← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 117

Sashe 4

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Hauwa ta juya zata bar ɗakin Zahra tayi saurin durowa daga gadon ta bita a baya tana roƙon ta.
"ko 30Gb ki saka min umma dan Allah , datan ne yanzu bayi da albarka"

"Yanzu wanda na saka miki last week ina yaje? Amfani da Internet ɗin ki yayi yawa Zahra, shiyasa baki ƙoƙari a makaranta saboda baki mayar da hankali."

Ƙara matsawa kusa da ita tayi ta maƙale mata hannu "Please Umma, karatu da assignment nake yi dashi fa a online Allah"

Reina da taga har zasu wuce ta basu lura da hallitan ta a parlourn ba ta miƙe "Umman Zahra an gama pancake ɗinne?"

Sai duk suka juyo suka dube ta.
"Bantan uba, Ni sa'ar ki ne da zaki kira sunana gatsau haka?" Bata son ta saki Hajiya Hauwa ne har sai ta amince da buƙatarta amma da ta ƙarasa ta gwaɓe wa Reina baki.

"Ashar ba zai bar bakin ki ba ko?" Hajiya Hauwa ta harare Zahra sai ta saka murmushi kawai, yanda yabi bakin ta a yanzu bata ma sanin tayi ɗin.

"Toh ki saka min Umma dan Allah" ta juya alƙiblar zancen hakan ya saka Hajiya Hauwa sake mantawa da Reina suka juya da ɗiyar ta suka ci gaba da tafiya don haka itama tabi bayan su.

Zahra bata sake Hajiya Hauwa ba saida ta amince da buƙatun ta, tana kunna mota Reina ta ƙarasa mazaunin mai zaman banza ta buɗe kofar ta taka zata shiga motar.

"A'a! Da lafiyar ki kuwa Hafsatu?"

Cike da rashin fahimta Reina ta ɗago ta dubeta kafar ta ɗaya a cikin motar ɗaya na reto a waje.
"Ina waffles ɗin zamu je siyowa?" Daman a rashin shi ta amince da wani abun.

Tsaki Hajiya Hauwa taja a tsawace tace "fitar min a mota da'alla! Bura uban waffles ɗin! Ke Zahra zo ki janye min yarinyar nan ki gani, na lura abin nata harda iskanci a ciki".

Zahra daman jira take yi, da sassarfa ta ƙaraso ta janyo Reina ta watsa ta a ƙasa, Hajiya Hauwa daga ta ciki ta jawo ƙofar da Reina ta buɗe ta rufe shi tayi wa motar ta key, rashin ƙuran dake wurin ya hana bata bule ta dashi ba.

Sai ta fashe da kuka, tana birgima a wurin kaman yanda ta saba, yanda take ɗaga hankalin Alhaji Tahir ya ɗauki tsatstsaurar mataki komin kashin abinda ya faru. Rikicin da yake saka duka mutanen gidan rufuwa a kanta suna bata haƙuri har sai ta daina kuka amma a yau babu wanda yasan ma tana yi, sai Zahra da ta zuzzungure mata kai kafin ta koma ciki ta tattare duk wani abu da zai iya ciyuwa a kitchen da dining ta saka a store ta rufo ƙofar, fridge ma ta rufe shi da key kafin ta shige da keys ɗin ɗakinta ta danna ma ƙofar ta sakata shima, tunda ta san Umman ta ba dawowar yanzu ba.

Kukan Reina bai yi nisa ba saboda yunwar dake kwaƙwular cikin ta kuma babu wanda ya kula ta, don haka da kanta ta share ma kanta hawaye ta koma cikin gidan niman mafita.

Fridge ta fara tunkara ko zata samu wani abun da zata saka a bakin ta emergency ko kayan marmari ne amma taja yaƙi buɗuwa.
Sai ta bar shi ta nufi ƙaramin parlourn Hajiya Hauwa shima fridge ɗin wurin a rufe, dining ma babu komai koda bread. sai ta dawo da nufin duba wani abu a store ko su cookies da juice ɗin da ba'a rabuwa dasu saboda yaran gidan amma store ma a garƙame.

