← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 117

Sashe 96

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Reina kuwa kallo take ƙare mata cikin kaɗuwa da tashin hankali. Da farkon fari ma babu wanda zai yi mata kallo ɗaya yace musulma ce. Riga ne irin wanda take saka ma mijinta na sunnah idan suna su biyu a jikinta, gashin doki har ɗuwawu, ga faracu zuƙa-zuƙa masu jajayen fenti, kwalliyan fuskarta kaman mai zuwa Club ga fake lashes suma sun tsaya, tsayin takalmin ta ma bata san da mene zata kamanta shi ba domin idan itace ba zata iya takawa a cikin su ba sai dai ta gwalmaɗe ta faɗi.

Itama Zahra kallon Reina take yi cikin abayar ta har ƙasa da coffee brown flat shoe a ƙafar ta sai mayafin rigan da ya kasance shima coffee brown ta yane kanta dashi, hannunta riƙe da wani coffee brown mini bag mai hannun manyan pearls cream color, sannan fuskarta babu yawan kwalliya amma sai taga ta mata kyau da kwarjini ainun.

Bata rufe baki ba ƙofan ya sake buɗewa wani saurayi ya fito cikin leather jacket da bakaƙen gloves a hannun shi kunnen shi ɗaya da ɗan kunne mai suffan cross. Bai lura da Reina ba saida ya ɗaura ma Zahra da ta daskare a wurin hannu a kafaɗa yana faɗin "let's go and live the night baby"

Ganin bata motsa ba yabi inda take kallo da ido lokacin da Yaseer ya janye Reina suka cigaba da tafiya domin idan ya bari wannan ɗan iskan ya kalla mishi mata sai yayi ma Zahra Allah ya isa.

Elevator ya danna jiran minti ɗaya sai gashi nan ya iso ya buɗe, suka shiga sannan ya danna floor ɗin reception suka fara sauƙa.

"Ya Umry" ya kira yana juyo da ita ta fuskance shi ganin yanda ta koma kaman wanda ruwa ya cinye.

"Bae Zahran Umman Jamal ne" sunan Jamal ɗin ya suɓuto daga bakinta ba tare da ta ankara ba, amma ba shine ya saka ta take jin kamar ta zubar da ƙwalla ba, irin rayuwar da ta ga ƴar uwarta a ciki shine ya ɗaga mata hankali tunda a iya saninta ba'a yi ma Zahra aure ba kuma koma auren tayi ba tare da saninta ba babu mijin da zai ke irin wannan rayuwar da matar shi ta sunnah. Hakan na nufin cin amanar iyayenta take yi idan tazo Abuja da sunan makaranta?.

Tallafo fuskar ta yayi amma ta gagara sanya kwayan idanunta cikin nashi domin ta sani kuka ne zai ƙwace mata.
"Please kada ki bari wasu marasa muhimmanci su ɓata mana daren mu, kin yi masifan kyau nake faɗa miki kada ki yi kuka ki bata ɓata kwalliyan ki"

Ta jinjina kai tana kallon shi daga ƙarshe tana mayar da tunaninta a duniyar shi kawai koda zata sake mantawa da wasu gaba ɗaya a cikin rayuwar su.

Har irin hoton ma'aurata da ake ɗauka a jikin madubin elevator ta so ɗauka musu amma yanzu sai taji komai ma ya fita kanta.

Jikinta Sukuku suka ƙarasa mota, ita dai tana kwance a jikin ƙofa idanunta a sama tana bin farin wata da kallo har suka isa gaban makekeken restaurant ɗin wanda aka rubuta 'Marks at the park' a mashiganta.

Suka shiga hannun shi a kunkumin ta ƙafafuwan ta kawai ke takawa, aka yi guiding ɗin su har table ɗin da yayi reserving a rooftop.

