Sashe 35
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Miƙewa yayi a matsayin na biyu ɗauke da plates ɗin shi, ya mayar da abinda bai cinye ba cikin food flask ɗin sannan ya kai abinda ya ɓata kitchen sink, daga nan ya fita waje ta ƙofar baya yanda kafin ya dawo ta bar wurin.
Hannun shi a aljihun wandon shi ya ɗaga ido ya kalli sama, Hasken rana ya wadaci samaniya, tsuntsaye suna ta shawagi suna kuka mai daɗin sauraro kaman basu san zuciyar shi a hargitse take ba.
A ciki Maama ce na ukun tashi itama tasu islamiyyar zata tafi.
"Reina kije kuyi wanka ko? Ina jiya kun zo da kaya daga gidan Ummi?" Umma ta tambaya ganinta da wata doguwar rigar tsohuwar atamfa da hijabin roba kuma da alama a cikin su tayi barci a maimakon kayan barcin da suka dace, ba don baƙunta ba ma ita ba'a zuwa teburin cin abinci sai anyi wanka an shirya don bata son ƙazanta.
Ita kuma Reina a nata bangaren kayan jikin ta sune sleeping dress ɗinta, domin da su take kwana take tashi a gidan hajiya Hauwa.
"Eh mun ɗibo" ta amsa mata.
"Toh maza idan akwai abinda kike buƙata sai kiyi magana"
Ta so ta bi bayan Yaseer ne ganin har yanzu bai fito daga kitchen ɗin ba, tana tsananin buƙatar ganawa dashi, saboda tana da explanations da take so tayi mishi, tana da uzurori sannan tana da tambayoyi, amma sai ta samu kanta da amsawa da toh ta juya saman benen ko daddyn tan bata samu sun yi gaisuwar kirki ba.
.
.
Rabon ta da wanka da su shower gel su menene ɗinnan har ta manta, don haka ta ɗauki lokaci tana lailaye jikin ta a ban ɗakin dukda ma an yi mata gyaran amarci sama-sama a gidan Ummi, duk don kada kokwanto ya shiga zuciyarta ta ɓata musu shiri, amma bata fito ba sai da jikin ta ya amsa ƙamshin lavender and citrus da kayan wankan suke yi, tana shafa lotion shima tana rufe ido saboda kamshin sa mai daɗi dake shiga hancin ta. Da gaske babu abinda babu a ɗakin, sannan komai sabo ne har darduman sallah kaman don su na musamman aka tanade su.
Wata riga da skirt mai ɗan mutunci ta saka na sallan bara da Ummi tayi mata, sai dai ya ɗan ɗangale mata, ita shiyasa ta gwammace dogon riga, don duk yanda aka yi mata tsayin skirt shekara ɗaya ne zata more shi yanda ya kamata ana ƙara kwana biyu shikkenan ya ɗangale.
Haka dai ta fice daga ɗakin bayan ta saka wani hijabin ganin gidan da samari, ta fita babu kowa a ƙasa yanzu, Maama da ta riga ta shiga wankan har sun wuce drivern dake kai irfan makaranta zai bi ya sauƙeta a nasu.
Ɗakin mahaifin su ta tura ta shiga da sallama, sai ta samu Abban Yaseer yana ɓalla mishi magani, tsugunawa tayi ta gaida su duka, Kamal ya amsa Alhaji Tahir kuma saida ya hadiyi magungunan sannan ya sake mata murmushi, sai ta rarrafa wurin shi ta dafa ƙafar shi "Daddy yaya jikin?"
Shafa fuskar ta yayi yana tuna ta lokacin da take da shekaru 12 kaman jiya ne wai har ta zama haka a yau, "jiki da sauƙi sarauniyata, kun kwana Lafiya?"
"Lafiya ƙalau Daddy, Allah ya Baka lafiya"
Da ameen ya amsa, tayi shiru kafin can tace "Daddy na ga Yaya Yaseer, yaushe ya fito?"
