← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 117

Sashe 104

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Reina tayi ɗan karamin murmushi tana godiya ma doctor Fahad kana ta dubi Yaseer dake zaune tare da ita tana ƙara faɗin murmushin. Itama ta shaida tana samun waraka cikin gaggawa shiyasa ta buƙaci ya kasance tare da ita a ganawar yau, domin yanzu tana jin a shirye take ta fara buɗe mishi sirrukan da ta binne a ƙasan zuciyarta domin ta guje musu. Yanzu ta daina gudun, Dr Fahad ya taimaka mata sun tono shi kuma bata jin tsoron ta buɗewa mijinta ya gani.

Murmushin alfahari Yaseer ya mayar mata yana patting bayan kan ta.
"Shiyasa nace maka ita ta musamman ce" yace da Dr Fahad idanun shi na kan matar shi.

"Haka ne, kuma daman therapy yafi aiki ne idan patient ya shirya ma niman waraka daga abinda yake damun shi ko kuma idan ya samu ƙwarin guiwa daga makusantar shi. Amma managing ɗin trauma da gaggawa kuma shi yafi, domin da ace lokacin da abun ya faru aka ɗauki wannan matakin, da bata sha wannan wahalar ba, amma Allah yasa kaffara ne"

Suka amsa da Ameen.

Dr Fahad ya ɗaura da tambayar "Yanzu yaya kike ji game da shi?"

"Jamal?" Ta ambaci sunan da sauƙi kaman yanda take kiran na kowa.

Dr Fahad ya gyaɗa kai ta cikin screen ɗin. Shirun second biyu tayi kana tace "tausayi yake bani"

"Tausayi? Interesting. Zan iya sanin mai yasa?"

Ta sauƙe numfashi kafin tace "Saboda koda ya cutar da ni, kan shi yafi cuta, haka iyayen shi ma ɗan su suka cutar, amma yanzu da zuciyata ta fara hutawa memories ɗin abinda suka faru suma sun fara gogewa daga cikin kaina. Saidai zai tabbata a halinda ya jefa kan shi koda bayan na gama manta komai"

"Haka ne. zan iya tambayar abokin rayuwar ki fa? Yaya kike ji game da shi?"

"Mijina?" Ta tambaya sai ta riƙo hannun Yaseer cikin nata biyu, tana kallon cikin idanun shi da murmushi. "A yanzu shine duniya ta. Ina jin kamar idan ina tare da shi bani da sauran damuwa har da wannan, I'm only free when I'm with him. I can finally breathe, properly."

Yaseer ya zame hannun ya zaga shi gefen ƙugun ta ya riƙe ta da kyau.

"Masha Allah" Dr ya murmusa don ya fahimci komai ya daidaita a tsakanin su.

"Gaskiya kin yi namijin ƙoƙari kuma ya kamata mijin ki yayi miki kyauta. Yanzu zamu iya mayar da ganawar mu sau ɗaya a sati ko kuma idan wani abu ya taso na gaggawa a tsakanin haka sai ku tuntuɓe ni"

Yaseer ya amsa da "In sha Allah doc. Mun gode" daga haka suka yi Sallama..

"I'm proud of you Wifey, so proud" ya sumbace ta a kunci.

"Doctor kyauta yace a bani banda daɗin baki"

"Shirya, shirya mu fita" yace yana sauƙe ta a ƙasa.

Shirin da zai ɗauke su minti talatin tunda already sun yi wanka sai gashi ya ɗauke su awa biyu da rabi tare da ƙarin wanka kafin suka fita Reina tana jinjina Hikima irin na Umma da tayi mata kitson nan da yanzu tana ta fama domin idan kanta yaji ruwa duskurewa yake yi sai tayi deep conditioning ɗin shi kafin ta samu gashin ta ya kwantar da hankalin shi.

Armada mall suka nufa, lokaci ƙarfe 12 da rabi agogon Turkey. Suna shiga ciki Reina ta sake ganinta a wata duniya daban. Stores ne birjik iya ganinka kuma babu abinda ba zaka samu ba in dai kana da kuɗin siya, komai an tanade shi a section daban.

