← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 117

Sashe 59

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Tahir ya amshe da "Haramun, ba ni na sakaya shi ba ni yayi wa alfarma ya sakaya, da arziƙin shi nake ci nake sha da na ɗan shi kuma asirin yara na yake a rufe. Amma idan a kan kuɗin da ka ƙara ne ka ɗaura mun ko kuma yunƙurin kashe ni da kayi toh ka koma gida ka kwanta ka samu barci domin ban waiwayo ta kanka ba tukunna"

"Subhanallahi, yunƙurin kisa kuma?" Alhaji Kalabu dake ta tsare gida tun ɗazun wai shi babba ya juyo ya kalli Alhaji Salisu amma sai Alhaji Salisun ya watsa masa harara ganin tun ba'a je ko ina ba yana ƙoƙarin gwada bai san mai aka yi ba ya zare hannun shi a ciki ya bar shi a ciki shi kaɗai.

"Ku je gida ku sake shiri don yanzu sharan fage muka fara Amma ba zan bar ko ɗaya daga cikin hakkin Hafsatu da nawa hakkin ko na Yaseer da kuka ɗauka ba. Kaga Salisu abinda kake ji a yanzu saboda rufe ɗanka da muka saka aka yi? shi naji a nan lokacin da kuka rufe mun Hafsatu a kejin da har yau ta kasa fita" ya faɗa yana gwada saitin zuciyar shi. " domin ko sunan azzalumin ɗanka ta ji sai nutsuwa ta bar jikin ta. Ba zan taɓa yafe muku ba wallahi " daga haka ya kunna keken shi ya bar musu parlon, suma sauran suka watse tunda basu da abinda zasu ce musu, ba zasu ce ga lokacin da suka bar gidan ba ma, an dai jaddada ma security ko kusa da gidan suka sake ganinsu su kama su su kai police station a rufe su.

.....

*Bayan sati biyu*

Daga kan Alhaji Tahir, Alaji Abdou, Abbah, barrister har zuwa kan Yaseer ne zaune a parlon abban a Yau.

"Ba zan ɓoye muku ba ina tsoron al'amura su tafi ba a yanda muka tsara ba" lawyern da ya tsaya musu a kan case din masu kuɗin ruwa ke bayani. "Idan da zamu samu isasshen lokaci zamu warware komai a hankali, amma we need time kuma da alamun Shari'ar ta zo da zafi ba zamu samu yanda muke so ba. Tunda duk da Musulunci ya hana cin riba(Interest) ko yaya take amma dokar ƙasa bata haramta ba kuma da amincewarka ka karɓa..."

Alhaji Tahir ya duƙar da kan shi cikin jin nauyi da kunya. Kunyar mutane ƙalilan ma kenan, kunyar gidan duniya, ina ga an gangara filin ƙiyama ne ake mayar da son zuciyar shi a gaban Allah?.

".. Sai dai kai ka tabbatar ba abinda ka karɓa daga wurin su ba kenan kuma gashi mun tabbatar da saka hannun ka ne a jikin takardar da ka gabatar kuma kaima ka amince."

"Toh yanzu barrister menene abun yi?" Alaji Abdou ya tambaya saboda a bar zancen Alhaji Tahir tunda laifi ne ya riga yayi mafita suke nima.

Barrister Ya sauƙe numfashi "Toh, a gaskiya ba zan ɓoye muku ba the worst that could happen shine case ɗin nan zai iya Taɓa darajar YK & Co, idan ma bai ruguza ta ba kenan tunda kun ce shine mai alhakin rabin kamfanin"

Abbah yace "Amma ai da sunan yarinyar shi aka sayi shares na kamfanin ba nashi ba" shikkenan fafutukan Yaseer zai tashi a banza.

"Amma idan aka bi salsala shi ya mallaka mata, don haka kotu tana da ikon ƙwacewa. Sannan tunda matsayin ƴa take a wurin shi bashin mahaifin ta zai iya hawa kanta kaman yanda itama bashin ta zai iya hawa kan mahaifin ta."