Sai yaji ƙirjin shi yayi masa nauyi har kunyar Kamal dake zaune a wurin ya daɗa kama shi.
"Shekara 7 kenan da ya samu Allah ya tseratar dashi Hafsatu, munyi yi babban laifin da Allah ba zai yafe mana ba sai Yaseer da iyayen shi sun yafe mana, mun yi kuskure Hafsatu kuma laifi na ne" yace hawaye na bin idanun shi kaman yanda yake bin nata idanun.
Ita yanzu da wani ido zata fara niman yafiyan shi bayan tsawon lokaci?.
Kuka suke yi sosai ta kifa kanta a kan ƙafar Alhaji Tahir.
Miƙewa Kamal yayi, yayi gyaran murya ganin tausayin su na son shigan shi.
"Muje ko Reina, kinga ya sha magani yana buƙatar hutu"
Da ƙyar ta iya tashi a kan kafafuwan ta tabi bayan kamal, abu na gaba da zata yi niman yafiyan Yaseer ne, koda zai kai nan da shekara ɗari, koda ace sai ta zaga bangon duniya da ƙafa kafin Yaseer ya yafe mata zata yi koma menene don kawai ya dubeta da idon yafiya.
Bayan nan kuma tana son taji aininhin abinda ya faru a tsawon wannan shekarun, yanda Mahaifin ta ya rayu bayan ya mutu, yanda aka yi rayuwar su yaya Yaseer ya canza haka da kuma yanda aka yi wuta da audugar da basu raɓar juna suka kasance cikin inuwa ɗaya.
~~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
67
~~~~~~~~~~
_J'ai retrouvé le sourire_
_(I found the smile again)_
_Quand j'al vu le bout du tunnel_
_(When i saw the end of the tunnel)_
~~~~~~~~~~
"Baka tafi emergency ɗin ba?" Saudat ta tambayi Yaseer dake shigowa ta ƙofar gaba a yanzu bayan ya gama shan hantsi har rana tayi zafi shiyasa ya komo ciki.
Waiwayawa yayi bayan shi kaman da wani daban take magana, sannan ya juyo ya shafi kan shi yana ɗan murmushi, ya manta ma shaff da yayi ƙaryan zai fita.
"Na saka an fasa ne sai gobe"
"Toh yayi kyau, sai ka sami yarinyar nan ta faɗa maka abinda take buƙata ita da ƙanwar ta ka samar musu da kuɗin ta kaman yanda kace, sannan Abban ku yace taci gaba da zuwa makaranta daga gobe"
Tambayar ta wata yarinya yaso yi amma ya sani ya dawo rainin hankali kuma bayan duka wannan bayanin.
"Toh Umma, tana ina ne?"
Tsakar kanta ta gwada mishi tana watsa mishi harara, tun jiya haushin sa ya kama ta ganin yanda ya wani susuce ya fita daga cikin nutsuwar shi.
Murmushi yayi sosai wannan karon har sai da fararen haƙwaran shi suka bayyana. Yayi mata jinjinan ban girma "Allah ya ja zamanin Umman mu, uwar ƴan samari da Aishatun Niger."
"Na ƙaraso wurin ranka zai ɓaci Yayanmu" tace tana ƙoƙarin basarwa amma murmushi ke son kwace mata.
Ya dubi Suhail da fitowar shi kenan daga ɗakin motsa jiki, yayi wanka a bathroom ɗin wurin ya mayar da kayan shi sannan ya fito da ƙaramin towel a wuyan shi zai haura upstairs ya canza kaya.
"Kai kira min Reina, kace ta same ni a study room"
ya ambaci sunan a karo na farko bayan da suka yi ido huɗu da ita.
"Ni kuma?" Suhail ya nuna kan shi, tabbas ba shi ɗin aka ce ba ko ba ita aka ce ya kira ba.
"In je in kira ta da kaina ne?" Yaseer ya tamke fuska.
"Allah ya baka haƙuri zan kira ta" yace yana juyawa hanyar da ya ɗauka tun farko.
