Sashe 11
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Numbern da ya laluɓo ya juyo da fuskar wayar ya nuna mata bayan ya danna kira. Ganin lakanin barrister a tare da sunan wanda yake kira yasa tayi murmushi kana ta juya suka bar falon lokacin da aka daga kiran.
Saida ya samu wuri ya zauna kana ya ƙara wayar a kunne.
Suka yi taƙaitaccen gaisuwa sannan ya ɗaura da "...ka tuna case ɗin da muka fara magana da kai 3 to 4 years ago? Wani attempted rape case na wani yaro?"
~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
48
~~~~~~~~~~
_I'd like to mean it when I say I'm over you_
_But that's still not true_
~~~~~~~~~~
Amsar da yayi tsammani shi barrister ya bashi saboda a lokacin har ya fara bincike a kai Uncle B ya kira shi ya dakatar dashi kuma bai sake ɗago da zancen ba sai yau.
A lokacin tsoro yaji idan yaseer ya kubuta Meesha ta saɓa alƙawarin dake tsakanin su ta koma mishi, ko shi ya rinjaye ta ya lalata mata rayuwa, ko cuɗanyar su da juna kawai ya isa ya saka ta gagara auruwa musu a gaba tunda babu wanda bai san abinda ya faru da Yaseer ba kuma kowa ya san fuskar shi.
Amma a yanzu komai ya daidaita, sun goge mayafin goben Meesha sun naɗe sun adana a wurin da hannu ba zai iya kaiwa ba. A yanzu idan ma Yaron yana da laifi yana da yaƙinin shekaru uku ya isa ya horar dashi ya shiga taitayin shi.
"Yes, Yaseer something na manta surname ɗinshi, but case ɗin nake so muyi reopening." Yayi shiru yana sauraron abinda barrister yake faɗi kana ya ɗaura da.
"Niece ɗina tayi insisting cewa yaron bayi da laifi sharri akayi mishi but ko yana da shi ɗin ma ina buƙatar a fito min dashi saboda alƙawari na ɗauka mata wanda cika shi ya zamo min wajibi, so kayi min ƙoƙari barrister and name your price ko nawa ne"
Sallama suka yi bayan yayi mishi alƙawarin fara bincike nan take, sannan zai samu lokaci ya je yaga yaron a prison.
Daga nan ya danna kiran Hajiya Hauwa.
Har ta shiga mota za'a kai sauran kayan ɗakin amarya gidanta wanda aka kawo daga baya kiran Uncle B ya shigo wayarta, don haka babu bata lokaci tace su tafi ita kuma ta juyo ciki ta same shi.
"Bilal?" Ta kira da tausashshen murya ganin tana zaune a gaban shi ya cigaba da hidimar shi kaman bai sani ba.
"Umm.. Addah Hauwa daman a kan maganar yarinyar nan ne, Reina..." Ya fara magana hankalin shi a kan waya yana duba saƙon da matar shi ta turo mishi a kan lafiyar yaron shi.
Yanda gabanta ya yanke ya faɗi da Uncle B ya kasa kunne tabbas zai ji ƙarar faduwar.
Bai lura da kaɗuwar da take ciki ba, saida ya turawa matar shi reply kan cewa yana hanyar shi na dawowa da an samu flight kana ya ɗago ya dubeta ya ɗaura da "Dame kike ganin zan iya taimaka muku da shi a kanta? Domin riƙon ɗan wani akwai ɗawainiya musamman maraya, duk da ɗumbin falalar dake ciki zai iya muku silar shiga aljannah ba tare da wata gargada ba. toh nima ina ƙwadayin wani kaso daga cikin ladan don Allah "
Yawun da ya taran mata a maƙogwaro ta haɗiye, ta sharce zufan kan goshin ta bayan AC dake busa su jin yanda zancen nashi ya nufa. A kan wannan shirmen ne ya saka ta dakatar da muhimman abubuwa tazo? Saboda banzar Hafsatu?.
