← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 117

Sashe 22

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya sawaƙe a haɗa biki na da wancan abun, habawa Umma sai kace bani da gata? Rana ɗaya na rayuwa na wanda idan ya tafi ba zai sake dawowa ba sai in bari Hafsatu ta lalata min?"

Cikin faɗa-faɗa Hajiya Hauwa tace "Toh ke so kike yi ta riga ki aure ne mutane su samu abin faɗa? Ba don Bilal ɗin ba har Zaheera sai na ɗaga a gaba na kafin a saka ta cikin lissafi, saboda idan ta tafi wa zan samu yake mun ɗawainiyar da take mun"

Turo baki Zahra tayi tana ƙunƙuni "ni dai gaskiya da sakel" ta miƙe kwance a kujeran tana cigaba da liking hotunan Yaseer.

.....

*Reina*

Ba don gargaɗin da aka yi mishi na kada yayi mata magana ba da sai ya tsayar da napep dinnan ya bata haƙuri ta daina cika mishi kunne kafin su cigaba da tafiya. Gudu yake yi kada mutanen kan hanya su jiyo gunjin kukan ta su ɗauka sato ta yayi, don haka cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gate ɗin makarantar.

Naira 300 kuɗin seat ɗin baya duka ya bawa wani adaidaita mai lasisin shiga makarantar ya ɗauke ta, koda suka zo shiga ciki aka tambaye ta ID card kukanta ya saka security suka ce su wuce kawai.

Da ƙyar ya samu ta faɗa mishi yanda zata je ya kaita ya ajiye ya juya. Babu kowa a waje alamun an riga da an fara jarabawar kenan, sai kawai ta nemi wuri a wurin ta zauna ta cigaba da abinda ya kawo ta.

Ɗaya daga cikin invigilators ne ta fito domin tana damun su tace "Hey are you with us?"

Ta gyaɗa kai.

"Kin tambaya an hana ki shiga ne zaki dame mu da ihu?"

Ta girgiza kai.

Ta ja tsaki, "zo ki shiga"

Sai ta sake girgiza kai, takaici ya kama ta, "toh idan cika mana kunne zaki yi sai ki ƙara gaba" tayi juyawar ta ta koma ciki.

Miƙewa Reina ta saƙala jakar ta a kafaɗa zata bar wurin, Safina tayi saurin ajiye abun rubutun ta fara sauƙowa daga can bayan hall ɗin zata bi bayan ta, matar ta dakatar da ita.

"Har kin gama ne?"

Ta girgiza kai damuwa ƙarara a fuskar ta "No ma'am, ƙawata ce Please"

"Okay kiyi submitting sai ki bi bayan ta" ta miƙa mata hannu daga inda take alamun taje ta ɗauko answer booklet ɗin ta kawo.

"Please ma" Safina ta haɗa hannu biyu cikin sigan roƙo ganin Reina har ta fara nisa daga wurin "itama tana ɗaukar course ɗin, idan ta tafi zai zama mata carry over"

Ganin ko a jikin ta yasa Safina cigaba da sauƙa zata bar ajin, idan ma rasa jarabawan zata yi saidai su rasa su biyu, amma ba zata yi submitting ba tunda ko rabi bata yi ba kuma ba zata bar Reina ta tafi haka nan ba.

Idanun kowa ya bar kan jarabawar su ya koma kanta yanda rai a bace take haɗa stairs bibbiyu tana sauƙa har ta kai gaban ajin kafin wani malami da ake masa kallon mugu shi ya tsayar da ita yace ta koma zai je ya zo da Reina.

Ya fita tana gani amma ta kasa komawa matsugunin ta. Da ya isa wurin Reina ma yanda kasan yana yi da dutse haka ta cigaba da tafiyar ta, gashi kukan da take yi ya bashi tausayi kamar wanda aka yi mata mutuwa, kuma yana tsoron taɓa ta yanzu ya shiga bakin ɗalibai don sauran venues ma idanun su yana kan su.

