Sashe 20
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana tafe tana kuka wiwi ba ko kunyar ɓoyewa ta fita daga gidan a kan idon shi.
Sai ya ɗauke kai don bayi son ganin kukan ta, yaci gaba da danne-danne a MacBook Air ɗin shi amma zuciyar shi yaƙi take yi dashi ya ɗago ya kalle ta koma yaje ya rarrashe ta.
"Yanzu kaji daɗi da ka raba ta dashi?" Cewar Muhammad dake zaune a mazaunin driver yana kallon Yaseer dake seat ɗin baya ta cikin mirror.
~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
55
*******
Knocking tayi sau biyu a ƙofar ɗakin ta jira ko za'a buɗe, jin shiru yasa ta murɗa handle ɗin tare da kutsa kai ciki tana kiran sunan shi.
Daga farko duhu kawai take gani saboda ta fito daga cikin haske, cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka daidaita da ƙarancin hasken dake ɗakin wanda ke shigowa ta cikin labulen da suke a sauƙe, alamun rana ta cika da hasken ta a waje amma gashi nan naɗe a saman gado.
"Yayan mu" Aicha ta kira tana ƙarasawa jikin gadon.
Bai amsa ba bai ma san tana yi ba, shaƙar baccin shi yake yi hankali kwance, ya rufe daga ƙafar shi zuwa ƙirjin shi da duvet, amma ya ƙure gudun AC na ɗakin.
Hakan ya bata daman ƙarasawa kusa da pillown shi tana ƙarewa kyakkyawar fuskar shi kallo tana jin kaman ta ƙarasa ta shafa kwantaccen sajen da ya ƙara ƙawata fuskar, ko itama ta shiga ƙasan duvet ɗin su cigaba da barci a tare.
Dogon numfashi ta ja ta ranƙawafa ta kunna bedside lamp idon ta ya sauƙa a kan goran sleeping pills da glass ɗin ruwa, ta ɗauki goran maganin ta buɗe taga saura kaɗan, yaushe ta karɓo amma har ya kusa shanyewa?
Wannan karon rai a ɓace tace "Yayan mu!"
"Hmm?" Ya amsa yana juyawa ta ɗaya ɓangaren kaman hakan ne zai saka ya daina jin muryar ta.
Ta jijjiga pillown da yake kwance a kai tana sake kiran shi.
Da ƙyar ya iya ƙyalla ido ya dube ta. "Darling Please..." Ba zallan kai ba, har tafin ƙafar ta saida taji dirin manganaɗisun muryar shi mai zurfi.
"Akwai aiki fa Yayan mu! Ka san ƙarfe nawa ne?"
"Ƙarfe nawa ne?" Ya tambaya cikin muryar barci.
"7:24, ƙarfe 8 da rabi muke da meeting but you're still in bed"
Sai ya ɗan ware rinannun idanun shi a kanta, a shirye take cikin wata doguwar riga ruwan ƙasa fuskar ta da ƙarancin kwalliya, ga signature ɗaurin ta wanda akewa taken Zahra buhari ya zauna daram a kanta, tana fitar da sanyayyen ƙamshin da wanda ke cikin dakin shi bai hana nata shiga hancin sa ba.
"30 more minutes Please darling. Idan na tashi minti talatin ya ishe ni in shirya mu tafi"
"No, ba zamu fita baka karya ba, haka jiya ma ka wuni da yunwa, so in dai skipping meals zaka dinga yi kai da lafiya kun yi hannun riga"
Numfashi ya sauƙe sanin duk yanda zai yi ba zata rabu da shi ba, ya tashi ya zauna da addu'a a bakin shi yana murtsuka ido ya ɗan yi hamma.
"Shikkenan, kije ina fitowa yanzu"
Ta jinjina kai "okay Ina jira" ta juya da nufin tafiya, sai kuma ta sake juyowa.
Idanu ya zuba mata na yaya aka yi ɗin nan.
"Yayan mu ka rage depending a kan maganin nan Please, idan ba haka ba shima ya kusa ya daina maka aiki sai an baka wanda yafi shi ƙarfi, kuma yana da illa ga lafiyar ka na san ka sani"
Daina aiki kuma na nawa. jiya tun farkon dare ya sha saboda ya samu hutu, kasancewar washegari monday tushen aiki yana da tabbacin ayyuka zasu taran musu dukda shi weekend ɗin ma babu wani bambanci a kan aikin yake wuni yana kwana. Amma sai da yayi doubling dosage na maganin sau biyu kafin ya samu ya rintsa bayan yayi sallar asuba, don haka jin kan shi yake yi yayi mishi wani dummm ga nauyi.
Yayi gyaran murya kana ya amsa da "Zan rage Umma Aysha"
Sai ta saki murmushi "yauwa, muna jiran ka a dining room" ta juya tana taku ɗaya bayan ɗaya, ba wai don ta ɗauki hankalin shi ba dukda tana da burin hakan sai don haka yanayin ta yake, tana yin komai, ma'ana komai cikin nutsuwa, aji da kuma kiyayewa.
Shima ita yabi da kallo a zahiri a baɗini kuma zugan tunani ne suka fara layin shiga kan shi.
Bayan kaman mintuna 20 kamshin shi ya fara shiga hancin su, kafin ya ƙaraso da sallama.
Abban shi ke zaune a head chair hankalin shi a jikin tablet ɗin da yake karanta news, ɗaya hannun shi kuma ɗauke da mug ɗin coffee mai tururi yana ɗan sipping a hankali.
Sai Suhail da Irfan daga gefen shi na hagu kowa hankalin shi a kan wayar hannun su.
