Sashe 66
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"No idan kika ce mu juya sai mu juya, daman zuwan Saboda ke ne kuma kin gwada baki buƙatar ganin mu."
"Wallahi ba haka nake nufi ba, kawai a gida ne za'a iya mun magana saboda karatu ya kamata ace na mayar da hankali nake yi."
"Na fahimce ki, Amma ko tambayan tare da wa muke ba zaki yi ba?." Bai jira ta tambayan ba yace "tare da yaron ki Mufid zamu zo, ya damu yana son ganin ki, kinga sai muje duba daddyn tare"
Taɓɗi! Bayan Abinda ya faru jiya a dalilin fitan su da Yaseer yau ta sake?.
Numfashi ta ja "A'a har zan je in dawo kafin ku iso, Allah ya kawo ku Lafiya"
Ta katse kiran tana miƙewa da nufin tayi wanka ta samu ta fita ta dawo.
Saida ta shirya amma bata ɗauki mayafi da jaka ba ta fita niman izinin Umma kada taga kaman sanar da ita kawai tazo yi.
ta lelleƙa parlon sama ta tabbatar Yaseer bayi kusa sannan ta karasa ƙofar bedroom ɗin Umma ta ƙwanƙwasa tare da ƴar sallama.
"Shigo Reina" muryar umman ta faɗa daga ciki don haka ta tura ƙofar tana sake wata sallamar ta mayar ta rufe sannan ta ƙarasa bakin gadon da Umma ke zaune da kwalliyar ta kaman mai shirin zuwa unguwa ta sha sarƙa da warwayen zinare tana amsa waya. Haka take kasancewa kowani weekends idan mai gidanta ba zai fita aiki ba tayi ta shige da fice cikin ado da kwalliya mai ɗaukan ido kafin da yammaci ma a sake shiga tunda yanzu kam Allah ya kawo mata yaranta duk sun miƙe toh mai zata yi idan ba hutu da gayu ta ji daɗin jikinta ba?.
Magana kaɗan ta ƙara tayi Sallama da mahaifiyar Falila dake ɗaya layin tana bada sakon a gaisar mata da Falilan sannan ta dawo da nutsuwar ta kan Reina.
"Masha Allah jiki yayi sauƙi kenan?" Ta tambaya ganin Reina cikin shirinta.
Sai kunya ya kamata tace "Daman duba Daddy zan je yi a asibiti"
"Yayanmu ai yaje ɗauko shi, anjima kaɗan zaki ga sun shigo shiyasa kika ga muma bamu je ba"
Sai ta jinjina kai tare da amasawa da "toh shikkenan" ta juya cikin sanyin guiwa don ta samu kanta da kasa sanar ma umma Uncle Bilal yana hanyan zuwa. Yau sai take jin nauyin ta fiye da ko yaushe.
"Akwai wani abun ne?" Umma tambaye ta ganin yanda take tafiya kaman ana tura ta.
Reina ta juyo tana shafa goshi "Dama... Dama Uncle Bilal ne yace..." Sai ta matse baki ta gagara ƙarasawa.
"Zuwa zai yi?"
Reina taɗaga kai sau ɗaya.
"Yau?"
Ta sake ɗaga kai alamar Eh.
"Babu laifi amma kina sanar mana kafin ranar zuwan shi don ayi shirin tarban shi"
Toh itama ai sai ya kamo hanya take samun labari amma sai ta amsa da "toh Umma".
Ta miƙe itama ta zura takalmin ta "Ki sauƙa kitchen idan akwai abinda zaki tanadar masa, kinga Yau ga ranar Darling bata nan balle ta taya ki, sai ki nemi ko auta ko mai haƙuri"
Suka fita a ɗakin tare Umma ta jawo ƙofa sannan ta wuce ɓangaren Abbah ita kuma Reina ta sauƙa kitchen ganin mai zata bawa Uncle B.
.....