Ganin haka Safina ta share gargaɗin malamar nan ta fice da sassarfa ta ƙarasa wurin da take ta rungume Reina a jikin ta itama ta saki kuka ba tare da ta san dalilin da ya saka aminiyar tata kukan ba.

Sun sha kuka kam harda masu ɗaukan su a waya wanda basu da jarabawa a lokacin,
Sannan Safina ta rarrashi kanta ta rarrashi Reina suka koma ɗakin jarabawar.

"Kiyi haƙuri ki rubuta ko yaya ne tunda kin riga kin zo ko? Zan ƙara miki minti talatin bayan tashi" malamin ya ajiye mata answer booklet bayan ya bawa Safina ta rubuta mata reg number da su department.

Haka tana rubutu tana hawaye har tayi ɗan abinda ya samu ruwan idanun ta basu fasa cigaba da jiƙa shafukan ba.

Safina tana fita ta kunna wayarta ta kira daddynta ta sanar da shi halin da ake ciki.

Katse wayar yayi ya kira Yaseer ya sanar mishi don tun ɗazu ya gagara haƙuri sai da ya kira Mahaifin Safina ko an kira shi a kan wani abu da ya shafe ta yace A'a.

"Nagode Yallaɓai, bari naje na ɗauko ta" cewar Yaseer cikin damuwa yana juyawa zai bar office ɗin da shigowar shi cikin ta kenan don sai yanzu meeting ɗin su ya ƙare.

"Da kanka kuma? A'a ka bari dai ni na ɗauko su in kawo su nan gida, Ba zan bari ta tafi ba ma sai ta dawo dai-dai"

Har yanzu bai shirya fuskantar Reina ba, ba yanzu ba, da sauran lokaci .
Don haka ya ja dogon numfashi kawai "toh Nagode, idan ana buƙatar wani abu dan Allah ku kira ni"

Daddyn Safina ya amsa da "za'a yi mata komai kada ka damu"

Ya kira Safina yace mata gashi nan zuwa da kan shi.
Zaman jiran shi da suka yi kafin ya iso sai da kukan Reina ya saka tayi amai sau biyu zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Don haka suna barin makarantar basu tsaya a ko ina ba sai asibiti.

Aka yi mata allurori aka basu magani suka koma gidan su Safina a can ta wuni barci, kuma har la'asar ta doso kai Hajiya Hauwa bata nemi yanda take ba sanin yau jarabawa ɗaya suke da ita, tun sha ɗaya ko sha biyu na safiya ya kamata ace Reina tana gida.

Sai da aka kira la'asar maman Safina ta ɗaga ta lokacin zazzaɓin ya sauƙa ta bata abinci da magani sannan tayi wanka, Safina ta duba mata kaya, da ƙyar aka samu wani dogon rigan da yake ja mata ƙasa Reina ta saka yayi mata daidai sai dai kuma yawo take yi a ciki don Safina a yanzu ta fita jiki. Ta saka rigan tayi Sallah, ta zauna tayi jigum lokacin da wayan ta dake saman gado ya ɗauki ruri.

Da sauri ta miƙe ta nufi wayar domin masu kiranta ƙayyadaddu ne, kuma wannan kiran tun safiya take tsammanin shi.

Zama tayi a bakin gadon tayi picking ta ƙara a kunne.

"Hafsa na" ya kira ta cikin tausasshiyar murya. Sai taji kukan na niman dawo mata, ta garara amsawa shima ya bari wasu ƴan sakwanni suka shuɗe kafin ya ƙara cewa "kuka kika yi ko? Kina son in haƙura da tafiyar ne kawai in dawo muyi aurenmu mu zauna?"

"Ni ban yi kuka ba" ta faɗa a shagwaɓe tana rau-rau da idanu kaman yana gaban ta.

