Sashe 89
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana jikin shi ya yunƙura har sai da hannun shi ya isa ya samu ya ɗauka, sai kuma tunanin wanda zai kira ya samu agajin gaggawa ya shiga kan shi. Umma fama take yi da jinyar Aicha ba zai sake ɗaga mata hankali ba, tukunna ma da sanin shi ya gina gidan shi can nesa da gidan su saboda kada kannen shi su mayar masa da gida wurin zuwa kullum amma gashi kafin su nemi zuwa gareshi shi ya fara buƙatar su.
Yayi saurin shiga search bar ya rubuta sunan Dr Fahad tunawa da cewa unguwan su ɗaya da gidan Meesha layi ne ba ɗaya ba. Cikin Sa'a wayan ta shiga ringing yana ƙirga duk wani second da ta wuce kafin a ɗauki wayar da bugun zuciyar shi.
...
Itama Meesha sai a lokacin suke shirin kwanciya kasancewar sai yau ta dawo daga Kaduna tun kafin bikin Yaseer taje rarrashin general a kan Uncle B, Uncle B ɗin da suke bin ƙafar shi idan suna niman alfarma kowanne iri ne, shiyasa aka yiwa general taron dangi don suna da tabbacin ba ƙaramin fushi yayi ba, shine sai yau ta juyo, kewa ya saka suka raba dare suna huce gajiya da Dr.
Wayan shi da ya shiga ringing lokacin ya shiga banɗaki Meesha ta ɗago daga bedside drawer, tana ɗaga murya ta sanar da shi kafin ta duba mai kiran.
Initials ɗin YK da ta gani ya saka ta tashi zaune da kyau kafin Dr Fahad ya kai ga fitowa kuma ta ɗaga "Yayanmu Lafiya?"
"Ameesha ina doctor?"
Daga muryar shi ta tabbatar ba lafiyan ba. ta gyara zaman hannun rigan barcin ta kana ta yunƙura zata sauƙa daga gadon ta kai ma Dr Fahad banɗakin sai gashi ya fito a lokacin yana tambayar waye.
Bata tsaya saka takalmi ba ta ƙaraso da wayan yanda yake tsaye tana saka mishi a kunnen shi tare da amsawa da "Yaseer ne, YK"
"Hello yallaɓ.."
Katse shi Yaseer yayi ta hanyar fara mishi bayani kai tsaye tunda bayi da lokacin ɓatawa.
"Bata numfashi?! Ka iya CPR ai" Ya tambaya yana ɗaura shirt a kan singlet ɗin jikin shi sannan ya shiga haɗe botirin shi da hannu ɗaya. Itama Meesha ganin haka da gaggawa ta shiga niman kayan da zata saka ta bishi.
Amsar da yayi tsammani shi Yaseer ya bashi yace "kayi ƙoƙarin resusicating ɗinta, gani nan zuwa yanzu, kada ka kashe wayan"
Shima ba niyyar kashewa yake da shi ba daman, don haka ya saki wayan daga kunnen shi ya faɗi a kan gadon sannan ya kwantar da Reina a sannu ya shiga danna ƙirjin ta da tafukan hannun shi biyu iya yanda ƙarfin ƙashinta zai iya ɗauka, sai ya dakata ya kama hancinta ya haɗe bakin su wuri guda ya hura mata numfashi kana ya cigaba da dannawa.
A haɗe bakin su na biyu yana hura mata Iska ya samu tari ya ƙwace mata, ya zare bakin shi daga nata tare da sake mata hanci ta samu ta ja numfashi mai ƙarfi.
Yayi saurin ɗaga ta zaune ya jingina ta da jikin shi ya kwantar da kanta a kafaɗar shi yana shafa bayan ta a hankali tare da nanata godiya ma Ubangiji da bai bari ya gama zarewa ba.
Saida ya shashshafa ƙasan lallausan duvet ɗin da rufa mata jin yanda jikinta yayi sanyi ya sake kafin ya samo wayan shi ya mayar kunne yana sanar ma Dr Fahad ta farfaɗo ya hanzarta kana ya katse kiran.
