Sashe 6
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Diddire kafafuwa ta fara "ni dai ka buɗe min, ni sai na tafi" sai a lokacin hawaye ya samu dalilin zuba a kan kuncin ta, ai kuwa ta buɗe su kaman famfo tana kuka kaman Allah ne ya aiko ta, ihun ta kuwa har maƙwafta.
Bata ankara ba sai ji tayi an fisgo hannun ta. Hajiya Hauwa ta fara janta da ƙarfi cikin ɓacin rai. Ƙoƙarin ƙwacewa ta shiga yi amma ƙarfin ba ɗaya ba don haka ta zube a wurin tunda ta kudura a ranta ba zata koma cikin gidan ba.
Ba tare da damuwa ba Hajiya Hauwa ta shiga janta a ƙasan, da taji tayi mata nauyi ma sai ta saka hannu biyu. Zafin interlocks dake gurzan jikin Reina ya saka tayi kiciniyar sake miƙewa a kan kafarta tana ma Hajiya Hauwa tsiwa da zazzaga mata ashariya.
Ba don tana tsoron takalo musu wata masifan ba da dukan shan gishiri zatayi mata a cikin daren nan ko zata huce, amma idan wani yaga tabo a jikinta a satin farko ta san kwaben su tabbas zaiyi ruwa. Don haka ta watsa ta a ƙasan dakin baƙi kawai ta rufo kofar ta garƙame shi.
Rana ta farko kenan da aka tuna mata komai ya sake haskawa garau a cikin idanun ta, haka Jamal ya wuntsulo ta ciki sannan ya biyo ta ya danne, saidai a wannan lokacin numfashin ta ne ya danne mata ƙirji, ƙokarin cisgan shi da ƙarfi da take yi ya saka ganin ta ya fara disashewa, ta fara ficewa daga hayyacin ta kafin ta fara jiyo muryar shi daga can nesa.
"Hafsatu!... Hafsah!... Reina!.... Ki Buɗe Idanun ki."
"Yaseer!" Nauyin da idanun suka yi mata ya saka ta rufe su kawai.
.....
Sai da ta fara jin sanyin ruwan a cikin kwakwalwar ta kana ta jishi a kan fatar ta. A firgice ta miƙe zaune tana jan dogon numfashi hanci da baki, ta kuwa bawa ruwan da ya tuttuɗa cikin hancin ta damar shigewa cikin kanta, taji zafin shi a yanda bata yi tsammani ba kana ya mata mugun shaƙa ta shiga tari babu ƙaƙƙautawa.
"Wa kika ajiye mai gadin ki da zai dinga tashin ki?"
Sai a sannan ta ware jajayen idanun ta a kan Zahra dake tsaye da goran swan water a hannu tana kallon halin da ta jafe ta cikin nishaɗi.
Wani ashar ɗin katsinawa ta mulmulo ta maka ma Zahra kana taci gaba da tarin.
Zahra ta tunkaro ta zata ƙara mata wani marin a kan na jiya Reina dake ankare ta saka mata ƙafa tsantsin ruwan dake zube a kan tiles ɗin ya taimaka wurin kada Zahra warwas a kasa ta ci da baki, ɗagowan da zata yi sai gashi kuwa ya fara jini.
Tayi ƙoƙarin miƙewa ta bar ɗakin kafin zahra ta samu kanta.
Ɗakin su da Zaheera ta nufa tayi saurin saka lock a ƙofar ta ciki sannan ta nufi haɗa kayanta yanzu ta bar musu gidan ba sai anjima ba. kukan yunwar da cikin ta ya fara ya saka ta yanke shawarar sai ta karya tukunna ta tafi don haka ta ajiye kayan da ta fara cukurkuɗa su zata mayar cikin akwati ta buɗe ɗakin ta fice.
Har tama manta da Abinda tayi wa Zahra sai da ta hango ta a gefen Hajiya Hauwa tana matsar ƙwolla ga gefen bakin da ya fashe har an sakawa magani.