Da ta samu dukkan su biyu suka amince zasu taya ta sai suka ɓige da yin abincin rana kawai ta ɗeba ma Uncle B ɗin a ciki ta shirya masa manyan tray guda biyu da duk abin buƙata.
Babu jimawa ya kirata ya sanar mata da har sun shigo gari bata tsaya mamakin ko awa uku ba'a rufa ba ma'ana Uncle B yayi nisa a hanya ma kafin ya kira ta, tayi saurin watsa ruwa ta mayar da kayan da ta cire kafin ta fara aikin tana gyara fuskar ta kiran shi ya sake shigowa. Bata ɗauka ba ta yafa mayafinta yanda ya dace sannan ta ɗauki wayar ta fita ta same shi tsaye a jikin motar shi riƙe da hannun Mufid.
Sosai fara'ar ta ya kawo da ganin yaron. Ta buɗe mishi hannun ta sai ya ɗaga ido ya kalli mahaifinsa.
Gyaɗa masa kai Uncle B yayi yana murmushi, Mufid ya ƙaraso da gudu ya shige jikin Reina ta rungume shi tsamm tana jin inama ɗanta ne na cikin ta? Yaron ya shiga ranta ba kaɗan ba.
Takowa inda suke tsayen Uncle B yayi yana faɗin "sauran na daddyn Mufid" ya ɗan buɗe hannun shi. Hararan wasa ta watsa mishi ta mayar da wayanta hannun hagu ta riƙo hannun Mufid da na dama sannan suka yi hanyan shiga Uncle B bayi da zaɓin da ya wuce ya bi su.
A parlo ta zauna a kujerar dake fuskantar nashi tana miƙa mishi gaisuwa, bai amsa ba yayi mata nuni da kujerar dake haɗe da nashi ta dawo ta zauna.
A kowani lokaci daddyn ta da yaya Yaseer zasu iya shigowa, ga Umma da Abbah ma a gidan. sai tayi kaman bata gane nufin sa ba ta miƙe tana faɗin "bari na kawo maka ruwa" kuma kafin ya amsa ta wuce kitchen rike da hannun Mufid.
Sai da ta bawa yaron packet ɗin cookies sannan ta ɗauko tray ɗin da ta haɗa Juice, ruwa da ɗan abin motsa baki suka fito.
Ilai kuwa taci karo da Daddy, yaya Yaseer yana turo shi nurse ɗin dake kula dashi kuma na biye da su.
Saurin ajiye tray ɗin tayi a gefen TV stand ta ƙarasa wurin daddy ta tsuguna a gaban sa tana masa yaya jiki.
"Normal checkup ne kawai sarauniyata, kuma sun ce komai Lafiya, ki kwantar da hankalin ki" Alhaji Tahir ya amsa da murmushi.
Ɗaga idanunta wanda suka fara tara ƙwolla da zata yi by mistake sai a cikin na yaya Yaseer, Tayi saurin kawar da ganinta don ba zata iya jurewa ba. Uncle B ya durƙusa yana miƙo ma Alhaji Tahir gaisuwa ya amsa Sannan yace ma Yaseer su ƙarasa ɗaki ya samu ya huta.
Hannu Yaseer ya saka ya ɗauki abinda yafi girma a kan tray ɗin da Reina ta ajiye ba tare da ya tantance menene ba, ya tura Alhaji Tahir suka yi gaba kaman babu halittar Uncle B a wurin.
A kunyace ta ɗauki bowl ɗin ta koma kitchen ta mayar da abinda ya ɗauka sannan ta dawo da shi kan tray ɗin ta ɗauka ta kai gaban Uncle B ta durƙusa ta shiga zuba mishi abin sha kana ta koma wurin zaman ta tana gaida shi.
Sai da ya amsa ya ɗora da "ai bayan na sha kira ba'a ɗauka bane nayi tunanin ko ba lafiya ba hankali na a tashe na bugo sammako, ashe ke ƙalan ki ma"
Da gaske ta ɗauka ta tsallake wa complain ɗinnan don ita murnar ganin shi ya mantar da ita abinda ya faɗa mata a text jiya.
