← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 117

Sashe 10

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'A wannan rana Allah ya azurtani da HAFSATU REINA. Ni Fauzee wai yanzu nice na zama uwa?! Na sha azaba kam but I can't believe it, na gagara gaskata cewa nice nake riƙe da ƴata da na haifa da kaina. Ƴata da mutumin da ban taɓa tunanin kasancewa dashi ba, wanda shekaru 3 baya, bayi cikin duniyata kwata-kwata, yau na riƙe Hafsatu ƴar Tahir wanda Fauzah ta haifa mishi, ya bata sabon suna ya bata sabon rayuwa ya bata sabon Identity, Amma abinda yafi komai kasancewa baƙo a cikin rayuwar Fauziyya shine canzuwar mafarkayya da burikanta. A yanzu Hafsatu Tahir Kamal itace duniyata, babu abinda ba zan iya aikatawa saboda ita ba, babu gwagwarmayar da ba zanyi saboda rayuwarta ya inganta ba, zan bawa Hafsatu Reina kyakkyawar rayuwar da babu uwar da ta taɓa bawa ƴarta irin shi. Kaman haka nake ƙaunar ta da dukkan zuciyata.'

"Gashi"

Kuɗin da Zaheera ta miƙo mata ta fara kalla, dala ɗari ne guda biyu, bayan mahaifiyarta ta ƙwace wanda aka bata wurin guda Ashirin. Ta tafi zuwa kan fuskarta dake ɗauke da murmushi, murmushin da ta daina gani a kwanaki kuma ta rasa a wani dalili, domin tunaninta bai taɓa kawo mata a kan wani yaron da idan ba saka shi tayi a idonta ba ma bata tunawa da existence ɗin shi.

"Bani so, Nagode" da gaske ne ita da take kulle a cikin gida mai zata yi da kuɗi?.

"In siya miki chocolate da shi toh idan mun fita?"

Bata taɓa tunanin akwai ranar da za'a yi mata tayin chocolate taƙi ba musamman a yanzu da bata da damar samun shi cikin sauƙi. Amma sai ta samu kanta da girgiza kai, "bani so na gode"
Ta ajiye littafin ta miƙe ta sauƙa daga gadon ta shiga banɗaki ta rufo ƙofa, idanun Zaheera sukayi mata rakiya.

Ɗaukan diaryn tayi a hannunta, ta gane shine littafin da ta hana ta da ta gwada tana so. Ji take yi kaman taje ta ƙona duka su rasa amma ba yanzu ba.

Lallai tayi wauta da ta daɗe tana fushi da Reina, ba wai wulaƙancin da ake mata a gidan yana mata daɗi bane, ta ɗauke ido daga taimakon ta ne saboda ta gane matsayinta, ita ba kowan kowa bane a yanzu. Kuma matuƙar zasu cigaba da rayuwa a wannan mataki to ta yarda zata cigaba da binta, don haka ta ajiye mata kuɗin a kan littafin sannan ta ɗibo wasu chocolate ɗin a cikin jakarta ta zuba mata ta fice a ɗakin, ta san dole idan ta gani ba zata iya haƙuri ba sai taci.

Washegari da sassafe principal ɗin makarantar su Reina ya dawo gidan tare da ƴan sanda. Mai gadi ya shigo ya sanar da Hajiya Hauwa domin ba wannan bane zuwan shi na farko, ta ɗauka barazana ne da yace zai ɗauko mata police idan bata bar Reina ta koma makaranta ba.
Tun sati biyu da rashin zuwanta makaranta babu notice yazo ya gani ko lafiya ne bata dashi domin ya samu excuse ɗin bawa form mistress ɗinsu tunda ba dukanta ake yi ba.

Amma sai Hajiya Hauwa tace wai sun cireta ne a makarantar.
Yace yaya za'ayi a cireta bayan kuɗin makarantar ta da komai yana wurin su har ta gama, har da na islamiyya ma tunda duk nashi ne.

