← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 117

Sashe 18

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safiyar ranar talata ce, kuma tana gama abin karyawan Alhaji Salisu ta fita ta ɗauki Safina suka wuce kasuwa, shima a can basu ɓata lokaci ba don shago ɗaya suka tsaya suka dawo, don haka har zata gama gasa cake ɗin lokacin ɗaura abincin rana bai yi ba.

Oven ɗin Hajiya Hauwa ta fara kunnawa don tayi preheating ɗin shi, ta ciro butter da sugar ta haɗa ta saka hand mixer ta shiga juya shi har saida ya sake, domin Hajiya Hauwa tayi mata iyaka da electric mixer ɗinta.
kana ta shiga fasa crate ɗin ƙoyin ta a wani rubber daban, ta tsiyaye wanda suka fashe ta cire bawon da ya shiga shima ta saka mixer ta kaɗa shi sannan ta juye a kan butter da sugar ɗin ta zuba vanilla flavour ta shiga juya shi saida ya haɗu da kyau ta fara tankaɗe flour a kai, ta zuba baking powder a kan flour ɗin kana ta jujjuya ta zuba resins.

Lokacin har cikin oven yayi zafi don haka ta ɗauko baking tray na cupcakes mai ɗaukan guda sha biyu da saka ƴan paper cups ɗin a ciki ta shiga saka batter ɗin da cokali har ta gama ta saka a ciki ta nemi wurin zama zuwa lokacin da zai gasu. Ta ciro wayar ta wanda Baba ya siya mata tayi sa'ar manta shi a jakar Safina ranar graduation tana karatun pdf, shima karancin kuɗin shi ya saka Hajiya Hauwa bata ƙwace ba amma babu kalan mugayen kalaman da bata faɗa mata a kai ba, harda wai su Ummi ne suke bata goyon bayan ta lalace, ita dai taji ta rabu da ita.

Ƙamshin cake ɗin da ya fara buɗe gidan lokacin da ya fara gasuwa ya saka Hajiya Hauwa shigowa kitchen ɗin taga mai yake faruwa.

"Mai kike gasawa?" Ta tambaya da tunanin snacks ɗin gida ne take yi.

Zoben mahaifiyar ta dake hannunta ta murza "Da.. daman ordern cake ne aka bani a.. a school, amma wallahi komai da komai siyowa nayi a kasuwa har sugar ma"

Hajiya Hauwa ta kintime fuska. "Toh shi oven ɗin uban ki ne ko uwar ki suka siya min?"

"Kiyi haƙuri don Allah"

Wucewa tayi ta kashe socket ɗin oven ɗin sannan ta ɗauki roban da sauran kwaɓin cake ɗin yake ciki ta buɗe ƙofar baya Reina na riƙo ta tana roƙon ta tayi wulli dashi ya faɗi har saida roban ya fashe, sannan Ta juya ta bar mata kitchen ɗin. Haka Reina ta koma ta tsuguna tana tattara wanda bai taɓa ƙasa ba, kusan duka ya malale a kan interlocks ɗin wurin.

Kuka ne yazo mata, yanzu a ina zata samu ta biya matar nan kuɗin ta? Gashi a gobe suke so zasu yi amfani da shi kuma tun kwana biyu da suka wuce ta karɓi kudin.

Barin kwashewan tayi kawai jin ƙaran doorbell har sau uku babu wanda ya buɗe, ta miƙe hawaye na mata zuba ta ɗauraye hannunta, ta share hawayenta kafin ta tafi buɗe ƙofar.

Kallon juna suka tsaya yi na tsawon daƙiƙa biyar, kafin hawayen da take riƙewa ya shiga bin kuncin ta.

"Uncle Bilal?!"

~~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

54

~~~~~~~~~
_Don't hate you_
_But we can't save you_
~~~~~~~~~~

"Reina, kece wannan?"