Ja mata kujeran da ya bada baya wa mutane yayi ta zauna shima ya zauna a wanda yake kallon nata sannan ya kamo hannunta ya matsa a cikin nashi. "Umry Please. Relax. This was supposed to be a surprise amma ya lalace dole na sake sabon arrangement, amma dan Allah ki sake mu ci abinci cikin kwanciyar hankali at least"

Gyaɗa kai tayi tana ɗaukan menu ɗin domin ta zaɓi abinda zata ci dukda cewa ba gane sunayen abinda take karantawa take yi ba, cikin Sa'a akwai list na ingredients ɗin kowani abu a ƙasan shi sai dai idanunta suna sauƙa a kan farashin su ta zaro ido ta ware su a kan Yaseer.

Girgiza mata kai yayi idanun shi a kan menu ɗin hannun shi "don't look at the price"
Ya ɗaga hannu sai ga waiter ya ƙaraso don karban orders ɗin su.

"Me kike so?" Ya tambaye ta domin waiter ɗin ya fara ɗaukan orders ɗinta kafin nashi.

"I'll have shrimp gyoza" ta ji daɗin yanda ta furta sunan dai-dai saboda ta san shi a J-drama da anime da take kallo, ta fahimci kusan yawanci Japanese cuisine suke serving a wurin.

"That's a dessert what about main course?"

Ta duba kuɗaɗen main course ɗin ma tana sauƙe ajiyan zuciya kafin tace "salmon teriyaki. Thank you" gudun kada tayi ta tsayar da waiter ɗin.

Murmushi Yaseer yayi ya bada nashi orders ɗin yana ɗauka sannan yace ya ƙaro mata bresola salad, spicy seafood soup, gunkan scallop, egg fried rice sai mango smoothie" ya miƙa menus ɗin su duka biyu ma waiter ɗin gudun kada ta sake duba kuɗin abinda ya zaɓa.

"Ko kina son sashimi ne ya dawo?" Ya tambaya bayan waiter ya tafi ganin ta fara sakewa.

"Sashimi ba ɗanyen kifi ko nama bane?" Tace tana mishi kallon gefen ido, ya ɗauka irin bata sani ɗinnan bane.

Ɗage kafaɗa yayi "Na sani ko tunda kina kallon su kema zaki iya ci?"

Haka tana gani aka jere musu abubuwa kala-kala, ta saita camera ta dauka a hoto tunda bata san ranan da zasu sake dawowa ba sannan suka fara ci.

Ga sarari da iska mai sanyi dake busawa a hankali, ga dogayen gine-gine da hasken lantarki wanda kake iya hangowa daga wurin, da sararin samaniya wanda taurari da farin wata suka mata ado a saman kan su, sosai ta ji daɗin yanayin wurin ga kyan restaurant ɗin shi kan shi.

Wasu abubuwan sun yi mata daɗi wasu kuma ko sun riga da sun shiga bakinta sai ta fito da su ta naɗe a tissue. Basu bar wurin ba sai karfe ɗaya da kwata, kasalan ƙoshi da barci ya saka ta manta da zancen wata Zahra.

........
Washegari

*Aicha*

Har ta ƙaraso bata daina jin kaman ta juya ba, parking tayi a gaban mashigar estate ɗin wanda BOLD'S RESIDENCE yake rubuce da manyan baƙaƙe cikin rubutu kalan ruwan gold.

Zuge glass ɗin window ɗinta tayi Saboda security ɗin da ya ƙwanƙwasa shi domin ya samu daman mata magana.

"Hajiya wani unit kika zo?" Ya tambaya ba tare da sallama ko gaisuwa ba tunda ba abinda ke gaban shi ba kenan.

Ita ta san ma a wani Unit yake ne ko kuma a ina zata same shi?.

"Umm.. na zo ganin Mr Rafeeq ne"

Ya sake kallon ta da kyau yana son tambayar ta ko shi ya bata appointment tazo ta same shi har gida ko kuma? Amma yana tsoron ta kasance baƙuwar shin ne da gaske ya tsaya yake tuhumar ta.

"Yaya sunan ki Hajiya?"

