← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 117

Sashe 78

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ciza haƙwaranta tayi cikin ɓacin rai dake taso mata tace "Idan ka kuskura wani abu ya same shi Wallahi nima sai inda ƙarfi na ya ƙare a kan ka. Try me and see please" ta ja ƙofar zata rufe ya saka hannu ya riƙe.

"A maimakon ki ƙarar da ƙarfin kuma ki tashi a tutan babu ba gwamma ki taimake ni muyi komai cikin sauƙi ba? Ko baki mafarkin ganin shi a tare da ke babu Reina a tsakanin ku? Ki je kiyi tunani amma kada ki bari kan ki yayi murfi kin ji?" Ya tura mata ƙofar ya rufe sannan ya koma nashi motar ya ja ya barta a wurin.

~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

96

Yau ta kama Ranar graduation ɗin su Maama. An shirya mata abubuwa sosai daga gidan su Yaseer sannan duka mutanen gidan ne zasu je mata har da Abbah. Sai da suka biyo gidan Ummi wanda suma suka yi nasu shirin sosai kaman yanda akayi ma Reina daga nan sai su ɗunguma baki ɗaya.

Umma da iyalanta suka fara shiga suka gaida Ummi da Baba Sannan suka fito gaba ɗaya.
Motoci huɗu ne a wurin, ɗaya na Yaseer ɗaya na Abbah ɗaya na Suhail sai na yayan Fauziyya, gashi tafiyar har da su aunty Zeenat, don haka aka ce ƴan mazan su haɗu a motan Suhail, Ummi da Aunty Aina zasu shiga motar yayan su, Aunty Zeenat ita kaɗai ta zo bayan motan Abbah tunda ɓangare ɗaya akwai gift ɗin da za'a kai ma Maaman, Aunty Sajida da Reina kuma su Je motan Yaseer.

Har ta buɗe gidan baya zata shige Aunty Sajida da tazo ta finciko ta tare da watsa mata harara "wa kike so ya zauna miki da angon ki? Ni da nake a matsayin goggon shi?." Ta shige ta jawo ƙofar ta rufe ta barta a wurin.

Bata da zaɓin da ya wuce ta ja ƙafafuwanta ta buɗe gidan gaba ta shiga. Shikuwa bai ce mata komai ba ya gaida Aunty Sajida ta amsa tana tsokanan shi ango-ango yayi ƴar murmushi ya kunna motar suka fara tafiya a bayan sauran motocin.

"Reina baki iya gaisuwa ba ko?" Aunty Sajida ta tambaye ta ganin bata da niyyan gaida yaseer.

Ta juya ta kalle shi lokacin da shima ya juyo. Shi ya fara mayar da idanun shi kan titi lokacin da muryar ta ya shiga kunnen shi.
"Ina kwana yaya Yaseer"

Kai tsaye ya amsa da "Lafiya ƙalau Umry, kina lafiya?"

Tayi saurin juyawa ta kalli Aunty Sajida ko taji sunan da ya kira ta dashi, murmushin da take yi kaman yaro ya ga alawa ya tabbatar mata kunnuwan ta yana gare su. Sai ta ɗaga mata gira tare da jinjina kai irin sunan yayi ɗinnan.

Ta gyara zama tana zumɓure-zumɓuren baki. Ita ba kunyar aunty Sajida take ji ba amma yanzu ta san zasu saka ta a gaba da tsokana don sai ta yayata sunan nan kowa ya ji.
.
.
Kaman lokacin da aka yi nasu itama Maama haka tazo aka dinga ɗaukan hotuna sannan kowa ya bata kyautar shi.
Duk miskilanci irin na Maama da ƙyar suka iya hana ta kuka suna faɗa mata idan ta ɓare baki zata yi muni a sauran hotunan. Don haka da ƙwallar da ya cika mata idanu Reina ta dafa ta za'a ɗauke su amma da mamakin ta sai Maaman ta riƙo ta jikinta da kyau ta saki wadataccen murmushi aka ɗauke su na farko idanun Reinan a kanta.

Da za'a ɗauki na biyu itama sai ta riƙe ta da kyau suka yiwa juna side hug da ƙayataccen murmushi a kan fuskar su. Yaseer ma ya ciro wayan shi ya saita su bayan mai camera aka ɗauki hoton da zasu yi alfaharin kasancewar shi har jikoki don tarihi ne mai daɗin gani. Ummi sai da ta shari ƙwalla da ta gan su a haka, domin a gaban ta suka dinga zaman doya da manja kuma babu yanda ta iya, amma gashi yau Allah ya haɗa mata kan su alhamdulillah.

"A'a Maama kuna ta nan ashe"

wata mata tayi Magana daga gefe sai suka samu kansu da juyawa gare ta dukkan su,
Hajiya Farida ce.

Kallo daya suka yi mata suka watsar da shirgin ta suka cigaba da abinda ke gaban su.

Tayi dariyar ƙarfin hali tana cewa "Ummi ina kwana, yara sun yi abin arziƙi Allah ya albarkaci ilimin su"

Ummi ta amsa da "Ameen" kawai.

Abun bai yi mata ta tafi ba ta ja taci gaba da tsayuwa, sai can jimawa har sun manta da halittarta cike da ƙarfin hali ta karaso ta riƙo hannun Maama tana cewa.

"Maama muje ku ɗauka da ɗan uwan ki mana. Kinga sai a ajiye tarihi, ai hoto tarihi ne"

Hannun da ta riƙo din Umma ta fauce sannan ta dubi Hajiya Farida tace "mu iyayen ta bamu gama ba tukunna, idan ya matsu shi ya zo"

Ta saki dariyan da babu karsashi a ciki tana kallon idanun Saudat. Saudat dai wanda aka bawa kwancen ankon sunan Reina, yau zanin jikin Saudat tayi imani yafi na jikinta tsada tunda tana sayar da su ta san kuɗin su.
"Toh ai ba matsala bane bari a kirawo shi, nan ɗin ma yafi kyan ɗaukan hoton ai. Harda su yaya luba ma da yaya Jummai duk bari su zo a ɗauke su tarihi da ƴar su.

