← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 117

Sashe 111

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Ni ba raina masa hankali nake ba hajjaju tunda ya san idanu na basu kan abin hannun shi kuma ko ya bani sai wanda ya zamo dole irin su kati da data da bani da daman mayar mishi nake karɓa' ta turo.
Reina taga tana kan typing alamun da saura sannan ta fara karantawa.

Kafin ta gama Safina ta sake turo da. 'kuma ba na faɗa mishi bane don yayi min wani abu, jagwal ɗin kaina ne yayi yawa ina gudun ƙarawa da wani yasa na bashi fake date ayi a wuce wurin'

'hmm. Toh gashi nan dai ya turo mun wasu designer perfumes da bags ki zaɓa birthday girl. Kika ƙi zaɓa kuma zan zaɓa miki in ce ra'ayin ki ne' ta tura sannan ta sake rubuta. 'kuma kin bashi fake date shi kaɗai ne saboda kada yayi clashing da sauran samarukan ki hankalin shi ya tashi ko kuma shi ya ɗaga musu hankali?'

Safina ta turo reply ma na farko da 'zaki saka bawan Allah yayi asaran kuɗin sa ne, domin kin sani ba iya nunawa zan yi a gida ba balle in yi amfani da su. Kuma ke kika jawo min Tunda kika yi aure Daddy ya saka min ido yace idan yaga ina tara samari ce musu zai yi su fito nima yayi mun auren'

ta zabi na biyu shima tayi replying da 'ba haka bane, kawai tausayi ya fara bani shiyasa bani son in yi breaking heart ɗin shi, sannan babu laifi a ɗan kwai maturity a hidiman shi, yana baiwa hidima na muhimmanci'

'Kin dai fara son shi kawai!' ta tura mata. A bayyane kuma tace "bae kaman yaya Suhail fa ya samu karɓuwa" don ta kasa riƙewa har sai anjima ta shafa mishi.

Yaseer ya amsa da "wannan nacin shin ai dole" yana duban yanda take murmushi, ta juyo tana fuskantar cikin shi tare da gyara kwanciya, shi kuma ya mayar da hankalin shi kan screen.

'idan nace miki ba haka ba ma ba yarda zaki yi ba' cewar Safina.

Sai Reina ta kawo speakern wayan bakinta tayi mata recording voice note. "Saboda kin san hakan ne ai. Amma zuwa yanzu shi da yaya Muhammad sun san suna takara da juna ko?"

Ganin ta ɗau lokaci bata yi replying ba ta fita daga kan chat ɗinta ganin Suhail ya sake turo wasu hotuna guda shida ta shiga tayi forwarding ma Safina hotunan, sai ga reply ɗin tambayar da tayi mata a sama. Kalma ɗaya 'Oho'.

'Allah ya kyauta lamarin ki' tace ta sake fita tana sauƙa chats ɗin ƙasa sai ta tsaya a kan na Maama dake da saƙonni biyu da bata karanta ba tana kallon Dp ɗinta. Hoton ta ne a kan dp ɗin Maama ita da saidai ta saka hoton kalaman hikima ko ayar Alqur'ani ko kuma ta barshi hakanan, status ma sai tafi wata bata ɗaura ba kuma tana online ɗin sai kayi mata magana ka gani ta amsa.

Hawa kan chat ɗin tayi taga yanda tayi reaction ɗin zuciya a jikin duk hotunan da ta tura mata.
sai kuma sabbin saƙonnin da na farko sallama ne, na biyu kuma yana cewa, 'Aunty Reina ina wuni, Yaya yaya Yaseer?
Ki gaida min shi Please.
And yaushe zaku dawo? Ina son in zo gidan ki'

'kizo kiyi min mene Maama' ta rubuta mata a matsayin amsa kaman yanda take yawan faɗa idan aka so haɗa su a wani abu, amma sai tabi ta goge tunda ta sani kewarta tayi ba zata iya faɗa bane kawai, amma tafi son taji daga bakinta don haka ta sake rubuta sakk saƙon da ta gogen ta tura mata.
Kaman jira Maaman take yi ta fara typing. 'na zo inga fuskar ki, missing ɗin ki nake yi big Aunty'

Sai ta tura mata emoji masu heart a ido guda uku. 'Nima haka sissy. Me kike so in kawo miki?'

Ɗan hiran da suka taɓa a ranan Reina ta gwada ma Yaseer ya fi sau biyu, kuma raba dare suka yi tana masa hiran Maama da yarintan su. 'Na ma yi missing wasu hotunan graduation ɗina ne amma da kaga yanda ta turɓuna fuska kaman wacce aka yiwa albishirin mutuwa, amma na san ba za'a rasa mai shi ba a cikin wanda suka je, zan tambaya in nuna maka'

Wayan shi dake caji yace ta ciro. Ta miƙe ta ɗauko ta bashi ya karɓa ta sannan ta koma position ɗin da take zaune tun farko ta sake kwantar da kanta a damtsen hannun shi, tana kallo ya shiga private folder ya saka password sai ga hotunan ta rututu, ya fara scrolling ƙasa tana kallon harda wa'inda bata san da su ba da wanda tayi tunanin ta rasa su har abada domin an daɗe sosai da ɗauka.

Ya kai kan hoton da take Magana a kai "wannan ne ko?" Ya tambaye ta yana ɗagowa ya dubeta, itama shi take kallo, cikin yanayin da ya zarce mamaki. Sai ya sakar mata da murmushi yana shafa sajen shi ya san sai ta tuna ranan da ta tuhume shi a kan bayi da hoton ta ko ɗaya a wayan shi.
"Zan iya tura miki idan kina so. Amma shi kawai" yace yana lakatan hancin ta. Bakinta dai ya gagara motsi.

