← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 117

Sashe 50

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta san yaya Yaseer ba dawowa da wuri zai yi ba yau ma, kuma Uncle B yace zasu yi waya shiyasa tana shiga ɗakin tayi wanka ta zura kayan barci ta bi lafiyar gado ta laluɓo number masoyi, in yaso suka gama wayan sai ta je tayi ma daddyn ta da sauran mutanen gida sai da safe ta dawo ta kwanta.

Ta gama yamutsa gadon da juyin da take yi daga farkon gadon zuwa ƙarshen shi Saboda daɗin wayar da take ji, awa kusan biyu suna abu ɗaya har goma ta gota basu saka lahadin gamawa ba.

Yaseer bai sake kira ba har sai bayan da suka iso gidan ya shiga ya watsa ruwa yaci abinci sannan ya sake kiranta amma still on another call yake ji.

Ran shi in yayi dubu ya gama ɓaci, kuma yayi danasanin bawa Reina waya ya ƙara.
Bai iya jurewa ba sai da ya tambayi ƙannen shi ko kwanciya tayi da wuri amma dake tana ƙoƙarin yi musu sai da safe musamman yanzu da suka ɗan fara shiri da kowa banda suhail sai suka ce masa A'a.

Don haka shi yayi musu sai da safe ya koma ɗaki.

Bai ɓata lokaci ba ya haɗiyi ƙwayoyin shi ya ƙure gudun AC ya shiga ƙasan duvet, domin idan bai samu isasshen barci a wannan daren ba Reina zata iya mishi sanadin kwanciyar asibiti.
.
.
Zafin da kunnen ta zuwa kuncin ta ke yi ya saka ta sauƙe wayar zata mayar da shi speaker tunawa da ita kaɗai ne yau a ɗakin nan idanun ta suka sauƙa a kan lokaci.

"Sha biyu saura?" Ta ambata da mamaki tare da saurin mayar da wayan kunne "Uncle Bilal it's quarter to twelve!"

"Seriously?" Ya tambaya yana duba agogon bangon ɗakin shi.

"Wow doll ya kamata in kwanta gobe zamu fita da general da sassafe. Ke kam you're free gobe ko?"

"Yeah, lectures ɗin da ya kamata mu yi goben ance last week double period ya ci. So we're free"

'Ance double period ya ci' yana nufin bata je ba kenan amma hankalin shi bai kawo nan ba ma sai cewa yayi "Kinga da ina gari ne sai in zo mu sake fita yawo, but zan dawo soon"

Da haka suka yi Sallama, ta gwada fita dubawa ko mutan gidan sun yi barci ta samu har an kashe wutan parlon ƙasa don haka ta dawo ta kwanta itama.

7:02am

Sai da ta gama haɗa komai a cikin mixer sannan ta kunna shi, tana tsaye a kan shi don kada yayi over beating don haka tana ganin komai ya haɗe ta kashe mixer ɗin ta zuba reisins da shredded coconut sannan ta sake kunnawa ya ɗan juya shi kaɗan ta sake kashewa ta ɗauko cupcake tray ɗin da ta gama jera paper cups a ciki ta zuba batter ɗin sannan ta saka a oven ɗin da ya riga ya ɗau zafi.

Daga nan ta koma haɗa filling ɗin samosa, ta riga tayi wraps ɗin ta gama don tashin asuba tayi ta shiga kitchen din ta samu ta rarrashi yaya Yaseer da abu mai daɗi.

"Umm-umm... ƙamshin me nake ji haka Aunty Reina?" Irfan ya shigo kitchen ɗin Sabir da Suhail suna biye da shi a baya.

Faffaɗan murmushi tayi ta juya ta nufi oven ɗin bayanta tana faɗin "cake ɗina ya gasu kenan"

Da zafin sa Irfan ya ɗauki ɗaya bayan ta ciro, ya kai baki Reina ta bishi da gargaɗin yayi a hankali kada ya ƙone.

"Wow delicious. Ke kika yi wannan yanzu? Gaskiya kin iya" Ya jinjina mata yana gyaɗa kai.

Reina baki har kunne. Ya ɗebi wasu biyu a hannun shi yana faɗin "bari na kai wa Yayanmu na ga yana shan tea sai ya haɗa"

Tayi saurin dakatar da shi "A'a a hannu kuma zaka kai mishi?" Tsayawa yayi ta ɗauko haɗaɗɗen baƙin bowl Irfan ya zuba a ciki. Zata ƙara mishi Sabir yace "ai ba shi kaɗai bane akwai sauran mutane suma zasu so ci"

"Akwai saura fa da ba'a gasa ba, kuma idan ya ƙare ma zan sake haɗa wani"

"Sai ki bari idan kin gama ki ƙara masa"

Ba don ta so ba aka tafi ma Yaseer da cupcakes guda biyu Sabir ya raba musu sauran baƙin ran Suhail bai hana shi karɓa ba, Sabir ɗin ya tafi kai ma Aicha ma.

Reina Ta sake zuba wasu a oven ɗin sannan ta koma kan haɗin samosa ɗin ta, can kuwa sai gashi ya zo da kan shi. Ya shigo yana faɗin "mai haƙuri kace wai ba za'a ƙara min cake b..."

Bai iya ƙarasawa ba ganin ita kaɗai ke aiki a kitchen ɗin, kenan cake mai ɗumi da daɗin da aka kai masa ita tayi?

Sabir bai lura da canjin yanayin sa ba ya amshe da "Yayanmu fa ba'a gama gasawa bane, za'a ƙara maka idan an ciro Sauran"

"Yaya Yaseer ina kwana" ta gaida shi tana ƙoƙarin ɓoye fargaban ta.

Gyaran murya yayi cikin basarwa ya amsa da "lafiya, daman kin iya baking ne?"

