Sashe 85
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya yaye mata gyalen kanta ya ajiye a saman kujera ɗaya kana ya riƙe hannunta suka koma cikin ɗakin da ta fito, yayi hanyar ban ɗaki da ita.
"Ka jira ni zan yi in fito" ya tsaya ya bata dama ta shiga ta rufo ƙofar.
Kafin ta dawo ya shimfiɗa musu darduma guda biyu ya ajiye mata hijabi a saman na bayan amma tana fitowa kuma ta samu bayi ɗakin.
Bata daɗe ba sai gashi ya dawo, Ya cire babban rigan da hulan kan shi fuskar shi da hannun shi da ruwa.
Bai tsaya ɓata lokaci ba ya jasu nafila sannan yayi mata addu'ar da addini ya tanadar. Kana ya ɗaga hannu sama cikin roƙo "Ya Allah," yace da murya mai nauyi, “Ka sanya ma wannan auren albarka. Ka sanya soyayya da fahimta tsakanina da ita. Ka tsare mu daga dukkan sharri na zuciya da duniya da abinda ke cikinta. Amin."
Ta amsa da "Ameen" Idanunta suna cika da hawaye, ta sunkuyar da kanta.
hannunsa ya saka ya riƙo nata.
“Daga yau,” yace cikin natsuwa, "kin zama amana a hannuna, Hafsatu. Zan kare ki, zan girmama ki, zan so ki saboda Allah." Sannan Ya ranƙwafo yana riƙo kanta da daya hannun shi ya manna mata sumba a goshi, sanyin shi ya saka ta lumshe ido babu shiri.
Bata buɗe su ba har saida taji yana faɗin "muje mu ci abinci ko? Ko in kawo mana nan?"
Kada ya fahimci yanda ya kashe mata guiwa yasa tayi ƙokarin mikewa tsaye tana amsawa da "muje"
"No ki zauna ina zuwa" yace yana fita daga ɗakin bayan ƴan mintuna ya dawo ɗauke tray da ya ajiye duk Abinda zasu buƙata. Shi ya ciyar da ita da hannun shi duk yanda taso noƙewa, harda barazanar idan bata buɗe baki ba zai mata ɗure.
Ya mayar da komai yanda ya dace bayan sun gama sannan ya ciro mata kayan barci wai ta shiga ta wanke baki ta saka ta fito su tafi.
"Ina?" Ta tambaya tana duba kayan barcin da ya zaɓo mata, babu laifi wadataccen riga da wando ne har ƙasa.
"Ɗakin kwanan mu, ko a nan kike so mu kwana?"
A dirirce tace "Amma...amma na ɗau sallama zamu yi ka tafi ni in kwanta a nan?"
"Mene kika ce Mrs Yaseer? Ai ko saɓani muka samu which is inevitable amma Allah ya kiyaye babu raba ɗakin kwana. Idan kika ga kin kwana ke kaɗai to bani kusa ne but we'll always be sharing the same bed. Hmm?"
Bata da karsashin dogon magana don haka ta shiga ban ɗakin yana jiranta har ta fito sanye da pyjamas ɗin da kuma hijabin da tayi sallah a wuyan ta.
"Zo nan" ya yafato ta da hannu ganin ta nemi wuri ta tsaya kamar mai niman shiga aikin uniform. A hankali ta tako zuwa inda yake zaune a bakin gadon, kaman yanda tayi tsammani kuwa saka hannu yayi ya cire mata hijabin ya ajiye a gefe amma abu na biyu da yayi Wanda bata yi tsammani ba shine yunƙurawa ya rabata da ƙasa ya sunkuce ta kaman jaririya sabon haihuwa ya zaga gefen gadon ya shimfida ta ya rufa mata duvet. Kana ya fita daga ɗakin ya koma ɗakin shi ya watsa ruwa ya sauya kaya zuwa na barci shima ya ƙarasa rufe ko ina da kashe komai sannan ya dawo ɗaki a zaton shi zuwa yanzu tayi barci.