"Babu komai fa, ai abban su na ƙoƙari a kanta sosai, in banda rashin godiyar Allah na mutane ai babu abinda Hafsatu ta nima ta rasa. Ko ta faɗa maka wani abu ne?"
"Kamar mene kenan?" Ya mayar mata da tambayar jin yana so ya jiyo ƙamshin rashin gaskiya a maganar ta.
"Toh na sani Bilal? Ka san yaran yanzu kaman da munafurcin su ake haifan su, musamman itama da tarbiyyar ta akwai naƙasu tunda uwarta a son duniya ta ƙare tata rayuwar, zata iya haɗa ƙarya da gaskiya ta faɗa maka".
Da zuciya ɗaya yayi mata magana, da zuciya ɗaya ya kawo wannan shawarar amma Hajiya Hauwa a ƙoƙarinta na ganin ta wanke kanta a idanun shi tunda bata san me suka tattauna da Reinan ba ta saka waswasi ya fara ɗarsuwa a zuciyar shi.
"Addah Hauwa akwai abinda ya kamata na sani ne?" Ya tambaya yana haɗe rai tare da tsareta da idanu duk sai ta daburce.
"Bilal ai sai ka bari idan Allah ya ɗauki ran general kafin ka dawo ubana, ka tsare ni da tambayoyi haka? Ita Hafsatun ba tare kazo ka ganmu ba?"
Jinjina kai yayi "tare na ganku, amma duk ƙarewan tarayya ai ba ke kika halicceta ba. Ki sani ko me zai shiga tsakanin ki da ubangijin ki idan yaga dama zai iya yafe miki amma kiji tsoron hakkin mutum a kanki komai kashin sa, wallahi zai saka ki a cikin bala'i domin Allah bayi yafe laifin wani a kan wani"
Ya miƙe ya bar mata ɗakin don bayi da lokacin sauraron abinda zai fito daga bakinta, idan tana cutar da Reina ita ta sani, bayan ƙaddarar rayuwa ma babu abinda zai raba iyaye da yaran su., shiyasa ya mance da abinda ya shiga tsakaninsu da maman Mufid, idan ma shine matsalar kaman yanda take ikirari zai gyara idan kuma itace zai ƙara haƙuri ya bata dama na biyu amma haɗuwar shi da Reina a yanzu ya saka ya fahimci shekara ɗaya a duniya yayi ma yaron shi kaɗan ya fara gararamba a gidajen ƴan uwa, sannan samun wanda zata kula dashi kamar mahaifiyar shi shima abune da kamar ba zai yiwu ba.
Haka ta wuni da ruwan ciki, tana da tabbacin Bilal bai san abinda yake faruwa ba, saboda ta san shi, kai tsaye zai tunkare ta idan ya sani amma ta wani ɓangaren gani take yi kaman kalaman shi hannun ka mai sanda yayi mata.
Da daddare ana wurin dinner sai ya samu kanshi da dubata, bai ganta a wurin ba. Zaheera ya tura aka kira masa, ta ƙaraso ya tambaye ta ina Reina sai ta fara kame-kame. uwarta saida ta gargaɗeta don ta san Uncle B zai iya tambaya.
"Tana barci ne a gidan Mummy M, kuma bata so a tashe ta shine kawai muka taho" ta shararo karya.
Yaso ya yarda amma sai ga Hajiya Hauwa tazo tana tuhumar Zaheera a gaban shi har saida ta mayar mata zancen su kafin ta shiga ƙara mishi ƙarya a kan ƙarya. A yanzun ma miƙewa yayi ya bar mata hall ɗin, cikin minti 15 ya isa gidan su Meesha, an watse kowa na wurin dinner sai ɗaɗɗai, tsofaffin da suka jigata da kuma wanda aka basu gadin gida.
Baza idanu ya shiga yi a main parlour niman wanda zai tura a kira masa ita lokacin da ta fito daga kitchen tana sanɗa hannunta ɗauke da cupcakes guda biyu.
