Sashe 81
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke da Maama kuma? Ai bayi son taron mutane kekuwa, kema sai da na roƙa ya yarda zai gana da ke so preparably ki fito sai in zo in ɗauke ki"
Tayi shiru tana juya zancen shi a kanta. Ta ina zata iya shiga motar shi a yanzu? Kuma daga shi sai ita? Ita da take shirin zama matar aure gobe?.
"This is a once in a lifetime chance Hafsah, idan kika yi missing ba zai sake dawowa ba. Zaki iya fitowa har muje mu dawo Ummin ma bata sani ba tunda ba daɗewa zamu yi ba."
"A'a uncle Bilal, babu yanda za'a yi har in bi cikin mutanen nan in fita babu wanda ya tambayi ina na nufa, kuma ko na samu na fita babu wanda ya lura kafin in dawo na san sai an nime ni tunda taron domin ni ake yi."
"Kin gwammace ki haƙura da rashin lafiyar mahaifin ki kenan?"
"A'a wani mafitan zamu nima koma in sami ummin in yi mata bayanin yanda ake ciki."
"Shikkenan. Do as you see fit" ya katse wayar shi.
Sai ta barshi kawai a kan idan tayi isha sai ta samu Ummi tayi mata bayani ta haɗa su ko da aunty Sajida suje su dawo, amma don fita kam ba zata fita ita kaɗai ba.
Tana cikin sallar Isha ƙofar ta buɗe aka shigo aka mayar da ƙofaf aka rufe. Sallamewar da zata yi ta ga Aicha a gefenta tana sake mata murmushin ta mai ajin nan.
"Idan kin shirya muje uncle B ɗin na jira"
Kwarjinin da tayi mata a lokacin ya saka ta amsa da "toh bari na canza wani kayan"
Ta miƙe tana barin wayan ta a wurin.
Sai da ta ɗauki kayan da zata saka ɗin ta shiga banɗaki da su kafin Aicha tayi wuff ta ɗauki wayan ta saka pin ɗin da uncle B ya faɗa mata sai gashi kuwa ya buɗe. Yana kan message ɗin Yaseer already don haka ta shiga typa wani abu da sauri-sauri har sai da ta ji alamun Reinan zata fito sannan tayi saurin sending ta goge shaida ta ajiye mata wayan lokacin da ta fito cikin wata doguwar riga har da hijab ma a cikin toilet ɗin ta saka don bata son Aicha ta gani mata jiki.
Bata san yaya aka yi Aicha tayi convincing ɗinta suka fito basu sanar ma ummi ba, kuma aka ci Sa'a basu haɗu da kowa cikin masu faɗa taji ba a hanyar su ta fita.
Motar Aicha suka shiga suka yi tafiya can cikin new GRA sai gasu a gate ɗin wani gida. Ta ɗaga waya ta kira Uncle B tana sanar mishi da isowar su Amma Reina ta lura da sai kallon mirror take yi kaman wani na biye da su.
Lokacin da Reina taga an buɗe gate Aicha zata danna hancin motarta ciki sai ta samu bakin da take jin kaman an saka super glue an nane mata shi ya buɗu.
"Gidan waye nan kuma?" Ta tambaya.
"Gidan doctor ɗin ne."
"Ba ance baƙo bane a yau ma zai koma?"
"Uhmm.. amm.. yana da gidan da yake sauƙa a nan ai dama."
"Gaskiya zan koma in yaso ko Abba sai mu sanarwa ya zo suyi maganan kawai, amma hankali na bai kwanta ba."
Uncle B ta gani ya fito daga gidan ganin an wangale musu gate basu shigo ba, ya san bai wuce Reina bane ta tsaya taurin kai don haka yazo zai shiga da su.
Jiniyan da suka fara jiyowa kaman daga sama yana tunkaro su gadan-gadan ya saka Aicha sauƙe numfashi cikin sadaƙarwa, shikkenan komai ya ƙare tun kan ya fara.
Tsoro ita kuma Reina ya hana ta fita tana leken abinda ke faruwa ta window, har sojoji masu yawa suka firfito daga motocin kowa da makami a hannun shi ɗaya a cikin su kuma ya saita pistol a kan uncle B, bai bashi daman ko waiwayan inda motan yake ba hannun shi a sama suka tasa ƙeyar shi har cikin motar su suka saka shi suka kara gaba.
Suna wucewa kuwa kaman an yi ruwa an ɗauke layin ya sake ɗaukan shiru daman yawanci sabbin gine-gine ne da filaye a wurin.
Sai a lokacin Aicha ta shiga sauƙe gauron ajiyan zuciya ganin ta tsira, bata cewa Reina komai ba dai har hasken wani mota ya dallare su again.
......
*Yaseer*
Duk da bai taɓa aure ba wannan ne karon shi na farko amma ya san cikin abubuwan da suka kamaci ango banda kwanan office. Sai dai gashi nan saboda yana so ya bawa amarya cikakken lokacin sa bayan biki ya saka ya mayar da hankali wajen ganin ya rage ayyuka masu yawa kafin ya ɗauki hutu.
Yana tunanin ta sai ga notification sound da ya saka mata saboda ya ajiye ko me yake yi idan ya ji yayi ƙara, don haka ba ɓata lokaci ya ajiye pull stop a abinda yake typawa ya ɗago wayan ya duba saƙon ta.
