Sashe 109
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai yayi murmushi yana sumbatar ta a goshi ta juya ta daɗa narkewa a jikin shi ƙaran ƙugin ruwa da iska yana kaɗa su har zuciya. "Bae" Reina ta kira bayan minti goma zuwa sha biyar da suke a cikin shiru.
"Zan bada Shaida a kan abinda ya faru a kotu" tace tana jin yanda numfashin Yaseer ya ɗauke na ƴan daƙiƙu domin bai yi tsammanin taji wayan shi na ɗazu ba, koda ma ace ta ji ɗin bai yi tsammanin zata fahimci da ita ake yi ko kuma ga zancen da ake magana a kai ba.
Shiru yayi mata bai ce komai ba, koda ta maimaita sai yayi kaman bai ji ba ya ɗauko mata wani hiran daban har suka gama da wurin suka koma masallaci yayi la'asar Sannan suka wuce gidan adana kayan Tarihi a matsayin wurin da zasu je na ƙarshe don dinner ma a restaurant ɗin hotel ɗin su zasu yi, tun a wurin ta tuttura hotuna ma Safina da Daddynta da group ɗin da su Aunty Sajeedah suka buɗe na musamman suka saka ta.
da safe kuma jirgin su ya ɗaga zuwa Iceland, ya sauƙa a keflavik international airport Reykjavik.
isowar su da kwana biyu, bayan sun ɗan zazzaga Yaseer ya samu daman haɗuwa da mutanen da yayi magana ma Abbah a kan su ba tare da ya jira an yi taron da yake fatan shine zai yi musu sanadin haɗuwar ba don haka ya nemi afuwar Reina a rana ta uku ya fita tun safe har yammaci bai dawo ba, ita kuma tun azahar ta samu tsarki.
*ATBU TH Bauchi Nigeria.*
Ƙarasowa Nurses station Dr Fahad yayi da takardun wani patient ɗin psychiatry wanda za'a mishi transfer zuwa asibitin shi. Nurse ɗin dake jikin computer ta miƙe tare da bashi hankalinta domin sauraron bayanin da yake buƙata ta samar mishi amma shi nashi hankalin ya tafi wurin wacce ta wulga yanzu tana amsa waya bayan ta sauƙe face mask ɗin da ta rufe rabin fuskar ta dashi, ɗaya hannunta cikin na saurayin da suke tare yana janta zuwa wurin da ya kamata su je.
Yayi saurin miƙawa nurse ɗin file ɗin hannun shi yana faɗin "ina zuwa" ya bi bayan budurwar kafin su ɓace ma ganin sa. Amma basu tafi da nisa ba sai yaga sun faɗa ɗakin Scanning.
Saida ya bari suka gama suka fito sannan ya shiga ɗakin yayi requesting ɗin abinda ya kawo ta.
Fitowa yayi ya nufi office ɗin shi, tun a hanya ya ɗaga waya ya kira Uncle B idanun shi a kan takardan dake gwada Zahra ta samu Miscarriage har ana bada shawarar ayi mata wankin ciki don fito da abinda yayi saura.
"Fahad yaya aka yi?" Muryar Uncle B ya shiga kunnen shi. Shirin shiga tiyata yake yi amma sanin Fahad ɗin ba zai kira shi a wannan lokacin idan ba abu mai muhimmanci bane ya saka ya ɗauka.
"Lafiya lau, niece ɗinka ce daman na gani a asibiti ita da mijin ta."
"Wacce kenan?" Ya fara tunanin yaran ƴan uwan shi dake Bauchi kuma suke da aure.
"Zahra" ba lallai ya zamo abinda yake tunani ba, kawai yanda Meesha take complain a kan rawan kan yarinyar da kalan rayuwar da yake gani tana yi a social media ya saka hankalin shi bai kwanta ba kuma da tayi aure garin nan ba girma gare shi ba zai sani.