"Eh ai sana'ar aunty na ne, nima na taɓa kaɗan lokacin da nake buƙatar kuɗi."

Sai ta bashi tausayi, yace "Allah sarki." Cikin ran shi yana addu'ar rahama ma Hajiya Fauziyya "yanzu idan na sama miki contract ɗin yi zaki iya?"

Da hanzari ta gyaɗa kai tana washe baki "Eh wallahi zan iya Nagode yaya Yaseer Allah ya biya ka da gidan aljanna" baki ɗaya murna ya cika ta ba don wai buƙatar kuɗin take yi yanzu ba domin kuɗin da Yaseer yake bata har ajiyan sauran ta fara ga wanda Abbah da Daddyn Niger suke bata kuma ba zuwa wurin kashewa take yi ba daga gida sai makaranta kullum.

"Zan nima miki, Amma sai na tabbatar kin daina wayan da ya zarce minti talatin, idan ba haka ba just forget it"

Ai da sauri ta shiga gyaɗa kai kaman ƙadangaruwa "wallahi na bari"

Ya kalle ta da gefen ido sai kawai ya girgiza kai ya juya yana ƙoƙarin fayyace yarinta ne ko rashin hankali ke damunta ko duka?.
.
.
.
Zuwa lokacin da aka gama haɗa abun kari Reina ta gama soya samosa da spring rolls ɗinta, ta haɗa da sauran cupcakes ɗin aka fito da shi. Kowa sai da ya yaba ma ƙoƙarin ta, kuma abubuwan sun yi daɗi, don haka da taga Yaseer ya ɗan sake mata sai ta saka ma ranta shikkenan ya haƙura komai ya wuce.

Gama karyawan su kenan ana tattara gidan lokacin ƙarfe 10 da ƴan kai security ya shigo ya sanar da cewa Reina tayi baƙi.

Ajiye towel ɗin hannunta da take goge-goge tayi tana maimaita "baƙi kuma? Ni ɗin?"

Ya amsa da "Eh Hajiya"

Da ace ma baƙuwa yace sai ta ce Safina ce, amma idan Safina zata zo ai zata kirata ko ba haka ba ma ba zasu hana ta shigowa ba domin ta faɗa musu ƙawar ta ce lokacin da taje mata rakiya rannan.

Haka dai ta fita ganin ko su wanene, aka buɗe gate ɗin don basu damar shigowa lokacin da idanunta suka sauƙa a kan Zaheera da Zahra.

Ja da baya Reina tayi ta waro ido hannunta a kan ƙirjinta dake bugawa da sauri da sauri.

"Ku ne?" Ta tambaya tsoron ta a bayyane.

Da ta sani da sai da ta tambayi sunan su kafin a basu damar shigowa.

Baki a washe Zaheera tace "Eh fa! Kayan ki muka kawo" ta mata nuni da mummunan akwatin da take janye da shi, wanda ko takalmin ta a yanzu ba zata ajiye a ciki ba balle kaya. Hatta nata wanda taje da shi gidan sai da Zaheera ta san yanda tayi ta raba ta da su, shine aka bata wani tsoho shekaru kusan biyar tana fafutuka da shi.

"Ki shigar da mu ciki mana sister, ko a nan zamu ƙarasa gaisuwan" Zahra ta faɗa tana wani babbasarwa Amma burinta kawai ta ga yanayin cikin gidan ne domin ta waje kaɗai ma ya tafi da ita.

Zaheera kuma mamaki take yi yanzu a Irin wannan gidan Reina take rayuwa? Ta ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa, tana sanye da atamfa embellish, ɗaya daga cikin sabbin ɗinkin da suka karɓo a gidan Ummi ne jiya, zannuwan da suka siyo da Yaseer ne sai jiyan tailor ya gama ɗinkin.

~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

78

~~~~~~~~~~
_J'ai clingné des yeux tu n'ētais plus la même_
_(I blinked my eyes and you were no longer the same)_
~~~~~~~~~~

Ta daskare a wurin sai gani tayi Zaheera ta wuceta ta kama hanyar ciki, da hanzari Reina ta ƙarasa ta sha gabanta ta dakatar da ita.

"Dan Allah ku tsaya in sanar da masu gidan zuwan ku tukunna"

Bata jira ta cewar su ba ta shige ciki tana rufo ƙofar parlorn ta jingina a jiki, gaba ɗaya hankalin ta ya tashi, ita da sun bata kayan ne kawai suka juya suka yi tafiyar su, amma yanzu me zata ce ma Umma balle yaya Yaseer? Ita kada ma su saka ya sake fushi da ita.

"Lafiyan ki?" Ta jiyo muryan shi.

Saurin ɗaga ido tayi ta dube shi, yana sanye da wata grey oversized Tee yana takowa cikin zatin shi.

Miƙewa tayi da kyau kafin ya ƙaraso ta shiga soshe-soshen ƙeya.
"Uhmm..." Sai ta gwada hanyar waje tabi ta sauƙe hannun ta gagara cewa komai.

Ganin haka ya nufi ƙofar, kaman zata saka hannu ta jawo shi saidai ya riga da ya buɗe don haka ta bi bayan shi.

Tsayawa yayi daga saman matakalan yana kallon su Zahra da suma shi suke kallo lokacin da Reinan ta ƙaraso ta tsaya ɗan nesa da shi.

"Su waye wannan?"

Su ya jefawa tambayar ba wai don bai san su ɗin ba. da wanda suke zagaye da ita, da wanda ke son ta da mai mata mugunta duk ya sani. Amma sai Reina ta amshe da "daman... Su... Su Zahra ne, cousins ɗina"

Ya haɗe fuska bai ce komai ba yana jiran yaji da me suke tafe.
Chapter 50 · 0% Book details