.....

*Bauchi, Nigeria*

Hajiya hauwa ce kwance magashiyyan a ɗakin asibiti, hawan jininta ne yayi mummunan tashi bayan faɗuwan da tayi, typhoid da ulcer ma yace salamu alaikum ga ciwon zuciya dake mata warning daga nesa.

Ɗakin yayyame yake da ƴan uwan mijinta wanda suka ɗebo ƙafa da niyyan dubiya amma babban dalilin shine su tsegunta raɗe-raɗin da suka ji a kan Zahra su tabbatar abinda aka ce ya samu Hajiya Hauwan gaskiya ne shiyasa suka shirya suka zo a lokaci guda dukkan su, aka mayar da ɗakin asibiti kaman gidan suna amma ita nata ƴan uwan babu ko ɗaya har maman Meesha Uncle B ya hana su zuwa, general kuma daman ya tsame ta daga cikin yaran shi tun farkon case ɗin Jamal.

"Ki gwada kiran ta ke, sai mu gani idan da gangan taƙi ɗaukan nawa kiran fitsararriyar yarinya" Hajiya Zuwairah ke faɗawa Hajiya Jummai, domin sun gama da babin Hajiya Hauwa sun aibanta sakacin ta a kan yaranta da kuma bata shawaran yanda ya kamata ace tayi tarbiyyan su tun farko da yanzu basu ɓaci mata ba. Bayan dukkan su da guntun kashi a ɗuwawun su amma dake kasuwar ta ne ke ci a lokacin haka ta barsu suka gama cinikinta bata tanka ba. Shine da suka gaji kuma suka koma chaptan Reina tunda wanda suka bi ta ƙafanta ta nima ma yaran su aiki ta faɗa musu wanda ta nima ta wurin shi yace YK ne ke da alhakin ɗaukan su, kuma Yaseer ɗan kamalun jama'are da suka sani a yanzu da ya ƙaro wulaƙanci da matuƙar wuya ya amince da su, kuma wasu a cikin su ma suna da aikin aka saka suka yi resigning tunda ga dama mai kyau ta samu. Ba zasu yarda suyi two zero ba shiyasa suka fara bi ta wurin ƴar su da suke da iko da ita.

"Bar shegiya jinin talakawa, da yanzu ba Haydar ɗin bane zai rufa mata asiri? Don yana da wa'inda suka fita har biyu ya ƙita gashi gidan shi ya fara cika da zuri'a shine zata gwada mugunta da ƙyashi ma ɗan uwanta! Wa ya sani ma Yaseer ɗin ko dukiyar jini ne kokuma na tsafi? Itama idan ba tsayawa muka yi a kanta ba kwanan nan zamu ji babu ita yayi tsafin da ita ya sake auro wata"

Ƙaramin tsaki Hajiya Lubabatu tayi murya babu armashi tace "da kin bar surutun ne kika kira mana ita, sai mu gani idan nima rainin zata yi mun"

Haka suka gama kira Reina taƙi ɗauka don tana da yaƙinin Hajiya Zuwairah ne ta canza number take kiran ta.
Aka kira ta da numbern Hajiya Farida ma a cewar ta sun taɓa gaisawa a WhatsApp sau ɗaya da ta tura mata hotunan graduation ɗin Maama da ta ɗauke su a wayanta tare da Junior ta amsa sallaman ta kuma tayi mata godiya, shima tana kallo ta ƙi ɗauka tama saka wayan a silent. ba zata yi blocking ɗin su ba amma basu kai su saka ta saɓa umarnin mijinta ba.
.
.
A sannu kuma tafiyar lokaci ta fara hanzari, abubuwa a lokacin da suka faru sai ka ga kaman ba zasu wuce ba amma kafin ka ƙyafta idanu sai kaga har lokaci ya wuce. Reina sun
Ƙarasa hutun su a Iceland sannan suka wuce ƙasa mai tsarki suka yi Umrah. Satin su biyu a can jirgin su ta lula Niger saboda bikin Aicha da angon ta Rafeeq wanda za'a cika ma irin su Reina burin su na shagali, dukda tana jin yanda tafiyar sun ya gajiyar da ita har a gaɓoɓinta.

Shiri ake yi gagarumi a duka ɓangarorin biyu, ga dangin ango kaman zasu ɗauko Nigeria su zo da ita tsabar yawa. Mata da maza yara da manya kowa yaci buri ma wannan biki.

"My daughter" mahaifiyar Rafeeq ta sake kira tana taba Aicha, tare da ƙarewa fuskarta dake sheƙi kallo, tana so ta saka ma ranta dilka ne ya amshi jikinta sosai.

Buɗe ido Aicha tayi ta zuba mata su, ganin ita ce ta miƙe zaune da ɗan saurin ta Amma yawun da ya cika mata baki ya hana ta magana don haka ta miƙe tayi hanyar banɗaki ta ɗaurayo bakinta ta dawo.

"Mummy ina wuni" Aicha ta gaida ta kanta a duƙe, sai ta riƙo hannunta ta zaunar tana ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa, kana ta amsa da "Lafiya ƙalau, zazzaɓin ne?"

Dariyan yaƙe Aicha tayi tayi saurin cewa "ai naji sauƙi, ina ɗan hutawa ne kawai"

"Allah ya ƙara sauƙi, Amma barcin ya ɗan yi yawa kinga an daɗe da yin la'asar har maghriba tana niman kunno kai, kiyi Sallah ga abinci na shigo miki da shi"

"Toh na gode Mummy"
Chapter 111 · 0% Book details