← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 117

Sashe 60

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ƙura mata ido ko ganinta a haka zai saka yaji wani abu da yake ji a game da ita ya ragu, amma matsayinta a zuciyan shi ko motsi bai yi ba balle ya girgiza.

Ganin babu motan dake zuwa ɗaukan su a wurin da ya saba tsayuwa sai wani motar daban ta ɗaga waya da nufin kiran drivern ta ji ko an samu wani tangarɗa ne tunda bai saba makara ba sai ma yazo ya jira ta. Gashi yau har da ɗebo wasu zasu rage musu hanya.

Ganin haka Yaseer ya buɗe motar ya fito yana maida ƙofar ya rufe sannan ya jingina a jikin sa.

Mamakin ganin shi ya saka Reina sauƙe wayar daga kunnenta tana ƙare mishi kallo, ko motar da yazo da ita abun kallo ne balle shi kan shi dake cikin wata farar shadda mai maiƙo.

Ba zallan wanda suke tare ba har wasu dake wurin attention ɗin su yana kan shi don ko ɗan committee ɗin hassada sai ya yaba balle ƴammata masu ido da kwalli.

Idanun shi na kanta ya sake mata murmushi lokacin da suka ƙaraso kusa sannan ya tako gabanta ya kai hannun shi jikin jakar bayan ta sai ta juya ta zame shi daga kafaɗan ta.

"Sannu da gajiya ko Sarauniyar Mata" yace yana karɓan jakar ita dai Reina da ido kawai take bin shi, suka gaisa da Safina cikin girma da arziƙi Sannan ta sanar da shi zasu rage ma ƴammatan nan hanya yace ba matsala.

Sai lokacin ƴammatan suka matse murya suka gaida shi ya amsa su da "sannu" kawai ya saka Hafsatun shi a gaba har ɓangaren mai zaman banza ya buɗe mata ƙofa ta shige ya rufe sannan ya zago ya shiga driver seat da jakar a hannun shi lokacin har sun gama shiga don haka ya juya zai ajiye jakan a space ɗin ƙasan bayan seat din shi wurin ƙafan wata, yanda ya tsuke fuska lokaci guda ya sakata matsawa da kafar ta jakan ya samu wadataccen space tukun ya tada motar da dukkan su suke jin kaman suna tafiya a iska babu ƙara ga taushin seat ga raɓa ga ƙamshi.

Reina da ta lume cikin seat ɗinta tana huta gajiya dai bin shi take yi da kallon mamaki, ba don ya ɗauki jakan ta ko dan ya buɗe mata ƙofar mota ba tunda wa'innan ba yau ya fara ba. Mamakin shi da take yi na ganin tsawon sati biyu kenan da ya ɗauki gaba da ita a kan zancen Uncle Bilal.

Ah toh gaba mana tunda bayi kula ta bayi mata magana, har sai da ya saka taji kaman tace ma uncle B yayi haƙuri kawai ko zata samu ta gane kan Yaseer amma son da take mishi yafi karfin haka, ta amince zata zauna da matar shi da yaran shi tunda ba a kanta aka fara auren mai mata ba kuma ba haramun bane.

"Have some water" yace yana miƙa mata goran ruwan da ya ciro a wata mini fridge da sam basu lura da shi ba. Gashi kuwa da ɗan sanyi kuma wuyan su a bushe yake don haka ta shiga kiciniyar buɗe marfin yayi gamm kuwa kaman wanda aka ɗaure da Flyer.

"Easy Ma Cherié" yace yana niman wuri yayi parking sannan ya miƙa hannu ta bashi goran yayi mishi murɗi ɗaya.

Saida ya jira ta sha kusan rabi ta miƙa ma ƴan baya sauran Sannan suka cigaba da tafiya.

Basu yi nisa ba zaman shirun ya fara isan su, sai waya da Yaseer kan amsa kaɗan-kaɗan masu muhimmancin cikin don bayi son su ɗauke attention ɗin shi, gashi ƴammatan nan tsoron magana suke duk sun kame kansu kaman kyanwa a jaka.

Safina ne ta ƙare ta ɗan zamo daga kujerarta ta riƙe bayan kujeran Reina sannan tace "yaya Yaseer kaima kana kallon kdramas ne?"

"Menene kdramas kuma Feenah?" Ya kira ta kaman yanda Reina take kiran ta sai Reinan ta ɗago ta dube shi.

"Korean dramas, ko Cdramas ko Anime duk baka kallo?"

Ya girgiza kai idanun shi a kan hanya.

"Gashi yaya Muhammad ya fara kallo har yana son zama addicted don har ya gama kallon Moon lovers a cikin sati biyu."

"Kice ke kika koya ma Muhammad wasa da aiki kawai"

Dariya Safina tayi tace "akwai daɗi ne kuma gwamma ana yi ana ɗan haɗawa da nishaɗi"

Ya jinjina kai sannan yace "Reina tana kallo?" Sai ya juyo ya dubeta itama shi take kallo jin ya sako ta a hirar su. Muryar shi bai kai yanda yake yiwa Safina magana ba yace da ita "idan kina kallo nima zan kalla"

Dake niman sulhu take yi sai tace "wani iri kake so?"
Ta buɗe wayanta tana duba wanda take da su tana faɗin "Akwai genre da yawa. Akwai action da thriller da mystery na san zaka fi son irin su."