Sai ta cigaba da wasa da Mufid kaman bata ji abinda yace ba.
"Son come" ya yafato Mufid da hannu sai yaron ya koma jikin sa, ya bashi glass ɗin orange juice da Reina ta zuba sannan ya maido da duban sa gare ta.
"Yanzu zaki saurare ni? Ina gaban ki doll har wani abu zai ɗauke miki hankali?"
Murmushin yaƙe tayi tace "me ka ce?"
Bai yi ƙasa a guiwa ba ya sake nanata abinda ya faɗa.
"Sorry, barci zan yi shine na saka wayan a DND kuma na manta ban cire da wuri ba." Ta faɗa dai-dai Yaseer ya fito daga ɗakin daddy, maganar ta ya shiga kunnen shi ya tsaya mamakin Reina ta iya bada haƙuri ashe, ma shine ba zata bayar ba.
Bai kalli yanda suke ba ya ɗauki hanyar waje. Babu daɗewa kuma ya dawo riƙe da wasu shopping bags guda biyu sannan ya kira ta.
"Reina" da dokawar zuciyar ta da miƙewan ta tsugul babu tazaran sakwan ɗaya.
Ta ƙarasa gaban shi da rawar jiki "gani yaya Yaseer"
Laidan hannun dama ya fara miƙa mata yana faɗin "ga wannan a wanke ki yanka min sweet melon da apples ki kawo min upstairs sauran kuma a saka a fridge".
Sai da ta karɓi laidan da yake da tabbacin nauyin sa, saboda fruits ne da yawa a ciki ya siya amma don ya ɗaga ta a gaban Uncle B ba zai tanada su da kan shi ba.
Tana karɓa nauyin ya saka ta ajiyewa a ƙasa tana mai amsawa da "toh" sannan ya mayar da laidan hannun shi na hagu zuwa hannun dama kana ya miƙa mata.
"Wannan kuma naki ne"
Karɓa tayi ta leƙa ciki idanunta suka yi karo da package ɗin slice cake ya sha frosting har saida ta haɗiyi miyau ta ɗago da murna tace "Nagode yaya Yaseer"
"Anything for you. Ina jiran ki" ya faɗa yana nuna mata saman sai ta shiga gyaɗa kai cike da jin daɗi, ta manta shaff da halittar Uncle B a parlon, Amma saboda Yaseer ya ƙunsa masa saida zai wuce yace "sannu fah" yana ɗaga masa hannu daga nesa ya wuce abin shi bai jira amsawar shi ba.
Ta juyo tayi arba da idanun Uncle B a kanta yana binta da wani kallo tsakanin mamaki da ɓacin rai.
Yanke shawarar taje tayi abinda aka saka ta tayi idan ta dawo su dabdale da kyau tunda ta san dole sai yayi magana.
"Please give me 10 minutes uncle Bilal, yanzu zan dawo" itama tayi wucewar ta ba tare da ta jira cewar shi ba.
Saida ta fara taɓa cake ɗin tana rausaya kai cikin santi sannan ta rufe sauran ta saka a fridge na cin anjima Idan ta zauna ta nutsu. A maimakon ta ajiye wankin fruits ɗin zuwa anjima shima tayi saving time, tunanin haka bai zo mataba saida ta wanke su tass ta jere komai a wurin da ya dace cikin fridge, Lokacin har ta wuce minti sha biyar. Haka dai ta ɗauko peeler ta fere melon da green apples tass tunda yaya Yaseer bayi son Red sannan ta yi slicing a plate daban-daban ta saka fork ta fito.
"2 minutes more please Uncle Bilal, yanzu zan dawo"
Bai ko kalleta ba balle ya gwada ya ji abinda tace, ta san halin kayanta don haka tayi gaba idan ta dawo sai tayi rarrashi da tushe.