"Reina"
Zubar da cake ɗin hannunta tayi ta ƙame tana kallon shi. Shima ita yake kallo abinda ba'a bata ba ta ɗibo kenan, sata tayi.
"Zo nan"
Haƙuri ta shiga bashi tana kuka kaman wanda yake zare mata rai har sai da ta fara tara mishi mutanen gidan bata ida ƙarasowa inda yake tsaye ba, kuma bai sake ce mata kyat ba, yana dai kallon ta.
"Ko me tayi ta tsorata ɗan nan, ayi haƙuri" wata tsohuwa tayi magana tana jawo Reina jikinta.
Bai ko san tanayi ba ya sake ambatan "kizo nace"
Da kanta ta ƙwace kanta ta nufi Uncle B. "Rage min tsayin ki a nan"
Ta ƙaraso inda ya nuna jikinta na rawa ta zuba a kan guiwowin ta. Ba zai bari hannun shi ya taɓa marainiya ba dukda ba laifi bane idan tayi laifi yayi mata hukunci amma yana da hanyoyin hukuntata da yawa.
"Kiyi ta marin kanki har sai na tabbatar fuskar ki ba zai sake barin hannun ki ya ɗauki abinda ba'a baki ba"
Zata cigaba da bashi haƙuri ya zare mata idanu, ta shiga marin kanta a hankali.
"In gwada miki yanda akeyi ne?"
Ƙara dagewa tayi tana shararawa fuskar ta mari tana kuka tare da bashi haƙuri. Sai da ya tabbatar ba zata sakeba da take maimaitawa ya isa har zuciyan ta kafin ya riƙo hannun ya matse a cikin nashi ta saki ƙara.
"Ke ana tausayin ki wato baki tausayin kanki ko?"
Girgiza kai tayi, "idan na ƙara Allah ya tsi.." ya saka yatsa ya ɗalle mata baki ta saki wani ihun, tausayinta ya gama cika mutane, sun kuma rasa yanda zasuyi da Uncle B.
"Jeki ki shirya na baki minti 10"
Yaseer!
Yaseer ya tuna mata ranar da zai fara musu karatu.
Abubuwa da yawa suna tuna mata da Yaseer kwanan nan.
"Ba'a zo min da kaya ba"
Sai yanzu ya lura uniform ɗin Islamiyya ne a jikin ta, mai take nufi da ba'a zo mata da kaya ba? Bayan ga Zaheera da Zahra cikin sabbin ɗinki?.
"Ɗauko takalmin ki muje"
Miƙewa tayi zata wuce tsohuwar nan ta miƙa mata cake ɗin da ta zubar ɗazu ai da sauri ta matsar da hannunta daga garesu kaman ta taɓa garwashi. Tayi saurin fita waje ta ɗibo loopers ɗinta a hannu ta shigo dashi, mai kyau da tsada ne sosai tun wanda ubanta ya siya mata amma rashin kula ya saka ya fara fita a hayyacin shi da datti.
Uncle B ya miƙe ya fara fita a gidan kana ta bishi a baya.
Sun ɗan zaga sosai don ba wani sanin kan Bauchi yayi ba kafin suka tsaya a wani babban boutique na inyamurai.
wata Ma'aikaciyar wajen ta nufo su tana tambayar abinda zata taimaka musu dashi, ya gwada Reina "I want a nice dress for her"
Tace su biyo ta zuwa wani section da take tsammanin za'a samu daidai tsayinta suka bawa Uncle B wurin zama kana ta shiga sauƙo da haɗaɗɗun gowns tana gwada mata, ko yayi tsayi, ko ya kasa, ko Uncle B yace bai yi ba.
Har suka kai kan wani haɗaɗɗen navy blue gown mai hawa-hawa da touches ɗin silver sai mayafin net shima navy blue da silver lace a bakin shi.