Da faɗar haka tayi gaba tana godiya ma Allah da Hajiya Hauwa bata zo ba, domin da ƙyar ta iya jure kallon Yaseer a jikinta tayi kaman bata jin ƙunan su. Amma ita idan zata samu shiga jikin su fa ko yayane a shirye take ta zubar da ƴan uwanta ta koma side ɗin su.
Daman ita wurin da ba zata ribanta bane bata zama, amma da ta san riƙon Reina haka zai zo da alkhairi da bata gudu daga meeting ɗinnan ba ta amshi duka yaran ta riƙe da yanzu ita ce a cikin alkhairin da su Saudat ke ciki don tayi imani Tahir ne ya jiƙa su Saboda ƴar shi.

Babu musu suma sauran suka biyo ta har da junior dake sanye da graduation gown irin na Maama.

Babu ƙosawa suka jira su suka gama kafin suka ƙarasa inda Maama take, zata bar musu wurin Ummi tayi mata ido dole ta tsaya aka ɗauka amma ta haɗe gabas da yamma kudu da arewa kuma ana ɗaukan guda ɗaya ta matsa.

"Allah sarki Saudatu yaya bayan rabo?" Hajiya Lubabatu da tafi kowa rashin kunya ne ta miƙo ma Umma wannan gaisuwan, Amma dake bata yi tsammanin samun amsa ba sai ta juya wurin Abbah shima ta gaida Kamalun Jama'are mai fiɗan shanu a bikin ƴar ta.

Sauran ma suka samu ƙofa suka shiga gaisuwan da ba kowanne suke samun amsa ba sai dariyan yaƙe da suke faman yi. Aka ci Sa'a dai duk cikin su babu wanda yayi gigin cewa yaseer wani abu, Suhail sai faman jero ƙananun tsaki yake tunda bayi da daman magana. Ana haka har Abbah ya je cikin mota ya ɗebo IV ɗin da aka buga su a jiya suka shiga hannun shi da sassafen nan babu ma wanda ya bayar ma tukunna.

"Toh gashi kun sauƙaƙa mana aiki tunda yanzu ba lokaci gare ni sosai ba kada in manta ban kai muku da wuri ba"

Yace yana miƙa ma Hajiya Lubabatu katin.

Karɓa tayi da murmushi a fuskar ta ganin har da gayyata suka samu.

"Masha Allah. Yaseer ne zai yi aure?" Ta tambaya lokacin da Hajiya Farida da Hajiya Jummai har da junior suka zari katin ɗaɗɗaya daga hannun Hajiya Lubabatu suna dubawa.

Kafin su fahimci abinda suke gani Abbah ya ɗaura da "Eh, kuma ƴata Hafsatu zai aura in sha Allah, nan da sati mai zuwa"

Katin hannun Hajiya Lubabatu suka zube a ƙasa sauran kuma ƙandarewa suka yi yayin da junior ya lailayo wata ashar.

"Reina aure zaki yi? Bura uban can Lallai Jamal zai ƙara haukacewa akan wanda ya riga yayi"

Lokaci ɗaya bugun zuciyar ta ya ƙara gudu ta fara jan dogayen numfashi don har gobe bata san jin ko sunan shi. Ta juya kawai ta koma jikin motar Yaseer da suka zo ta buɗe gaban ta shiga tana mayar da numfashi. Ganin haka sauran ma suka ƙarkare taron suka yi ma Maama Sallama zasu koma ganin idan ta zauna babu abinda zata yi ta yanke shawarar bin su itama.

niƙi-niƙin gift ɗinta aka mayar bayan motan Abbah, ta dawo motan Yaseer tunda shine akwai space ga kuma halin da ƴar uwarta take niman shiga.

A kan idon su Hajiya Jummai suka ja motocin su suka bar su da ƙura.

Cike da damuwa Maama ta saƙalo kanta ta tsakanin kujeran Reina da Yaseer ta dafa ta ganin yanda ta koma sukuku lokaci ɗaya.

"Reina are you okay?" Ta tambayi abinda yake damun ta a karo na farko cikin kulawa amma sai jin muryar Yaseer tayi yana tambayar ta "sa'ar ki ce ita?"

Maama ta taɓe baki. Ba yanzu ta samu mai karɓa mata faɗa ba?! Sai ta gyara da "Aunty Reina nace kina Lafiya?"

Reina ta riƙo hannun Maama dake ƙafaɗan ta, ta ɗan matsa tana mata murmushi, sai take ji kaman ta goya ta wallahi, Lallai ɗan uwa yana da daɗi.

.....
"Gaskiya na daɗe ban ji abun al'ajabin da ya girgiza ni irin wannan ba. Wai Tahir ne zai yi auren ƴa, har sauran sati amma babu wanda ya sani a cikin mu? Toh su waye suka karbi auren? Tunda ni dai ba da izini na ba ko shi da kan shi zai yi ma ƴar shi waliyyi don kawai ya tozarta mu?"

"Uhmm yaya Kalabu da ka je ka same shi ne kayi masa wannan tambayoyin tunda ni ba amsoshin su gare ni ba. Ina nan ina fama da Shari'a na biliyoyin kuɗi ina ruwa na da wani aure? Ni me ya saka ma zaku kawo mun wannan hiran gida na tunda ni ban tara ku ba?"
Chapter 78 · 0% Book details