Ta san nawa suke biya ma Zahra da Zaheera duk term, kuɗi ne mai yawan gaske balle a haɗe na shekara da shekaru? Sai ta kawo shawarar ya kawo kashi 70 na cikin kuɗin ya riƙe sauran amma Reina kam canza mata makaranta zata yi.

Wani ɓari na zuciyar shi yaso ya yarje mata da hakan, dukda cewa zai ji zafin cire kuɗin amma bayi da asara, yace zai je yayi tunani har ta bashi numbern wayarta da account numbern da zai saka kuɗin idan ya yanke shawara.
Da ya zurfafa tunani a kan yanda hakan zai iya gurɓata rayuwar Reina sai tsoro ya kama shi, mahaifinta amana ya bayar a hannun shi, a kan son zuciya idan ya cutar da marainiya Allah zai barshi kuwa? Dukiyar da yake ta fafutukar tarawan ma abu mai sauƙi ne ya lalace a sanadin hakkin marainiya guda ɗaya ce, bayan haka Allah ya tsayar da shi da ita da Alhaji Tahir ranar alƙiyama.

Ya kira Hajiya Hauwa ya faɗa mata shi ba zai iya ba ta dawo da Reina makaranta kawai, yayi mata barazanar zai haɗa ta da dangin mahaifiyar yarinya tace idan ya fasa, tunda a tunanin ta ba komai su Ummi zasu iya mata ba, ƴan canjin aljihun su bai kai ya basu wannan ikon ba, kuma ma ai makaranta tace zata canza mata, wanda bai kai wannan tsada ba tunda su zasu dinga biya ba laifi tayi ba.

shine da ya matsa mata tayi blocking ɗinshi kuma ta hana Reina komawa, da ya dawo aka hana shi shiga shine yau ya dawo mata da police.

Sakawa tayi a basu damar shigowa ta shiga ciki ta sake shiga yanda zatayi musu kwarjini idan ta ɗan sallame su da wani abu su share maganar su hakura su tafi.

Fitowa tayi tana taku ɗaya bayan ɗaya idanun ta a kan abinci da kayan motsa bakin da ta saka a jere musu, ko ruwa basu taɓa ba.

Principal ya riga da ya sallame su da kauri tunda daman yayi tsammanin za'ayi hakan.

Duk yanda tayi ta lallaɓe su sun botsare mata, tare da barazanar saka human right a cikin lamarin idan bata bar Reina ta koma makaranta ba.

Haka dole ta amince suka bata takarda ta saka hannu kafin suka bar gidan.
Babu yanda ta iya washegari ta saka Reina ta shirya suka tafi makarantar, ita da taso wannan satin da ita zata dinga tafiya gidan su Meesha tana kama aiki itama.

Labarin dawowarta school ya zaga ko ina har kunnen Maama amma bata damu tazo ta ganta ba. Da bata nan ma idan mutane suka matsa mata da tambayar tana ina sai tace ai ita gidansu ba ɗaya ba yanzu bata sani ba.

Zaheera kuma idan aka tambaye ta sai cewa take yi daman ai Reina bata son zuwa school tun da, yanzun ma haka ne.

Samun kanta tayi a ƙofar ajin su Maama, haka kawai taji tana son saka ƴar uwarta a ido, tana seat ɗinta a gaba tana rubutu Reina ta tsaya a kanta ta kira ta sai tayi kamar babu wani abu mai rai a gabanta ta karkata taci gaba da rubutunta.

"Maama na, bakiyi kewa ta bane? Umman Zahra ne fa ta..."

"Nayi kewar ki ke wa? Ki tashi mun a kai Please kaina ya fara ciwo"

Da ta buɗe baki zata sake magana ma sai ta miƙe da littafinta ta bar mata kujeran ga idanun ƴan ajin ƙurr a kansu.