"Ina kwana" tace cikin tsarguwa da kallon da Alhaji Salisu yake aika mata amma don ta Hajiya Hauwa ne ba gaida ta zatayi ba saboda fushi take yi da ita, amma babu komai bari mata gidan ta zata yi.
Kallon abincin dake gaban su tayi taga ɗaya daga cikin cimar ta ne don haka ta ja kujerar gefen Zaheera sannan ta jawo plate ɗinta gaban ta in yaso ita ta ɗebi wani.
"Hafsatu!"
Taji muryar Alhaji Salisu Kamar rugugi.
Bata fasa kai loman farko bakin ta ba domin yunwar cikin ta yafi abin tsoro. Ta tauna ta haɗiye kana ta amsa da "na'am" tana ƙokarin tura loma na biyu.
"Sauƙa ki zuba min guiwowin ki a ƙasa" yace yana gwada mata inda zata zuba ɗin.
Shima loma na biyu sai da ta taune shi kana ta amsa da "Iye??!" Domin da gaske bata fahimce shi ba. Ma mutum ɗaya ta taɓa yin kneel down kuma bata jin idan ba shi ɗin ba wani zai iya sakata.
"Ki sauka nace!" Ya daka mata tsawa.
Firgici ya sanya ta ɗago da plate ɗin abincin, su kuwa suna ganin ikon Allah har ta ƙarasa wurin da Alhaji salisu yake nunawa ta zube a kan guiwowin ta kana ta cigaba da cin abincin ta, ai yunwa ba ƙanin ubanta bane.
Abin sai yaso bawa Zahra dariya, Zaheera kuwa kallon tausayi take binta dashi, Hajiya hauwa bata ce komai bane saboda ta riga ta miƙa ƙara wurin Alhaji Salisu, amma da dukan da ta hana kanta yiwa Reina jiya shi zata yi mata yau duk abinda zai faru ya faru.
Shi kuwa Alhaji Salisu tagumi ya saka kawai yana kallon ta cike da takaici. Lallai sun ɗauko ruwan dafa kansu.
~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
45
~~~~~~~~~~
_In the back of my mind, I'm still overseas_
_A bird in a cage, thought you were meant for me_
~~~~~~~~~~
Su biyu ake jira kasancewar Zaheera ta tsaya taya Reina shiryawa, ko da suka fito Reina na gaba Zaheera na biye da ita a baya riƙe da jakar makarantar dukan su biyu. Seat ɗin baya ta buɗe ta shiga zata rufo ƙofar taji muryar Zahra tana faɗin "malama fita ki shiga gaba"
Bata ko kalleta ba ta jawo ƙofar ta rufo shi, Zaheera da ta ƙaraso ganin Reina ta shiga bayan sai kawai ta buɗe seat ɗin gaba zata zauna tare da driver.
Ba damuwar ta bane duk abinda Reina zatayi ma Zaheera tunda ta lura ita take cusuwa mata amma dake tana cike da haushin fasa mata baki da tayi gashi Abban ta ya gagara hukunta Reinan yanda zata ji sanyi sai ta buɗe kofar ɓangarenta ta fita.
Reina na ganin alamun zagowa zata yi ta fitar da ita sai ta saka ma ƙofar lock sannan ta riƙe hannun shi gam-gam yanda koda Zahra ta koma ta ɗaya ɓangaren tana ƙoƙarin jawota ƙarshe haƙura tayi don ba za'a haɗa karfin ƙashi da tsoka da ƙashi da rai ba.
Driver ya shiga roƙon su ganin zasu yi latti kuma ya bari hajiya Hauwa ta fito laifin kan shi zai koma.
Haƙura Zahra tayi ta koma ciki saidai bata fasa laccin Reina da dungure mata kai ba dukda nesa da juna suke zaune.
.
.