A maimakon amsa sai ta kece masa da kuka. Ya tsaya yana kallon yanda ta jingina da jikin ƙofa tana sheshsheƙa, sai ya rasa yaya zai yi mata, yanzu ba da bane da za'a ce yana da daman rungume ta ko ɗaukan ta. Reinan dake tsaye a gaban shi daban take da wancan, bambanci sosai.

Ƙarasawa yayi ya riƙe hannun ta zuwa ciki, ta bishi bata fasa kukan ba, ko da ta zauna sai ta haɗa kai da guiwa.

Sai ya sauƙa a kan guiwowin shi ya ɗago kanta ta dube shi.
"Duk wannan kukan na kewa na ne?" Yace yana murmushi.

Ita karan kanta bata fayyace ainihin dalilin kukanta ba, na asarar da Hajiya Hauwa tayi mata ko kuma na kewar shin ne da gaske?, amma sai take ji kaman duk abinda take fuskanta na tsawon shekarun ne take jin zafin su a yanzu da take gaban wanda zata kawo ƙara ya share mata hawaye.

"Uncle B kaga Umman Zahra ko?..." Ta shiga nanata mishi abinda ya faru ɗazun da wanda tayi mata jiya da na shekaran jiya har da wanda tayi mata watannin baya duk wanda yazo kanta sai ta sanar dashi kukan ta na ƙara tsanani.

"Ya isa! Na ji, ya isa." Ya dakatar da ita ganin tana niman ficewa a cikin hayyacin ta. Ya miƙe tsaye ya riƙo hannunta suka fita daga gidan, Hajiya Hauwa sai fitowa tayi taga tashin motar su.

Sun yi tafiya mai ɗan nisa cikin shiru tana maida ajiyan zuciya kafin ya tsayar da motar a gaban wani restaurant ya cire mata magani ya bata ya buɗe mata robar ruwa.

Siyayyan magunguna yayi mata na musamman, daman yana aiko mata wasu a kai a kai amma tara su take yi bata sha don ba son magani take yi ba.

Sai da ta fara tara ruwan a bakinta ta jefa maganin ta yi saurin haɗiyewa kana ta sake kurɓan ruwan tana yamutsa fuska.

Ya karɓi ruwan yana tambayar ta "zaki ci abinci?" Ta girgiza kai. "Nama fa?" Shima ta girgiza kai"

"Toh ni ina jin yunwa kinga baki bar ni na zauna ba ma"

Ta juyo tana duban shi, ya tsare ta da idanu. Buɗe baki tayi zata yi magana bata bar ajiyan zuciya ba ta samu tace "to..h muje in ddafa maka"

Ya waro ido "ke zaki dafa min abinci Reina?"

Ta gyaɗa kai irin yess.

Yayi murmushi "yanzu shekarun ki nawa?"

"Shsha takwas"

"Ahh lallai, amma yanzu bari muyi takeaway kawai, ko kina son muci a wurin?"

Ta gyaɗa kai don tana son zuwa irin wurin cin abincin ƴan gayun nan amma sai dai ta rako Zaheera, da abokan Zaheeran maza suka fara kulata sai ta daina zuwa da ita.

Ya fita ya zago ya buɗe mata ƙofa ya riƙo hannunta ta fito. Suka jera a tare zuwa ciki. Lokacin da motar da ya biyo su a baya ya tashi ya bar haraban restaurant ɗin.

Shi yayi musu ordern abinda zasu ci aka tafi kawo musu kafin ya dube ta, zuwa yanzu numfashin ta ya daidaita.

"Ban yi tunanin zaki iya gane ni ba." Ta ɗago daga kan menu da take karantawa ta dube shi. "Ko dayake ke kika canza ba niba Reina"

Sai ta ɗan shagwaɓe fuska "bayan kaima ka manta dani Uncle Bilal kaman Daddyn Niger, kayi min alƙawarin zaka kai ni wurin yaya Yaseer daga nan ban sake ganin ka ba"

Ya ɗan sosa ƙeya "kiyi haƙuri, wannan karon kam nayi alƙawarin sai na kai ki wurin shi kafin in koma"

"Hmm, idan ka tafi hala sai na tsufa nima kafin ka sake dawowa"

"No, yaro na yana Nigeria yanzu ba zan yi nisa da gida ba."