Zuwa yanzu har wani jiri-jiri take ji.

Ta daddafa ta koma dakin su ta samu Zaheera tana kwafan note a wani littafi tana ɗan rera wakan ta na ƴan makaranta.

"Zaheera zan mutu yunwa!" Tace tana zubewa a kan gadon Zaheeran, ga nata can yanda ta tashi daga barci haka aka bar mata a yamutse don Hajiya Hauwa ta hana masu aikin gyarawa. Har akwatinan kayan ta suna nan yanda aka kawota dashi brush kawai ta cire a ciki, da suka zo share ɗakin suka matsar suka jera mata a wuri guda.

"Baki yi breakfast ba har yanzu?" Zaheeran ta tambaya da damuwa a muryar ta.

Bata iya amsa ta ba sai juyin da ta cigaba da yi a gadon don haka Zaheera ta miƙe ta fita da sauri. Itama bincike ta shiga irin wanda Reinan tayi ta dawo ɗakin bata samu komai ba.

"Umma bata nan ne?"

Reina ta gyaɗa mata kai kawai don bata jin zata iya magana.

"To ko taje siyo miki abinda kike so ne, mu ɗan jira ta"

Ta girgiza kai. Da ƙyar ta iya furta "unguwa ta je"

Zaheera ta furzar da numfashi. "To muje Wurin aunty Zahra ta kira mana ita a waya"

"Wayyoo Allah ciki na, wayyoo daddy na" hawaye suka cigaba da bin fuskar ta tana murƙusoso.

Fita Zaheera tayi taje ta shiga bugun ƙofar Zahra, tun tana yi a hankali har ta saka hannu biyu ta shiga bugun kofar amma yanda Zahra ta ƙure volume ɗin headphones ɗinta bata ma ji, kuma koda taji bata da niyyar buɗewa.

Bugun ƙofar da yayi yawa ya sanya masu aikin gidan shigowa tunda sun san da tafiyar Hajiya, suka fara tambayar Zaheera abinda yake faruwa.

"Reina ne take jin yunwa, kuma Umma ta fita an kulle store shine Aunty Zahra zata kira mana ita a waya." Tayi musu bayani.

Wayar ta mai aikin ta ciro ta danna kiran Hajiya Hauwa, sai da tayi mata two missed calls bata ɗaga ba kafin tunanin wani abu ne ya samu ɗaya daga cikin yaranta ya saka ta ɗaga na ukun.

"Yaya aka yi Amina!"

"Hajiya daman aunty Zaheera ne take son magana da ke" ta miƙa ma Zaheera itel mai tocin ta karɓa ta ƙara a kunne.

"Hello Umma"

"Mai ya faru Zaheera? Ina tare da mutane fah."

"Umm.. daman Reina ne wai tana jin yunwa sosai, shine nace kin kusa kawo mata abincin ne?"

"Kinci uban ki Zaheera. Kika sake damuna a kan yarinyar nan ranki zai ɓaci, tunda an bata abinci lokacin da kowa yake ci taƙi ci yunwa ya kasheta ita taji wurin" ƙitt ta katse kiran.

jikin Zaheera duk yayi sanyi, ita yanzu yaya zata yi da Reina?.

"Me hajiyan tace?" Amina ta tambaya.

A maimakon ta amsa sai ta mayar mata da tambayar "babu wani key ɗin a wurin ku?"

"Wallahi babu Aunty Zaheera, saidai idan zata iya cin shinkafa da wake idan an gama na ɓangaren mu sai in zuba mata kafin hajiyar ta dawo"

"Toh dan Allah kuyi sauri. Bari na koma na same ta."

Da Zaheera ta sanar da Reina halin da ake ciki bata iya haƙurin zaman jira a ɗakin ba sai gasu a kitchen ɗin waje suna zaune a gaban murhun itace mai ɗauke da ƙaton tukunya, idanun su yayi jaa saboda hayaƙi sai jan hanci suke yi.