"Na soyayya nake so, irin wanda kike kalla shi zaki tura mun" ya ɗauki wayan shi ya mika mata. Hannun ta suka karɓa amma kanta yana bata ba Lafiya ba.

"Na zamani ko na da?"

"Kowanne"

Tura mishin kuwa ta shiga yi har suka isa awala sai suka ga yayi parking. Ƴammatan sun ɗauka har gida zai kai su amma babu yanda suka iya haka suka fito daga cikin motar suna saka ƙafar su a waje kaman wanda suka shiga cikin oven.

Saida Safina tazo fita ne ya dakatar da ita yace zasu kai ta gida.

Suka cigaba da tafiya suna hira Reina ta mayar da hankali a kan tura masa film sai bayan da yake shiga ne ta shiga gallery ɗin shi tana tura ma kanta hotunan sa kusan duka da ta gani don duk babu wanda zata ce bai yi kyau ba, daga professional na talle har zuwa wanda akayi mishi da cameran waya.

Cin karo da hotunan Aicha da tayi ne ya saka ta jan tsaki mtsewww.

Yayi saurin duban ta yana tambayar "Lafiya"

"Ita wannan bata da waya ne ta cika maka naka wayan da hotunan ta?" Ta juyo mishi wani hoton Aicha da shi bai ma san da shi a cikin wayan ba.

Wannan yarinya da kishi? Ya ayyana a ran shi a zahiri kuma cewa yayi "ki goge"

Bai sani ba abinda take yi kenan ma. Ta maida hankali taci gaba da duba hotunan gashi har da na Maama yana da shi da wanda suka ɗauka da ƴan uwan shi da wanda suka ɗauke ta ita kaɗai amma ita bata ga hoton ta ko ɗaya ba.

"Hmm ni ko hoto na ma baka da shi" tace tana taɓe baki.

Sai ya lashi laɓɓen shi yana cewa "ko? Toh ki tura mun"

Guda goma ta zaɓa ta tantance uku wanda suka fi kyau ta tura mishi, ciki harda wanda Safina ta ɗauke ta ranar da suka je restaurant ɗin nan.

Akwai abinda kuke so? "Ya tambaya yana parking a pizza heaven.

"Yes beef pizza please, extra cheese thank you " Reina ta ambata cikin fara'a kaman ya san ƴar gusau take ji.

"Kefa Feenah?"

A kunyace tace "duk abinda na samu"

Reina ta dube ta da mamaki "laa ki sake jikin ki yaya Yaseer ne fah"

Murmushi yayi ya rufe su a motar ya shiga ciki bayan wani lokaci ya dawo ma'aikatan wurin suna biye da shi da kayan da ya saya.

Ƙofar baya suka buɗe ya bawa Safina haƙuri Sannan suka ajiye kayan a kan seat yace ta ɗauki abinda take so sannan ya ɗauki kwalin pizza ɗin Reina wanda shine a sama ya zaga mata da shi.

"Kin tura mishi When life gives you tangerines, da Tale of the nine tailed? Shine abinda yaji suke fada lokacin da ya koma cikin motar.

"Ai ya ce na soyayya yake so dole na tura mishi"

Ya miƙa mata kwalin pizza ɗin ta karɓa da godiya "gashi sai ki duba if it's to your liking, akwai abun sha a kayan baya amma sai ki bari mun kusa isa ki ci a gida"

Ta sake mishi Godiya sannan suka cigaba da tafiya suna mishi hiran fina-finan da suka tura mishi har suka sauƙe Safina suma suka yi gida.

Cikin Sa'a Uncle B yana surgery da yamman don haka suka sha hira mai daɗi da Yaseer har suka isa bai kira ta ba.
.
.
Gajiyan da Yaseer ya ga tayi ga kuma test da ta rubuta ya saka yace yau ta huta babu karatu.
Wai sai gashi nan da tarin abun yi a gaban shi ya ƙura ma screen ɗin MacBook ɗin shi idanu yana kallon film saboda ya burge mace.

Kuma yana gama episode one ganin dare bai yi sosai ba ya kira ta ya bata review sai ya ji ta on another call as always.

Babu komai a hankali zai bita, lokacin da zata daina ɗaukan kiran Uncle B ma bata sani ba.

~~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

85

*Jama'are*

Kamal da Saudat ne durƙushe gaban goggo Halime, ita tana faman zubar ƙolla shikuwa kallon ta yake yi da mamaki. Yau da safen nan ya sanar da ita a kan zancen Yaseer da Reina amma shine ko rana bai gama faɗuwa ba har ta kawo shi ƙara.

"Naji ta bakin ki Saudatu. kai fa, kana da abin faɗi?" Ta dubi Abbah sai ya sauƙe kallon ɓacin ran da yake wa Umma sannan yace "goggo yaron nan sai da na tambaye shi, kuma da bakin shi ya shaida min yana son yarinyar nan.."

"Da kuka tursasa shi ba?" Umma tayi saurin katse shi. Sai ta ja numfashi ta cigaba da zubar hawaye "Idan ba haka ba ta ina Yaseer zai so mai sunan Hafsatu ma balle ita kanta? Ka manta azabar da ya sha a domin ta? Ka manta ƙunci da baƙin cikin da shi da mu duka muka shiga duk a dalilin ta? Ai idan mun yafe ba yana nufin ya goge a cikin kwakwalwar mu bane don haka kuka salwantar da farin cikin sa saboda cikar burin ku Wallahi baku yi mishi adalci ba!"
Chapter 60 · 0% Book details