"Toh idan tana da alaƙa mai karfi da mariƙin dunkiyan nata fa? Ya kasance mijinta guardian ɗinta?"

Idanun su duka suka bi Muryar Yaseer zuwa wurin da yake zaune saman carpet idanun shi a kan yatsun ƙafar shi.

Cikin jin daɗin samun mafita cikin sauƙi barrister yace "perfect, sai kuma mu koma kan wani problem ɗin daban don an yi solving wannan"

Bakin sa ya ɗan ciza yayi dogon ajiyan zuciya Sannan ya ɗago ya dube su "Zan Aure Ta!"

Alaji Abdou ne kawai ya iya furta "Whatt??" Amma Alhaji Tahir da Kamal kallon Yaseer suke yi kaman wanda ya fidda ƙaho a ka.

Sai da shock ɗin ya ɗan sake Alhaji Tahir sannan yace "Toh idan aka gama warware matsalan gabaki ɗayan ta fa? Yaya za'a yi da auren?"

Kai tsaye ba tare da gargada ko tangarɗan harshe ba Yaseer yace "zan cigaba da zama da ita, har abada in sha Allah"

~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

84

*Yaseer*

Da kyakkyawar fata ya shiga binciken Uncle B kaman yanda Abbah ya umarce shi a matsayin shi na babban wa a gareta.

Ko da ace bai auri Reina ba, ba zai yi mata fatan rayuwar auren da ba zata ji daɗin shi ba, idan kana son mutum dole ka so farin cikin shi, kaman haka yake son ta samu wanda zai mata so mai tsafta kuma ya ɗauke ta da daraja ta samu kwanciyar hankali da farin ciki a gidan shi.

Sai dai tun ba'a je ko ina ba ya samu bayanin da ya ruguje duk wasu shirin da yake da shi na tsananta bincike a kan Uncle B.

Yayi tunanin yanda Reina zata ji Saboda son da ya fahimci tana mishi, amma idan ana zancen rayuwar aure ba ta soyayya ake ba tunda ita ana iya sake ta, haka zata saka ma zuciyan ta haƙuri ta sami wanda ya dace da ita ta so shi.

Tun daga ranar da ya tunkare Reina da maganar ya gane ashe yanda yake ɗaukan Reina ba haka take ba, tunanin da yake tsammanin tana da shi a shekarun ta na yanzu bai riske ta ba tukunna.

Shi kuwa ba zai iya zuba mata idanu ta ɓata rayuwar ta ba balle ya bata goyon baya, idan tana cikin farin ciki da jin daɗi ko a ina take hankalin shi zai kwanta idan ba haka ba kuma sai dai ya ɗauki mataki a hannun shi.

"Zan Aure Ta!" Bakin sa ya bayyana hukuncin da zuciyar shi ta yanke don haka ya ɗan ciza ta yana mata gargaɗi kana ya sauƙe dogon ajiyan zuciya Sannan ya ɗago ya dube su.

Abinda yayi tsammanin shi ya gani a fuskokin su, wato tsananin mamaki da kaɗuwa sai dai ya riga da ya bayyana abinda yake cikin shi yanzu babu gudu ba ja da baya.

Cikin su Alaji Abdou ne kawai ya iya furta "Whatt??" Amma Alhaji Tahir da da Abbah kallon shi suke yi kaman wanda ya fidda ƙaho a ka.

Sai da shock ɗin ya ɗan sake Alhaji Tahir sannan yace "Toh idan aka gama warware matsalan gabaki ɗayan ta fa? Yaya za'a yi da auren?"