Ya yunƙura zai kashe musu wutan ɗakin sai gashi ta miƙe zaune tsugul.
"Ka bari sai nayi barci don Allah kafin ka kashe"
Bata rufe bakin ta ba duhu ya lulluɓe rabin ɗakin sai ɓangaren gadon da bedside lamp ya haska shi.
"Idan kin yi barcin sai in kashe wannan" yace yana komowa jikin gadon ta ɗaya ɓagaren ya zauna yayi addu'a sannan ya miƙa mata hannu.
Kallon hannun ta fara yi na wani lokaci kana ta saka nata a ciki ya jawo ta ta afko a kanshi baki ɗaya. Ya gyara mata kwanciya a jikin shi ya rufa musu duvet. "Good night my queen" yace a ƙasan numfashi sannan ya lumshe idanun shi.
~~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
100
_Menene uzurin ki da ba zaki kasance cikin ƙamshi ba a koda yaushe? Rashin samun ingantattun turaruka ne ko kuma masifar tsadan su ke hana ki siya? Idan na kawo miki maslaha zaki gyara? To kizo ga Bakhoor by Seemah zata kawo muku haɗaɗɗun turaruka all the way from Maiduguri and at Fair prices._
_Ko sana'ar turaren wuta kike son farawa baki iya ba ko baki da lokaci? Toh Bakhoor by Seemah suna bada sari naki kawai siyan containers ki zuba idan hakan ma yayi miki wahala zasu iya packaging miki tsaff naki kawai kiyi sticker ki manna._
We have all the varieties of turaren wuta you'd like ranging from;
*Sandal chips*
*Sandal bange*
*Sandal flakes*
*Sandal balls*
*Kajiji*
*Hawi*
*Halut*
*Bayan Halut*
*Gabgab*
*Farce*
*Cotton*
*Dorot*
A ɓangaren turaren jiki akwai Kalolin *Black khumrah*
*White khumrah*
*Dufr khumrah*
*Oil perfumes*
*Kabbasa spray*
*Original and cream Kulecham*
Akwai kuma *wardrobe balls* ma kaya.
Muna da bridal packages *_bronze, silver, gold da diamond_* and it's customizable.
Za'a tsuma muku turaren amarya idan biki sauran wata biyu ko sama da haka.
Ku dai ku tuntuɓe ta a kan lambar waya 08021689184 domin ƙarin bayani.
~~~~~~~~~~~
Ita duniya daɗinta duk abinda yake da farko a cikinta toh yana da karshe, duk wani shiri da hidima an yi an gama yanzu ya rage a bi amarya da ango da addu'a, wanda suka sha ɗawainiya su kwanta su huta gajiya, wa'inda kuma suke da shiri na daban a kan su kwaɓen su ya riga da yayi ruwa jagab kuma a bar su da jinyar zuciya.
Kaman da wasa general ya saka aka kai mishi Uncle B Kaduna aka rufe shi ya kwana ɗaya, biyu har saida aka kai Reina ɗakinta kafin ya saka aka sake shi. ita wanda ake bidirin a kanta ma bata san ana yi ba, tana can kwance a jikin angonta tana huta gajiyan biki.
Ana zancen gajiyar biki, Aicha mai fama da gajiyar zuciya da ciwon da take mata a wannan daren, da kuma na ƙwakwala mai faman harsaso mata yanayin da ma'auratan zasu kasance a ciki. Hawayen ta sun jiƙe matashin kanta, barci ya ƙaurace ma idanunta, danasanin amincewa da tayi Yaseer ya fara auren Reina take yi, da ta san lissafi zai ƙwace mata haka da ta matsa ya aure su a tare kawai amma yanzu idan ta shiga gidan daga baya mutane cewa zasu yi ita ta shiga gidan Reina bayan kuma ita ta ƙwace mata shi kowa ya sani.
Kaman yanda ta kwana bata rintsa ba haka ma'auratan suka kwana suna shaƙar barcin su hankali kwance. Domin tun Reina tana tsammanin wani abun Yaseer zai yi mata har barci yayi awon gaba da ita tana sauraron bugun zuciya da saukar numfashin shi.