"Zahra kuma? Ina da niece Zahra?"
"Yes, Fatima Zahra Salis. ƴar sistern ka" ya karanto sunan dake kan takardan hannun shi.
Ɗan shiru yayi sannan yace "Zahra bata da aure, maybe saidai da wani ɗan uwa haka suke tafe"
Shima Dr Fahad shiru yayi kafin a hankali ya warware ma Uncle B dalilin da ya saka yace mijinta ne "ta samu Miscarriage har za'a mata wankin ciki, kuma saida na tsaya na tabbatar da ita ce kafin na kira ka." Kenan zai iya yiwuwa sun yi ƙoƙarin fitar da cikin ne yayi musu gardama shine suka zo asibiti, ba Miscarriage bane kenan abortion ne.
"Nagode Fahad, idan na fito daga surgery zan kira ka"
......
Abuja
*Aicha*
Hannun Rafeeq a cikin gashin ta, jikinta kuma na tsakanin kafaɗun shi, ta ɗaga idanu ta zuba mishi.
Tsayawa yayi da shafa gashin kanta yana duban ta cikin ido ya ɗaura murmushi a saman fuskar shi. "Yaya aka yi Mon amour?".
Bata amsa ba sai zame jikin ta da tayi daga riƙon shi, tana riƙe da duvet ɗin da ya kare mata ƙirjinta ta tashi zaune tana mayar da tsillin gashin da Rafeeq ya sauƙo mata kan fuska baya. Ganin haka shima sai ya tashi ya zauna a gefen ta yana kallonta dukda yana da yaƙinin ya san dalilin rikicewar nata tunda ba yau bane farko.
Hannu ya zura ta bayan ta ya riƙo ta jikin shi "Matata abin alfahari na" ya kira ya tuna mata da cewa zaman halarci suke yi kuma duk mu'amalar da zai shiga tsakanin su ya halarta.
Juyowa tayi tana rau-rau da idanu sai ga hawaye. Ita yanzu ina zata kai kunyar duniya? Basu shaida ta zama ta Rafeeq ba amma har ɗan zaƙin baki ya saka ta bashi kanta ba tare da tanadin da akewa kowace amarya ba.
Kife fuskarta tayi a tafin hannunta wani abu mai kama da nadama yana so ya lulluɓe ta. Rafeeq ya furzar da numfashi ya saka hannu daya ya janye wanda ta kife fuskarta da su Sannan yayi amfani da na bayan ta ya juyo ta suna fuskantar juna.
"Biki ba shi bane Aure Aysh. Al'ada ce kuma binta ba wajibi bane. banga dalilin da zaki dinga ɗaga hankalin ki a lokacin da muke ƙarƙashin inuwar rahamar Ubangiji ba"
girgiza kai ta shiga yi a hankali, Rafeeq ba zai gane mai take hangowa ba. "Nikam zan koma gida please" ko wayar Maami ta daina ɗagawa kuma itama ta daina kiran ta don ta san duk wanda ya san a inda take yanzu ya san me take yi. Koda babu aure keɓewar mace da namiji a wuri guda akwai hatsari balle masu lasisi.
"Kina da gidan da ya wuce inda nake Amor? Ni kece gida na, kece ɗaki na, kece sirri na" yace yana ɗauke mata hawayen fuskar ta, ya shiga karanto mata alƙawuran da ya mayar da ita ƙirjin shi ya sake kwantar da ita, hannun shi ya koma cikin gashin kanta ba tare da ta ankare ba.
....
Sai yammaci Zahra ta shigo gidan su na yanzu wanda yake madaidaici, za'a ma iya kiran shi ƙarami a gaban nasu na da sannan babu jeren motocin nan, tunda duk tattalin arzikin su ya ƙare a case ɗin mahaifin su domin ba ta Jamal ma suke ba yanzu tunda shi nashi case ɗin babu hope.