"Kana da yaro dama?" Ta tambaya annurin fuskar ta na dawowa.

"Eh mana, yara na har biyu. Bari ki gan su" ya ciro wayar shi ya nuna mata hoton Mufid da ƙanwar shi. "Babban yana nan wurin Mummy M ita kuma macen tana wurin mahaifiyar ta a Egypt."

"Ka gansu kyawawa Uncle Bilal?!"
Ta karɓi wayan tana ƙare musu kallo kaman yaran larabawa "yaushe zaka tafi to?" Gwamma ta sani ta san kalan uzurawar da zata yi mishi ya kaita ta ga Yaseer.

"Akwai abinda nazo nima ne, idan ya samu daga yanzu zuwa sati uku zan iya tafiya na shekara biyu, idan kuma bai samu ba na dawo nan kenan zaki dinga gani na kullum"

"Toh yaron ka fa? Egypt ɗin zaka maida shi wurin matar ka?"

Riƙe haba yayi "Har yanzu kina nan da tambaya Reina?"

Ta saka tafukan hannunta ta kare fuskar ta a kunyace.

Zara-zaran yatsun ta yabi da kallo, zuwa zoben azurfan dake yatsar ta na dama.
"No, bamu tare a yanzu. Sabuwar mummy zan nima mishi, ko kina son shi in baki?"

Sai ta sauƙe hannun daga fuskar ta suka yi ido huɗu kuwa, kallon rashin fahimta take mishi shi kuwa na tabbacin shawarar da ya yanke a yanzu yake binta dashi. "Idan zaki aure ni sai in baki yaro na kyauta"

Sai taji kaman ta tashi salum alum ta taka a hankali har waje kafin ta ɗiba da gudun da ba zata tsaya ba sai ta isa ɗaki ta rufe kanta.

Isowar abinci yasa Uncle B dake jin yunwa da gaske ya fara ci, Reina kam cakalar shi kawai take.

"Ko shine dalilin da idan dan zo ganin ki kike guduwa? Saboda kada ince ina son ki?" Ya tambaya hankalin shi na kan abinda yake ci.

Ajiye fork ɗin hannunta tayi tace "ni kuma? Ni da na kasa gajiya da ƙirgen kwanakin da zaka zo ka kaini wurin yaya Yaseer? Har numbern wayan ka na kira a wayan Umman Zahra baka ɗauka ba".

Ɗagowa yayi ya dube ta. Tun lokacin da ta bashi labarin abinda Jamal yayi mata ya fita harƙan Hajiya Hauwa, amma hakan bai sa ya tsame hannun shi a cikin lamarin Reina ba, yana mata siyayya yana mata aika kuma duk lokacin da zai saka ƙafar shi a Nigeria sai ya zo duba ta.

"Na zo wurin ki sau biyu wai baki nan. Na biyu kan ma har gidan grannys ɗinki naje aka ce wai kin tafi Abuja"

Ta tuna lokacin, zuwanta Abuja na farko da wayon ta kenan, bikin gidan Hajiya Zuwairah da ita uwar gayyar ma bata so zuwan ta ba Hajiya Hauwa ta tursasa ta saida taje ashe ta san cewa Uncle B na hanya ne.

"Hmm" kawai Reina ta amsa.

"Lokacin da kika gama school har baki zaɓin idan kina da ra'ayin karatu a wani kasar a kawo ki Canada wuri na nayi, zaki zo da wani ɗan uwa wanda zai kula dake, ko su biyu ne ma ba matsala zan ɗauki nauyin ku duka amma wai sai kika ce a faɗa min baki so"

"Ni ɗin?" Ta gwada kanta da yatsa, ita da biyan kuɗin makarantar ma tana tunanin sadaƙatul jariya ta samu?.
Chapter 18 · 0% Book details