A ɗarare ta ƙaraso gaban kujerar Reina, tana kwance ta kifa kanta a kan desk. Sai ta ajiye mata ɗan container tare da cokali mai yatsu kana tayi saurin matsawa baya a tsorace tana zazzare idanu.
Dagowa Reina tayi ta kalli containern sannan ta kalli mai ita, jikin ta sai tsuma yake yi amma bata bar wurin ba.
"Da banzo karba bane shine kika kawo da kanki ko?" Wato yanzu har masu tsoron ta tausayin ta suka koma ji Saboda abinda ya samu daddyn ta "Zo ki ɗaga abun ki bana ci"
Sai yarinyar ta amsa da "Cake ne" tana ƙara matsawa baya domin ba ƙaramin aikin Reina bane ta buɗe abinda ke ciki ta wanke mata jiki da shi.
Da hanzari Reina ta buɗe, ta kuwa yi arangama da slice cake na red velvet, Ba irin shi tafi so ba amma an dade ba'a haɗu ba don haka ta saka fork ɗin ta yanki babban loma ta angiza a baki tana lumshe ido. Yaushe rabo?.
"In kawo miki juice ko ruwa?" Yarinyar ta tambaya cike da jin daɗi.
"Duka. Banzo da komai ba yau" ta amsa. Da sassarfa ta koma ta ɗauko kwalin happy hour guda biyu a jakar ta da water bottle ta dawo, lokacin wani taƙadirin yaro shima da ake jin tsoron shi a ajin ya ƙaraso gaban desk ɗin Reina ya zauna, kaman kullum tayi kaman bata san dashi a wurin ba taci gaba da cin cake ɗinta, domin yanzu tana kula shi sai sun bawa hammata Iska kuma duka yake mata ya bata kunya a gaban yara.
"Ke yaya kike kallo na?" Ya zare ma Safina idanu.
Abun hannunta ta ɗaga mishi cike da tsoro "wannan zan bata"
"Toh kawo" ya miƙa mata hannu, da mamaki ta ƙarasa ta bashi don tayi tsammanin korata zai yi.
"Ya ishe ki Reina ko in kawo miki wani?" Ya jefa mata tambayar Sai ta ɗaga ido ta kalle shi da cake ɗin da ta cika bakin ta bata samu taunawa ba don haka cikakkun kumatun ta suka sake haurowa kumbus, ko wani sabon salon muguntan yau ya samo shiyasa yake mata magana cikin tausasawa.
Amma har a fuskar shi taga tausayin ta, ita abar tausayi ce?
Share shi tayi ta cigaba da kai loma, gani take yi kaman idan bata yi ta cinye ba cake ɗin ma rabata za'ayi da shi.
Shigowa ajin Zaheera tayi rungume da littafin jiya ta tunkaro su dai-dai lokacin da ya saka Yatsar shi ya share mata cream ɗin da ya shafu a gefen leɓɓen ta.
"Ba sammaka zanyi ba Wallahi" Reina ta riƙo hannun yaron ta saka a bakinta ta lashe kafin ta sake mishi, dukkan su uku suka tsaya suna kallon ikon Allah.
Saɓule jiki Safina tayi kafin su kaure da riciki ya ritsa da ita. Sai yaron kawai ya murmusa ya ɗauki juice ɗin ya saka straw ya ɓula mata.
"Na faɗa miki idan kina son ƙari ma zan baki, ke yanzu ƙanwata ce. Ki gama muje muci abinci"
Ta harare shi tare da murguɗa baki kana ta fauce juice ɗin, ita bata son munafurci. Haɗiyan miyau Zaheera tayi ta ƙaraso wurin da suke sannan ta kira sunan yaron.
Haɗe fuska yayi daga murmushin da yake yi ma Reina lokacin da idanun shi suka sauƙa a kan Zaheera. Ta mika mishi littafin hannunta guda biyu "gashi na gama kofan note ɗin"