Barci har ya fara ɗaukan ta a yanda suke zaunen, hankalin shi bai tashi bane a yanzu saboda tashi da sauƙan kirjin ta da yake ji a nashi sai kuma ɗumin numfashinta dake dukan wuyan shi. Amma kuma tunanin yanda Dr Fahad zai samu duba ta idan ya iso yake yi bacin tana cikin wannan yanayin.
Ya shafa kanta da parking ɗin ya wargage ribbon ma ya kama gaban shi a hankali ya shiga kiran ta "Umry...Ya rawhati(my comfort/my rest)..."
Numfashin da ta sake ja da ƙarfi ya sanar da shi ta farka.
"Ki min alfarma mu shirya ga doctor nan zai ƙaraso duba ki"
Kaman bata ji mai ya faɗa ba sai kawai ya yunƙura ya sake kwantar da ita kanta a saman pillow ya lulluɓata sannan ya shiga ya haɗa mata ruwan wanka.
Can ya dawo daure da towel a ƙugu jikin shi na ɗigan ruwa ya karaso gadon ya yaye duvet ɗin ya cicciɓeta, sannan ya ɗauki wayan shi ma kada doctor ya kira basu gama ba.
"Y..yaya Yaseer"
"Na'am Umry" ya amsa cike da tausayi da kulawa.
"Ƙirji na" tace cikin muryar kuka.
Daman ya san dannan sai yayi mata ciwo ya amsa da "sorry na kusa rasa ki ne Umry"
Ɗan sauti ta sake fitarwa dake bayyana irin ciwon da take ji, ya sake binta da kalmar haƙuri yana yaba ƙoƙarin ta kafin yayi ƙoƙarin ajiye ta cikin bathtub da ya tara ruwa mai zafin da zata iya shiga ciki.
Nan ta saki ihun da ya saka shi kokwanton da ba su ƙadai bane a cikin gidan tabbas sai an jiyo ta, zafin ruwan ne yayi mata yawa ba wani abu ba, dole ya kunna famfon ruwan sanyi ya zauna riƙe da ita hannun shi a cikin ruwan yana jin temperature ɗin shi lokacin da wayan shi ya shiga ringing a cikin sink.
Ya kashe famfon kafin ya miƙe da ita ya ɗauki wayan a take sanin mai kiran, Dr Fahad ya sanar da shi gashi a gate da Madam ɗin shi suka zo.
Sai a lokacin ya kira security yace a barsu su shigo sannan ya ajiye ta da kyar ya fita zuwa closet ɗin shi ya saka baƙar jallabiya mai dogon wando kana ya fita buɗe musu main door na gidan su shigo.
Dr Fahad ya shigo da akwatin aikin shi Meesha tana biye da shi sanye da zumbelelen hijabi har ƙasa.
Parlorn shi na sama ya wuce da su yace bari ya shiga ya fito da Ita.
Yana shiga ciki ya yaye bedsheet ɗin dake shimfiɗe ya daɗa baza duvet ya wadaci gadon kana ya wuce da shi banɗakin ya jefa a cikin washing machine ya koma gareta.
ƙoƙarin su hanzarta kada su bar su suyi ta jira yake yi ya samu ya suturta ta, ta koma ta kwanta ya dauko wani duvet ɗin ya rufa mata.
"Bari doctor ɗin ya shigo toh, mijin Ameesha ne, suna tare ma"
Ya miƙe zai fita tayi saurin riƙe hannun shi tana girgiza kai.
"Ameeshan ne baki son ta shigo? Then zai shigo shi kaɗai"
Ta sake girgiza kai.
Sai ya koma ya sake zama.
"Menene Umry, talk to me please "
Bakin da yayi mata nauyi ta buɗe a hankali tace "Babu komai, na warke, su tafi kawai zan sha magani na" ita yanzu saboda wannan dalilin shine har sai taga likita, ta kai kunyar sa ina toh? Gwamma ma Ameeshan macece ƴar uwarta.