Kallo na farko da yayi ma saƙon ya ji a jikin shi wannan ba rubutun Reina bane saboda ina tarkacen emoji da take sakawa a duk layi? Sannan bata spelling properly ta fi gane abbreviation da slangs amma kuma waye zai ɗauki wayan ta har ya tura mishi saƙo?.
sai dai ya mayar da hankalin shi kan abinda saƙon ya ƙunsa wanda bai karanta rabin shi ba ya mike zubur a kan kafafuwan sa yana kaiwa ƙarshe kuma yayi hanyar fita.
Abbah ya kira ya turo mishi numbern general mahaifin Bilal. Jin urgency dake muryar shi ya saka abban bai tsaya bin ba'asi ba ya turo masa. Yayi parking a hanya ya tura masa saƙo don ya san ko ya kira ma tunda bayi da numbern shi ba lallai ya shiga ba.
Babu jimawa kuwa sai gashi an kira shi da numbern ya ɗauka.
"Bilal din na ina?" General ya tambaya cikin dakakkiyar murya.
Address ɗin da Aicha ta tura mishi ya faɗa masa, general ya kashe wayan cikin zafin rai ya kira division commander na Bauchi aje a kawo masa Bilal cikin daren nan ko da amincewar sa ko babu don yayi kaɗan ya ɓata masa suna a lokacin da yake niman hawa tsani mai girma.
Yaseer har ya iso layin sai ga jiniyan su kaman zasu tashi sama, ya koma gefen hanya yayi parking yana kallon su har suƙa ƙarasa suka kamo Bilal suka yi gaba.
Sai bayan sun tafi ya kunna motar shi ya ƙarasa inda na Aicha yake. Tana gane shine ta fito daga motar ganin haka itama Reina ta fito, da ita da Aichan ba zaka ce ga wanda yafi wani tsorata ba.
"Zo mu tafi Umry" yace da Reina ko kallon ta baya yi saboda ran shi ya ɓaci da gaske.
Ya dubi Aicha "na gode sosai"
Ta ɗaga kai sau ɗaya sannan ya juya ya koma cikin motar shi Reina ma tayi saurin shiga gaba ya kunna ta suka bar wurin.
Sun yi kusan rabin tafiya amma tana gumm da bakin ta don ita bata fahimci abinda ya faru ba fa kwata-kwata.
Ganin idan ya barta wannan karon ma haka abun zai wuce ya saka yace "Reina ki bani haƙuri, kin ɓata min rai ki bani haƙuri." Muryar shi babu hargowa amma a hakan ta firgitata ga yanda idanun shi suka sauya kala.
"Kayi haƙuri yaya Yaseer. Kayi haƙuri don Allah ba zan sake ba."
Ya haɗiyi miyau tare da fushin shi sannan yace "na haƙura"
Haka suka isa gidan Ummi ya shigar da ita har ciki don hankalin shi bai kwanta mishi da barin ta a wajen gate ba. Su kuwa ƴan biki masu kwana zaune suka samu na cewa; ashe ba zallan amarya bane babu kunya har da angon ta.
Saturday.
11:05 am.
Yana zaune tare da sauran ɗumbin mutane a matsayin shaida aka mallaka mishi burin ran shi. Hafsatu ta zama tashi, kowa ya shaida.
~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
98
"Ke Umairah! Ina Umairah ne?" Aunty Sajida ta turo ƙofar ɗakin ta shigo ɗauke da rufaffen bokitin plastic mai ɗauke da ruwan zafi.
Daga ƙuryar gado ta hango ta tana shaƙar baccin ta hankali kwance, ta jinjina kai, lallai yarinyar nan bata san mai yake jiranta ba.
Tayi hanyar toilet ta buɗe ƙofar ta fara ajiye bokitin hannunta sannan ta ƙarasa jikin gadon tana bubbuga ta. "Umairah! Zaki buɗe idanun ki ne ko kin fi son sai an daura miki Yaseer ɗin tukunna, Kada kiyi zaman jira?"
Maganan ya saka ta ƙyalla ido ɗaya tana kallon ta kaman yau ta fara ganinta.
"Ki tashi kiyi wanka, Ko kin fasa ne a je a faɗa musu?"
Har yanzu booting take yi don barcin ba wai isan ta yayi ba tunda ba samun shi tayi a kan lokaci ba. "Ƙarfe nawa ne?" Ta tambaya tana tashi zaune tare da sosa damtsen hannunta.
"Lokacin miƙa mishi ke ɗin da saura ki dai tashi ki shirya kiyi zaman fargaba kaman kowa kema ki ji yanda ake ji."
Ba zata bi nata ba don haka ta waiwaya bayanta ta kalli agogon dake manne a bango yana gwada ƙarfe 7 da mintuna 12.
Tayi saurin juyowa kaman zata fasa ihu tace "haba Aunty Mummy, barcin awa uku fa nayi dan Allah, shiyasa nace ma Maama kada a tashe ni sai karfe 9 ko goma, wallahi jiya da ƙyar na samu na rintsa kuma duk na gaji.
"Wai nace me aka yi da maza? Sannan me ya hana ki barci keda hankalin ki yake a kwance? Ni ban taɓa ganin amarya mai kwanciyar hankalin ki ba ma"
"Hmm" tace tana maimaita kalmar kwanciyar hankali a cikin ranta, da ta san kalan tashin hankalin da tayi experiencing a daren jiya ba zata ambata mata kalmar kwanciyar hankali ba. Dukda har yanzu idan wuƙa zaka saka mata ba zata ce ga abinda Ya faru ba, ganin komai dai tayi kaman a cikin shirin film sannan har yanzu cikin su biyun yaya Yaseer da Aicha babu wanda yayi mata bayanin abinda ke faruwa balle Uncle B da aka sakawa bindiga aka tura shi a mota kaman wani criminal.