Ta shiga parlo tana takawa a sannu domin jikinta babu ƙarfi, don ma saida aka ɗaura mata drip bayan an gama wankin cikin, amma taci azaba ba kaɗan ba, abu kaɗan mai haihuwa zata gwada mata.
Da Hajiya Hauwa da maman Meesha taci karo a parlo, ita da tayi tunanin yau babu kowa a gidan tunda an fara bikin ƴar ƙawar Hajiya Hauwa kuma ta riga ta fita a gidan ma kafin ta shirya suka je asibitin.
"Sannu da zuwa Mummy M" ta ɗan ranƙawafa jiki babu ƙwari sannan ta miƙe zata ƙara gaba domin bata da burin da ya wuce ta jita a gado yanzu, ga kuma yunwar dake ƙwakular cikinta.
"Zahra!"
Tsayawa tayi Ta juyo tana kallon Hajiya Hauwa dake zaune idanunta wane gauta. "Na'am Umma" ta amsa tana mata kallon tuhuma sanin yanzu su basu rabo da bala'i a gidan.
"Daga ina kike?"
Sai ta kalli maman Meesha dake zaune shiru ta tsare ta da idanu, ba zai wuce wani munafurcin aka kai mata ta sake ɗaukowa ta kawo mata ba tunda ƴan Bauchi su aikin su kenan saka ido da gulma. Ita ba don karo da suka yi da Reina a hotel tayi tunanin zata fasa mata taya ba da babu abinda zai dawo da ita daga Abuja.
"Gidan su ƙawata naje" ta amsa da ƙarya babu gargada.
"Wata ƙawar ki?"
"Suzanne"
"Na kirata ta haɗa ni da ke tace kina lectures sai yamma zaku gama."
Haɗiyan miyau tayi tunawa da itama suzyn tafi two weeks a lagos so bata san ma ta baro Abuja ba.
"Umma kai na ciwo yake Wallahi, bari in ɗan shiga in huta" ta juya da sauri zata bar wurin maman Meesha tace "daga asibiti kike kenan kaman yanda Bilal ya faɗa."
Sanƙarewa tayi wurin ƙirjin ta na lugude, shaff ta manta da doctor Fahad yana zama a TH duk ranan Alhamis.
Ita bata so zuwa babban asibiti ba daman amma hatsarin da aka faɗa mata zata iya shiga saboda yunƙurin zubar da cikin da suka dinga yi yaƙi fita yasa aka bata shawarar ganin babban likita a babban asibiti.
"Eh gaisuwa muka je shine nabi na karɓi maganin ciwon kan ma. Hala mijin aunty Ameesha ne ya ganmu ya faɗa mishi. Ai mu da course mates ɗinmu ne muka je, mata da maza, muna da yaw..."
Naushin da Hajiya Hauwa ta sauƙe mata a baki ya hana ta ƙarasa shirgo ƙaryan da ta saba. Ta kaita har ƙasa ta hau ruwan cikinta ta zaune don ma yanzu wahala da babu sun fara zabge ƙiban, taci gaba da ɗirkan ta kaman Allah ne ya aikota, ita dake dukan tana kururuwa da kuka da jero mata Allah ya Isa "shegiya tsinanniya! Har kin san kiyi cikin shege ki zubar Zahra? Tarbiyyan da nayi miki kenan?". Ita da da a yanzu bata da sauran burin da ya wuce Zahra da ƴar uwarta. Duk wani bala'in da zasu shiga atleast idan ƴammatan ta biyu suka yi aure a gidan girma da daraja abun zai zo mata da sauƙi, amma yanzu Allah kaɗai ya san zancen yau a ina zai tsaya tunda har ya shiga bakin ƴan ɗakin su Maryam sai sun kai rahoto har bangon Africa bayan Meesha a nan ta gama bin Yaseer a gindi- a gindi amma tudun laifi sai dai ya baka daman hango na ɗan uwanka.