A ƙofar ɗakin da aka basu ya tsaya yayi knocking sau biyu yana ƙare haɗe giran sama da ƙasa.
Reina kuwa zaman shiru da ɗar-ɗar da mutanen gidan da suke yi da ita yasa ta dawo ɗaki tunda taga TV a ciki, sai ta zauna takunna Cartoon network yana ɗan ɗebe mata kewa.
Tunanin Uncle Bilal take yi, yanda tun dawowar Jamal ƙasar ya fita a harƙan ta ya daina kiran ta, kuma ko ta ari waya ta kira shi da yaji ita ne zai kashe. A iya sanin ta babu wani abu a kanta da Abinda ya faru da ita a baya da bai sani ba, to ko su Umman Zahra sun haɗa mata wani sharrin ne a wurin shi? Ko kuma ya gaji da hidimta mata ne ya jefar da ita kada ta dame shi? Amma koma menene da ya saurare ta ko sau ɗaya, yanzu kuma babu yanda zata samu wani wayan balle ta kira ta sanar dashi dawowar Yaya Yaseer, sai dai ta bari idan sun sake zuwa gidan Ummi ko ta gwada aran na daddyn ta.
Tana wannan tunanin ne knocking ɗin Suhail ya shiga kunnen ta. Sai da ta kashe TVn gudun kada tayi laifi kana ta mayar da hijabin ta wuyan ta kafin taje ta buɗe ƙofar.
Fuskar Suhail yanda kasan zai doke ta yace "wai kije inji Yayan mu"
Ta gane wa yake nufi tunda taji da abinda Hajiyar gidan ta kira shi kenan don haka koda ya juya ya cigaba da tafiya sai ta janyo ƙofar a bayanta ta cigaba da bin shi.
Bai fahimci tana bayan shi ba har sai da ya kusa isa ƙofar ɗakin shi, juyowa yayi yana duban ta da mamaki. "Malama yaya dai?"
Itama sai ta kalle shi cikin rashin fahimta, cikin sanyin murya domin yayi mata kama da masifaffe tace "kace ana kira na"
'kalle ta kaman na Allah' Suhail ya ayyana a ran shi yana ƙwafa, duk munafurcin Reina tarr yake kallonta idan kowa ma ya makance ne suka yarda da ita saboda wannan Sumu-sumu ɗin da take yi na munafurci.
A fili kuma cewa yayi "A ɗaki na ne Yayan mun yake?"
"To ai baka faɗa min inda zan same shi ba"
Sai da yayi tsaki tukunna yace "Dalla kije ki same shi a ƙasa a study Room" ya ƙara gaba ya barta a wurin tana mishi rakiyan idanu, tunani take yi ita wani laifi tayi mishi daga zuwan ta jiya-jiya?.
Haka dai ta sauƙa ƙasan ta samu Sabir shi kaɗai yana zaune. A ɗarare ta ƙarasa gudun shima kada ya masife ta "Uhmm dan Allah ina ne study Room?"
Da hannu yayi mata nuni idanun shi a kan TV, "me zaki je yi a ciki?" Ya tambaya sanin Yaseer ko Abba suna ajiye abubuwa masu muhimmanci kada taje tayi musu ɓarna a rashin sani.
"Yayan mu ne yake kira na" ta faɗa kaman yanda taji kowa na kiran shi a maimakon yaya Yaseer.
Da sauri Sabir ya juyo ya dube ta, "yayan mu dai? Inji wa?"
"Umm...Wannan dogon mai ido... Ina.. ina nufin wanda ya ɗan fika tsayi kuma ɗazu ya zauna a gefen umma.."
"Yaya Suhail!"
"Yauwa, Eh shi" ta amsa tana ƙoƙarin tilasta murmushi a saman fuskar ta Amma sai Sabir ya ɗauke kan shi ya mayar kan talabijin sanin cewa Suhail ba zai yi mata ƙarya ba yace "kije ki same shi"