Ta rasa iyayen ta, ta rasa Yaseer duk da ƙananun shekaru lokacin bata san menene rashi ba, sai a yanzu gurguwar zuciyar ta ke daɗa nakasuwa da kewa da kuma tsoron rabuwa.

Gani take yi kaman da gayya lokaci ke raba ta da masoyan ta a lokacin da tafi buƙatar su. Yanzu idan Uncle Bilal ya tafi bai sake dawowa ba kuma shikkenan ta rasa shi? ko kuma ya makara a hanyar shi ta dawowar?. Shikkenan kuma bayan shi sai waye zata sake rasawa? Maama? Ummi? Ko kuma Safina?.

"Doll" Uncle B ya kira ta da sunan da ya raɗa mata a lokacin.
"Zan dawo doll, kuma mutuwa ne kaɗai zai raba ni dake" babu makawa abinda ke cikin zuciyarta ya karanta.

~~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

57

~~~~~~~~~~
_Too afraid to step outside_
_paranoid and petrified of what you've heard_
~~~~~~~~~~

Zamewa tayi ta kwanta a gadon jin kalaman shi sun fara narka ta.

Bata ce komai ba yaci gaba da faɗin. "Duk abinda za'a yi, duk abinda za'a ce ke tawa ce doll. Don haka ki kwantar da hankali kin ji? Ina son ki."

Hawaye ne ya gangara daga idanun ta, amma wannan karon na daɗi ne, "zaka dinga kira na kullum ina?"

"Nayi alƙawari. Idan na samu lokaci kafin na tafi ma zan dawo muyi sallama amma ban san haka process ɗin abun yake da wahala ba, tun isowa ta sai yanzu na samu kaina shiyasa ban kira ba tun ɗazu."

Share hawayen tayi da bayan hannun ta "Babu komai, Allah ya dawo da kai lafiya, ya bada sa'ar Abinda aka je nima"

"Ameen my Doll. And please ki rage yawan kuka kin ji? Ba zan samu nutsuwa ba idan ina jin ki haka, ko jarirai basu kai ki yawan kuka ba."

Ƙara turo baki tayi "Toh kai baka da labarin ko da nake jaririya nawa kukan na daban ne? Aunty na ko barci bata iyawa Saboda kuka na, wataran sai daddy na ya ɗauke ni mun bar ɗakin."

Uncle B ya murmusa "ba zan yi mamaki ba, amma ke a ina kika samu wannan labari?"

"A diary ɗin Aunty" nan ta shiga karanto mishi layi bayan layi na labarin yarintar ta daga hoton da ta adana a ƙwaƙwalwar ta, Uncle B yana sauraron ta yana ƙara mata ƙaimi, sai gashi Reina mai kuka sautin dariyar ta har parlo.

"Ashe rigimammiya ce doll ɗina"

Dariya tayi zata sake magana ƙofar ya buɗe Safina ta shigo. Ganin yanda Reina ke cikin farin ciki itama ta washe baki ta ƙarasa gaban gadon ta tsuguna ta saka tagumi tana kare mata kallo yanda take zuba taɓara.

"Uhmm ga wata mai gulma ta tsare ni da idanu" Reina ta murguɗa ma Safina baki.

"Zaheera ko? Kice ta bar ɗakin nan kafin na ƙirga uku"

"Ba ita bace. best friend ɗina ne wannan ina gidan su ne, amma ta cika gulma."

Wani abu Uncle B ya faɗa Reina ta cire wayar a kunnenta ta ƙara a kunnen Safina.
"Best friend" Uncle B ya ambata kasancewar bai kiyaye sunanta ba.

"Ina wuni" ta gaida shi cikin rasa abin cewa.

"Lafiya ƙalau, yaya school"

Ta amsa da "Alhamdulillah"

yaci gaba da cewa. "Ga amanar Doll ɗina please, ki taya ni kula da ita, tana cin abinci da yawa kuma a kan lokaci"
Chapter 22 · 0% Book details