Haske da ya fara shiga idanun yaseer ya saka shi buɗe su, da mamaki yake kallon labulayen windown ɗakin, dake basu da nauyi da duhu kaman na ɗakin shi sai suka bada dama ma hasken rana da ya fito a sararin samaniya ya ratso ta cikin su.
Yau shine ya makara Sallan asuba? Lallai kam.
Mayar da duban shi kan Reina dake kwance a ƙirjin shi yayi ya saki murmushi ganin yanda ta tukuikuye shi. Bai so ɗaga ta ba domin daga gani tana jin daɗin barcin ta amma duk suna buƙatar su yi sallar asuba in yaso sai ta koma tayi mai isar ta idan sun idar.
"Umry..." Ya kira a sannu yana shafa gefen fuskar ta. "Ki tashi muyi Sallah ko?"
Ta buɗe ido a hankali ta kalli fuskar shi na ƴan sakwanni kafin tayi saurin miƙewa daga jikin shi tana dudduba jikinta, shima tashi zaune yayi yana kallon yanda take dube-dube sai ya miƙo mata beanie ɗinta da ya zame daga kanta. Ta taɓa gashin kanta da ya sha gyara ya kwanta luff ɗan jelar shi na tufke cikin ribbon, ta karɓi hulan ta mayar ta rufe shi. "Ina kwana yaya Yaseer" ta miƙo mishi gaisuwa don ya tsura mata idanu ne ita kuma ta gagara kallon shi.
Ya sauƙe numfashi. "Mu fara gaida Allah ko wifey?"
Ta gyaɗa kai sannan ya sauƙa daga gadon ya riƙo hannunta ta sauƙo itama, ya rakata har ƙofar banɗaki ta shiga ta fara wanke baki sannan tayi alwala ta fito.
Shi ya jasu suka gabatar da sallan asuba, bayan sun idar ya juyo ya dube ta. "Umry ina kwana."
"Ina kwana" tayi saurin amshe gaisuwan tana sauƙe idanunta a ƙasa, kunyar yanda ta gama shige masa jiki yana daɗa lulluɓe ta, yanzu da wani ido yake kallonta?.
Tana kan saƙar zucin ta sai ji tayi ya jawo ta da ita da darduman da take kai zuwa gaban shi, ya sunkuyo daidai fuskarta suka kalli juna cikin ido sannan ya sauƙe idanun shi a kan lips ɗinta ta ya manna mata peck a wurin "my good morning kiss tunda an hana ni na good night "
tayi saurin kai hannun tana taɓa laɓɓen bakinta kaman wanda ya ɗauki wani abu daga wurin.
"Kace da wasa kake ai"
"Ni? Da yaushe?" Ta kaikaita kai tana kallon shi kawai.
"Ranan dinner a mota?" Idan ma da gaske mantawar yayi to ta tuna mishi.
Ya ɗan yamutsa fuska"Gaskiya I can't remember, Kinga yau kin saka mun makara Sallah"
"Ni kuma?" Ta fahimci so yake yi ya kawar da zancen farko.
"Yes, da baki nan sai dai in jira lokacin Sallah ba dai ta wuce min ba, amma daga zuwan ki kinga mune har karfe 7"
Ɗan turo baki tayi "shiyasa nace mu kwana daban-daban ai, da ko baka tashi ba ni sai in je in ɗaga ka"
"Idan muna tare hakan ba zai fi daɗi ba? Ko dan kin samu pillown da baki da irin shi da?" Ya ɗaga mata gira ɗaya.
Kallon mamaki ta bishi da shi baki buɗe. "Kai ma ba kace Insomnia kake da shi ba? Kaima ai ka samu wannan ne..matan da baka da irinta da" ta ƙareshe tana matse baki saboda yanda kunya ya sanya maganan ta ya fito da gargada.
"Ai ban musa miki ba dama. Hakan ne"