"Matsalar numfashin ki zai duba ba wannan ba" ya faɗa Kaman ya karanci zuciyar ta.
Fafur ta ƙi tunda dai duk ɗaya suna da alaƙa da juna. Ƙarshe haka ya fita ya sanar da su, ya same su suna zaune jingum-jingum.
Bai gama bayani ba Meesha ta miƙe ta nufi ɗakin ta turo ƙofa, sai shima Yaseer ya bata daman ta shiga ɗin ko zata iya convincing ɗinta.
Suna zaune yana sake bayani ma Dr Fahad a kan issue dinta amma bai faɗa mishi sanadin Trauma ɗinta ba, ba za'a taɓa jin labarin wannan babi na rayuwar Reina daga bakin shi ba. Kiran Meesha ne ya shigo wayan mijinta ya ɗauka sannan yace Yaseer ya shiga ciki bayan tayi magana ya katse kiran.
Tura ƙofan yayi idanun shi suka fara sauƙa a kan Meesha dake zaune a kujeran dake kallon gadon fuska a tamke take kallon Reina don ta bata haushi.
Su gashi an ɗago su da talatainin dare har jaririnta sai bari tayi a wurin dattijuwar mai aikin ta amma Reina ta zauna tana ɓata musu lokaci.
"Ka gwada mata magana nima na gaji, don tace tana jin ciwo amma ta faɗa min a ina da ina tana tunanin allan misru ce ni, ko kina so ayi miki jinyar cuta ɗaya ne a bar ki da sauran?" Ta ƙare da karamin tsaki.
Yaseer ya ƙarasa gadon sannan ya zauna ya janyo ta jikin shi kana ya shiga tambayar ta cikin lallami. Meesha tana zaune tana kallon su, tana kallon Yaseer Kamal Jama'are, Yaseer ɗinta na ATBU da wata macen a ƙirjin shi. Sai ta saki murmushi tana jinjina lamari na ƙaddara kasancewar Reina ce wannan macen, wanda a shekarun da suka wuce ta samu masaniya a kan halin rayuwa da ya canza ma Yaseer Allah yayi ikon shi a kan shi ya ɗaga shi zuwa matakin da ya so, koda ace zata ƙare ƙirgen duka matan duniya da zasu iya kasancewa da shi ba zata saka da Reina ba amma ƙaddara itan ya zaɓa.
Mamaitawa Meesha abinda tace yayi tunda shi ba kunyar ta yake ji ba, bama ta kunya yake yi ba tukun sai ya gama da ta lafiyar ta.
Ta daɗa ɓoye fuskanta a jikin shi ƙwallan idanun ta na jiƙa rigan shi.
Meesha ta taɓe baki tunda ai shi yaga zai iya. "Bari ya shigo ko allura yayi miki"
Wannan karon ma atafur taƙi, sai bada pain reliever Dr Fahad yayi a bata ta sha tunda bai san abinda zai yi mata daga nan ba, Amma yace gobe sai sun je asibiti an dubata musamman ma ƙirjin da take kokawa don ana iya samun gocewan ƙashi ko mamakancin shi yayin CPR idan ƙarfin da aka saka yayi ma mutum yawa.
Pain reliever ɗin Yaseer ya bata ta sha, ya shiga tambayan ko akwai abinda take son ci tayi ta girgiza kai A'a.
ya samu ta koma barci daga ƙarshe yana ƙudurtawa a ran shi daga gobe zai fara fafutukar niman lafiyan ta har zuwa iya lokacin da za'a ɗauka ko kuma nisan wurin da za'a je kafin ta warke.
Komai zai wuce kaman bai taɓa faruwa ba.
.....
"... Nayi tunanin Idan zaka iya yiwa kowa haka banda darling, ko ka manta marainiya ce? Ka daina tausayin ta ne Daddy?"