Shinkafar ko gama tsantsamewa bata yi ba aka zuba ma Reina a plate ɗin roba aka bata wani cokali fakayau da taji kaman bata riƙe komai ba saboda rashin nauyi, gashi yaji jiki, amma haka ta tsoma cikin shinkafa da waken da aka yaryaɗa musu mai da yaji ko latas babu haka take kai loma tana lumshe idanu saboda daɗin mai da yajin har maɗiga.

Kan kace mene ta kusa tashi da rabin plate Zaheera ta ƙura mata idanu kaman TV riƙe da cokalin da aka bata itama su ci tare.
Haka Reina ta tashi da plate ɗin ita kaɗai ta buƙaci ƙari, suka ƙara mata suka bata pure water mai sanyi.

Bata iya ɓula pure watern ba ma tunda ba taɓa sha tayi ba, sai ruwan gora. sai da amina ta ɗaurayo kofi ta juye mata kafin ta iya sha, tana fitar da kakkaurar gyatsa, duniyar ta da ya hargitse ya fara dawo mata dai-dai.

"Toh muje kiyi wanka" Zaheera ta buƙata don zafin Ranar wurin ya fara damun ta, sai a lokacin ma Reina ta lura da dattin da kayan jikin ta yayi.

Babu godiya suka tashi suka bar musu komai a wurin ga shinkafar da ta zuzzubar.

Kayan jikinta Reina ta cire ta jefa a laundry basket ɗin Zaheera sannan ta bata aron bathrobe ta saka tunda bata ciro nata ba. Ta shiga tayi wanka da komai na Zaheera kana ta fito ta bata lotion ta shafa.

"In taya ki buɗe kayan mana kinga nawa ba zai yi miki ba" ta faɗa tana daɗa kallon ƙiban Reina ɗin na renon Alhaji Tahir da ya ninka na da saboda tarin carbs da calories babu nutritional balance, domin abinda take so take ci a lokacin da take so uwa ba kwaɓa.

Su biyu suka kama babban akwatin kafin suka iya sauƙe shi wanda suke tsammanin kayan sakawa ne a ciki.
Kayan sakawan ne kuwa, a goge a ninke. Amma kafin kace mene sun yi filla-filla da su a tsakiyar gado, har ta samu wata shirt peach colour da jeans ta saka a jikin ta, tulelen tumbin ta ya taso a cikin shi Masha Allah, ga ƙugun wandon wane yaro amma ba don ta ɗan saɓe kwana biyunnan ba ma da shiga da ƙyar ne.

Suka buɗe sauran akwatunan don ciro turarukan ta da sauran kayan buƙata, sai dai duk wani abu mai kyau Idan Zaheera ta saka idanun ta a kai sai tace ma Reina tana so, ita kuwa tace ta ɗauka.

Kafin su gama cire kayan ta kwashe kusan kwatan kayan ta da wasu abubuwa har da wanda ba zasu yi sizing ɗinta ba tace zata bawa tailor a rage mata.

*Seemahwrites ✨*

44

~~~~~~~~~~
_Desolé mon amour, I'm trying my best_
_Don't know what's in store, open up the door_
~~~~~~~~~~

Sai da suka zo kan wani littafi mai zanen flowers masu kyau a jiki yana rufe da wani ɗan ƙaramin kwaɗo, kafin Reina ta janye shi lokacin da Zaheera ta saka hannu a jiki.

"Banda wannan" tace tana manna littafin a jikin ta kana ta ɗago shi tana kallo hannun ta a kai tana shafawa ƙwalla na taruwa a idanun ta.
Sunan dake rubuce a wurin da aka tanada ta ƙasa ya saka hawayen idanun ta sauƙa saman kuncin ta.

'Fauziyya Ahmad Malami'

"Na Auntyna ne." Ta ambata cikin shaƙaƙƙiyar murya.
Chapter 4 · 0% Book details