Toh shi ai ko ba Hafsatu Reina ya aura ba a cikin dictionary ɗin shi babu saki balle, Kai tsaye ba tare da gargada ko tangarɗan harshe ba yace "zan cigaba da zama da ita, har abada in sha Allah"

Kusan dukkan su suka ja numfashi a tare kafin aka samu Abbah ya iya buɗe baki ya sake jefo mishi tambayar "Kana son ta ne?"

Ƙasa yayi da kai ya ƙura ma persian carpet ɗin idanu kaman mai son gano wani abu a jiki.

A ɗan hasale Abbah ya sake tambayar "nace kana son ta ne?!"

"Eh Abbah" ya amsa da sanyin murya yana jin kaman an sauƙe mishi nauyi a kirji. Sai kuma dambaruwan da za'a yi kafin iyayen nashi da mahaifin Hafsatu su amshi baƙon lamarin.

Amma da mamakin sa sai ji yayi Abbah yace "Shikkenan"

Daga nan bai sake cewa komai ba kuma, aka sake rasa mai magana a cikin su, Alhaji Tahir yana tsoron yanke hukunci a kan lamarin da yake ganin bayi da iko a kai a yanzu, Amma indai Hafsatu Reina ce ya daɗe da bada ita halak malak ma wa'innan mutanen. Ba Yaseer ba ko wani daban Kamal ya kawo mata a matsayin abokin rayuwa bayi da ja a ka.
Amma kuma ace Yaseer ya auri Reina bayan duk abinda suka mishi an yi mishi adalci?

Shi kuwa Abbah a nashi ɓangaren komai ya daɗe da wucewa tunda daman asalin shi ba mai riƙo bane Amma bayi son ya nuna goyon bayan shi a kan lamarin su tilasta Alhaji Tahir yin abinda bai yi niyya ba don ya faranta musu ko kuma ita Reina ayi mata dole.

Fahimtar hakan ya saka Alaji Abdou ya shige musu gaba. "Sai ka nemi amincewar Yarinya idan kun daidaita tsakanin ku shikkenan Allah ya sanya alkhairi"

Taɓɗi ana dara ga dare yayi. Ga fa inda gizo yake saƙa, ta ina yanzu rana ɗaya zai sauya ma Reina fuska zuwa mai niman soyayyar ta? Sannan ga Umma ma, lallai ya ɗibo da zafi Amma zai roƙi Allah ya sanyanta masa ya shige masa gaba.

Alaji Abdou ya fara sallaman barrister Sannan ya sallami Yaseer zasu zanta da iyayen akan yanda lamari ya juye shi kuma zai je ya san nayi.

Sai da aka yi la'asar Sannan yayi wanka ya sake shiga ya fito da key ɗin motar shi a hannu.

Ya samu drivern da yake ɗauko Reina yana warming mota don tace masa 5:30 zasu fito daga lectures, idan ya fita yanzu kafin ya isa lokacin ya cika tunda tafiyar da nisa.

Driver ya ƙaraso da nufin karɓan key ɗin hannun Yaseer yana faɗin "Alhaji fita zaka yi ne? Gashi Hajiya Babba ta aiki Nuhu amma ba nisa yayi ba, muje in kai ka sai shi in faɗa mishi ya bi ya ɗauko Hajiya Hafsah a makarantar"

"No ka huta kawai, zan je in ɗauko ta da kaina" yace yana wucewa cikin nishaɗi ya ɗauko motar da bai cika bawa drivers su ja ba sai dai idan zai yi tuƙi da kan shi kana ya ɗauki hanyar Gubi campus.
.
.
.
Daga cikin motar da Yaseer ya faka a tsallake ya hango ta sun fito da Safina da wasu ƴammata biyu tana goye da jakar bayanta a kafaɗa ɗaya, ga jilbab ɗin da ta saka ɗaurin kan ya warware, fuskar ta yayi maiƙo kana ganin ta zaka fahimci gajiyar dake jikinta don duk da kasancewar yau ɗin asabar wuni suka yi suna lectures aka kuma rufe musu ranan da test.
Chapter 59 · 0% Book details