Ya ƙarasa kusa da Kamal ya rage tsayin shi kana ya gaida shi. "Yayan mu har an fito?" Abbah Ya tambaya da fara'a a kan fuskar shi yana karantan gajiyan dake idanun Yaseer ɗin.
"Eh Abba, ina son mu ɗan kafa wasu projects ne a nan ɗin kafin mu koma yanda lokacin da zamu sake dawowa sun yi nisa"
"Toh Allah ya taimaka, ya bada Sa'a, ya shige muku gaba"
"Ameen ya rabbi. Ina Umma?" Ya tambaya yana ɗaukan hanyar kitchen domin ya san ba zata wuce can ba, ita dai tayi amanna da girki da kanta koda ba zata yi na yaran ba na Kamal dai sai dai idan bata jin daɗi.
Bai kai ga shiga kitchen ɗin ba ta fito rike da wani haɗaɗɗen food flask.
"Yayan mu ka tashi?" Ta tambaya hankalin ta a yanda zata kai ta ajiye flask ɗin, Yaseer ya ƙarasa da azama ya karɓe daga hannun ta.
Ya juyo wurin su Suhail cikin ɗaga murya yace "ku kuma zaman me kuke yi? Ita ce zata shirya table ɗin?!"
Bai rufe baki ba kowa ya dire waya suka wuce kitchen ɗin a guje.
"Umma idan kin gama kawai kina bari a kitchen ɗin dan Allah, ko masu aiki zasu fito miki da shi idan bamu nan" yace yanayin fuskar shi kaman zai fasa ihu domin da gaske bayi son ganin tana ɗawainiya komin kashin sa, idan ba haka ba kuma menene amfanin aikin da yake yi tuƙuru idan mahaifiyar shi ba zata huta ba?.
"Ni don miji na nake yi ba don su ba, ba don shima sammakon fita zai yi ba ka san da yanzu ina gado" ta amsa tana zama a kujeran da Yaseer ya ja mata, sannan shi da kan shi ya bude flask ɗin don ya fara zuba musu.
Aicha ne ta fara fitowa ɗauke da tray mai jug ɗin ruwa da glass cups sai spoons, forks da butter knife, ta ƙaraso tana jerawa a gefen plates da bowls ɗin da Sabir ya riga a ajiye a gaban mazaunin kowa tuntuni.
"Yayan mu ka bari zamu yi, kada ka ɓata adon ka" ta ɗaga ido ta dube shi aka yi Sa'a shima ya ɗago suka haɗa ido sai suka sakewa juna murmushi.
"Kina dai so ince kin yi kyau ne kuma ba zan faɗa ba"
Rolling eyes ɗinta tayi tace. "Nagode"
Ta karɓi flask ɗin hannun shi shima ya samu wuri ya zauna.
Lokacin da Sauran suka fito a jere, Sabir a gaba yana ɗauke da ƙaton bowl mai ɗauke da chicken and vegetables stir fry da ya gama haɗawa, Suhail na biye dashi da wasu food flask ɗin guda biyu, sai Irfan na ɗauke da tray ɗin mugs a hannu ɗaya ɗayan hannun ɗauke da flask ɗin tea. Duk suka sama ma kayan wurin zama saman wadataccen teburin.
Wayan shi Yaseer ya ciro ya shiga ɗan dubawa zuwa lokacin da za'a gama haɗa mishi abinci. Tarin notification ba baƙon sa bane amma yanda wayan take zut-zut duk bayan second ɗaya yasa yaji bari ya sauƙe public account ɗin shi na Instagram ya goge tiktok ma ya huta na kwana biyu.
Gani yayi followers ɗin shi har sun zarce dubu ɗari bakwai shida ya bari bai wuce dubu ɗari shida da hamsin ba last week.
Fara duba shafin yayi don ba shi yake managing da kan shi ba, bayi da wannan lokacin.
Last post da aka yi a shafin ya duba wanda shine hoton bikin da suka je a Abuja. Hoton yana da likes dubu ɗari biyu da, yayi sliding ya kalli sauran ma kafin ya dubi Aicha "Darling, page ɗina shine sharan ki? Abinda nake biyan ki kina mun kenan? Da hoton wani product kika saka ya samu miliyoyin views da likes haka da yanzu mun yi ciniki sosai"
Ta taɓe baki "toh aka ce maka idan shine zai samu hakan ne? Ai abun sai ana yi ana saɓa hannu saboda nishaɗin mabiya, amfanin marketing department kenan, amma kayi ta saka musu kayan kuɗi gundura zasu yi su daina dubawa daga ƙarshe a bar ka da kayan ka don basu gani ba ma balle su san da shi"
"Still hoto ɗaya ya isa tunda su mutane magulmata ne basu da aiki sai duba rayuwar wasu"
"Ai gashi ma harda masu fashin baƙi a kan hoton a tiktok, har sun saka muku Ranar aure ma baku sani ba" Suhail ya faɗa yana gimtse dariya tare da juya fuskar wayar shi ma Yaseer yanda wani ke faman shirga ƙarya, an rubuta 'save the date' da tutan Nigeria da na Niger a saman video ɗin.
"Ga wasu ma sun kai musu kayan aure" Sabir shima ya nuno yanda aka ɗauko tsohon video ɗin kawo lefen auren wata aka saka hoton Aicha a ƙasa harda waƙan Niger.
"Darling zaki auri Yayanmu?" Irfan ya tambaya yana washe baki don Allah ya gani yana son su tare, ba don ya tashi yaga iyayen Aicha ba ma da zai ce umman shi ne ta haife ta, yana jinta a jikin shi kaman yanda yake jin sauran ƴan uwan shi, iyayen shi ma haka sun ɗauke ta kamar ƴar cikin su, yana da tabbacin itama a nata ɓangaren haka ne.