Yana gidan kenan? Ta kaɗe!. ta ayyana a ranta.
A fili kuma ta amsa da "Aicha Abdou Hamissou" tana ciro business card ɗinta ta miƙa mishi.

Ya koma ɗan office ɗin su ya shigar da suna da numbern wayanta da ma numbern motar ta a computer kafin ya danna kiran intercom na gidan ya sanar da wanda ta ɗauka zuwan Aicha. Saida ya jira aka sanar da mai Unit ɗin kafin ta bada izinin ta shigo.

Har ta fara murnan komawan da zata yi ta cewa Yaseer bata samu ganin shi ba ya hakura ya sake shigewa gaba a lamarin ya lallaɓa shi da kan shi amma sai gani tayi gate sun wangale a gabanta.

Kuka ne kawai bata yi ba, da sanyin guiwa ta tada motar ta shiga bayan sun sanar da ita Numbern unit ɗin da zata nufa.

Saida tayi tafiya mai ɗan nisa dukda a mota ne kafin ta iso Unit ɗin. Tayi parking ta fito tana ƙarewa estate ɗin kallo ya haɗu ya tsaru, gashi ko ina shiru sai dogayen bishiyoyi da kyawawan gininnuka, tana kuma mamakin wai family ɗaya ne suke rayuwa a nan, abun sai yaso burge ta.

Doorbell ɗin gidan ta danna tana gyara zaman mayafin da ta yafa a kafaɗa da kuma jakan da ta saƙala.

Babu ɓata lokaci ƙofar ta buɗe, taci karo da wasu kyawawan mata guda biyu suka tsareta da idanuwa.

"Umm... Ina kwana, na zo wurin Mr Rafeeq ne please"

Sai matan suka saki murmushi a tare, ƙaraman cikin su harda zuwa ta rungume ta. Sannan suka jata ciki ba tare da sun bari tayi bayanin kanta ba ma.

Suka shiga har tsakiyan babban parlon yanda ta hango masu aiki cikin uniform ɗinsu suna ta zirga-zirgan shirya breakfast a saman dining sai su tsaya su gaida ta kafin suci gaba da aikin su. Tunawa tayi itama ko karyawa bata yi ba ta bugo sammako a bisa umarnin Yaseer.

Ƙaramar cikinsu tace "yi haƙuri bari na kawo miki ruwa" ta juya da ɗan hanzarinta ta ƙule ciki.

Babban ta jijjiga kai "Asal da abinta baki bawa mutum wurin zama ba kya tafi kawo masa ruwa ya sha a tsaye kenan? zauna ƴar uwa" tace tana nunawa Aicha kujera ta ƙarasa ta ɗofana ta ajiye jakar ta bisa cinyar ta domin matar shiga mata idanu take yi, sannan aka sake sabon gaisuwa. Sai kuma ta ja tayi shiru tunda ta riga da ta faɗa musu wanda tazo wurin shi idan dai ba ɓatan kai tayi ba kaman yanda tayi tsammani ta san idan ta jira zai fito. Amma a maimakon mai jini a jika sai wata tsohuwa ta gani ta fito tana dube-dube da wasu ƴammata biyu da yarinya ɗaya biye da ita.

"Ke Safnah! Ina Safnah?"

Matar dake zaune da Aicha ta miƙe ta tunkari tsohuwar tana faɗin "gani Jadda"

Tsohuwar da aka kira da Jadda ta riƙo hannun matar tana faɗin "ance nayi baƙuwar alheri da farar safiya, tana ina?"

Gwada mata Aicha dake zaune tayi tace "gata nan Jadda"

Sai Jadda ta washe baki tana tunkaro Aicha. Bata san mai ya kaita saman guiwar ta ba amma tana da yaƙinin cikin kunya, ruɗu, da kuma ganin girman shekarun Jadda akwai guda ɗaya.

"Ina kwana" Aicha ta gaida ta, a maimakon ta amsa sai ta ƙaraso ta riƙo ta zata zaunar.

"Zauna da kyau abinki ƴar nan, kaina a waye yake kin gani."
Chapter 96 · 0% Book details