ne kuwa, Saboda Hajiya Hauwa tayi kuka ta kare shi.

Bayan faruwar case ɗin Reina suka tura shi Ghana daga nan bai san ma yaya aka ƙare ba.

Kaman abun arziƙi ya ɗan fara karatun saboda tsoro ya shige shi daga farko amma da ya haɗu da waɗanda suka dama shi suka shanye a barikanci sai shima ya hau layi kawai, hidiman shaye-shaye, party, ƴammata babu wanda bayi ciki.

Ba'a ɗau lokaci ba kuɗin da ake turo masa daga gida ya fara kasawa facakan shi don haka ya fara niman hanyan samun kuɗi, ido a rufe ya faɗa cikin kasuwancin ƙwaya. Kuma Ubangiji yayi mishi talala ya daɗe yana samu a ciki yana daɗa bunƙasa amma dake kuɗin babu albarka kullum a tambaɗewa yake ƙarewa.
Chapter 55 · 0% Book details