Haka da sanyin guiwa ta bar class ɗin. A ranar duk yanda take jin tayi kewar abincin makarantar haka ta gagara ci, waffles ɗin da aka yi a dessert menu ne ma ta saka aka yi mata packaging idan taje gida zata ci.

A gidan su Meesha ake ajiye su idan sun dawo, sai dare suke komawa gida., su Zaheera Hajiya Hauwa ta ɗauko musu kayan da zasu sauya amma ita Reina ohonta. Haka zata yi ta galantoyi da uniform har sai lokacin tafiya Islamiyya yayi kafin ta sake kaya shima don ya zamo ma hajiya Hauwa dole ne, har sai ranar friday da sauran yaran ba zasu je school ɗin ba ta ɗauka musu excuse kafin Reina tayi fashin makaranta.

Anyi shagali a bikin Meesha ba kaɗan ba ita dai amarya yaƙe kawai take yi amma bata wani farinciki da auren, dukda cewa doctor Fahad ba aibu yake dashi ba, kuma yana ƙoƙarin bata kulawa tunda yana sonta, a wayar Uncle B yaga hoton ta ya maƙale mishi sai da yayi mishi Iso, kuma Uncle B yana da yaƙinin mutumin kirki ne zata ji daɗin zama dashi.

Daga Wurin ɗairin Aure Uncle B suka shiga gidan da su ango, sai a lokacin ya buƙaci ganin Meesha tun bayan zuwan shi.

Aka buɗe mishi falon mahaifinta ya zauna aka ƙarasa ɗauko mishi ita daga cikin jama'a.

Kanta a ƙasa ta shigo ɗakin tayi sallama cikin muryar da yawan kuka ya dishar da shi.
A tuaninta Daddyn ta ne yake buƙatar ganinta, tana ganin Uncle B ne ta juya zata bar ɗakin mahaifiyarta ta juyo da ita tana masifa ganin abun nata yaki ci yaƙi cinyewa, sannan ta fita ta bar rufo musu ƙofar.

Sai kawai ta tsaya daga bakin ƙofar tana kuka mai tsuma zuciya.

Miƙewa Uncle B yayi ya ƙarasa wurin da take ya rungume ta a jikin shi, sai ta cusa kanta a ƙirjin shi tana ƙara sautin kukanta.

"Ba zan iya ba Uncle B, nauyin damuwata zai rinjaye ni"

"Zaki iya Ameesha, ina da yaƙini a kanki zaki saka mu alfahari".

"Ta ina zan fara? Nayi tunani har ƙwaƙwalwata ta gaza ɗawainiya amma na rasa amsa"

Dagota yayi daga jikin shi ta saka idanunta a cikin nashi. "Ta haƙuri da biyayya. Ni kuma nayi miki alƙawarin ko dutsen dala kike so zan ɗauko miki, kada a samu matsala daga gareki dan Allah, kije da zuciya ɗaya da niyyar zama har abada, kada ki zamo kamar Uncle ɗinki kinji?"

Ɗan murmushi ta saki yana share mata hawaye, "ai na ɗauka zaka zo mana da Mufid"

Ya girgiza kai "No ba daɗewa zanyi ba, yana wurin mummyn shi"

Ta ɗan ware ido. "Ta haƙura ta koma ɗakinta ne?"

Sai yace "toh yaya na iya?"
Da ita kawai yake yarda yayi hiran iyalin shi ko mahaifiyarta ma ba sosai ba, bayi son ana saka mishi ido a rayuwa shiyasa da ya tashi aure ma bai auri ƴar Nigeria ba don yanzu zasu maidata ƴar dangi kaman ma su ya aurota.

"Toh Uncle B...." Kallon da take aika mishi ya isa ya sanar dashi ƙarshen zancen ta.

"Yanzu kuwa" ya ciro wayan shi daga aljihu lokacin da mummy ta buɗe ƙofar ta shigo ta sanar dasu iyaye maza suna buƙatar ganin amarya.

"Please Uncle B" tace cikin sigan roƙo.
Chapter 10 · 0% Book details