Saida suka ɗan zaga domin duk store ɗin da yayi mata tayin shiga sai ta girgiza kai lissafin ta duk ya juye.
Basu daɗe da isa ba lokacin Sallah yayi don haka suka wuce Masallacin dake mall ɗin suka yi Sallah sannan Reina ta ɗan samu nutsuwan fara tunanin abinda take so.

Store ɗin wani customizable perfumes Yaseer ya kai su, yana riƙe da jakakkunan abubuwan da suka siya, ya ciro handkie ɗin shi ya bawa mutumin ya shinshina Sannan ya shiga haɗa turaren suna kallo har ya basu suka yi tasting sakk irin turaren shi kuwa, kafin ya juye a container da ya kamata. Reina kuma ta masa kwatancen irin ƙamshin da take so, sai ya haɗa mata wanda yafi shi daɗi.
Da aka buƙaci sunan da za'a bada haɗin sai tace a nasa a saka Rey nata a saka Reina, sarki da sarauniya kenan.

"Ni da na kawo ki in miki kyauta kuma shine zaki mun?" Ya karɓi pouch ɗin turaren da ta karɓi card ɗin shi ta biya shine ta miƙo mishi wai gashi ta siya masa.
"toh na gode Mrs YK"

Ɗan rausaya kai tayi sannan tace "You're welcome hubby"

"Yanzu muje in baki naki kyautan" ya sake riƙo hannunta suka shiga store ɗin Cartier. Daga yanda taga ba mutane da yawa ta san ba shagon gama-gari bane. ga sarƙoki, zobuna da bracelets sai shining suke yi a cikin akwatunan su dake killace cikin glass case, har ma'aikatan wurin hannayen su da gloves.

Tun daga ƙofa aka gaida su, aka yi welcoming ɗin su ciki tare da basu wurin zama sannan suka tambaye su abinda suke so don a gabatar musu da shi.

"I'll like a beautiful bracelet for my beautiful wife" cewar yaseer.
"Got you sir" ma'aikaciyar tace da ɗan murmushinta sannan ta jere musu cases ɗin wanda zasu iya yiwa Reina wurin guda shida a wurin ta zaɓi wanda yayi mata.

Ta gwada farincikin ta sosai kuma tun kafin ta zaɓa take nanata godiya, sai ta fara gwadawa da mai ƙarancin design saboda kada ya kashe kuɗi mai yawa sai aka ci Sa'a yayi mata ruwa.

Yana cikin taya ta gwadawa wani ma'aikaci yaje ya saka wani ƙaramin case a cikin shopping bag ɗin da aka karɓa aka ajiye musu kafin ya dawo ya gyaɗa ma Yaseer kai a fakaice, lokacin sun samu bracelets ɗin da yayi mata ya biya suka fito sai kallon hannun take yi. Suna fitowa kuma Muslim pro ɗin Yaseer ya fara kiran sallah don haka suka wuce masallaci don gabatar da la'asar, sannan suka shiga Kahve Dünyasi bayan sun idar.

Reina tayi ordern Iced latte da macaron, shi kuma yayi ordern pastry mai karancin sugar da tea suka zauna sai kallon bracelet ɗinnan take yi tana juya shi. Can ta ciro waya tana ɗauka a hoto bayan an kawo orders ɗin su ma ta sake ɗaukan wani.

Ta ajiye wayan domin su fara ci Sai taga case ɗin cartier a gaban ta zoben ciki na faman ƙyalli.

Ɗagowa tayi ta kalle shi bakinta ba a buɗe ba kuma shi ba a rufe ba, shima irin kallon ta tayi masa yake binta da shi.

"Bae!"

"Yes babe"

"What is this?"

Ɗaukan case ɗin yayi a hannun shi ya cire zoben ya riƙo hannunta yana faɗin "kin tuna daren da muka fita a Abuja nace I have a surprise for you har wasu useless mutane suka ɓata?"

Gyaɗa kai tayi da sauri tana jin kaman hawaye zai zubo mata.

"Toh abinda na shirya kenan amma mood ɗin ki yasa na haƙura sai yau" ya shirya zura mata zoben amma yatsar ta akwai tsohon azurfan Aunty.
Sai ta janye hannun tana ƙokarin zare azurfan ya dakatar da ita ya riƙo ɗaya hannunta mai bracelet ɗin ya saka mata, ya tsaya yana kallon yanda yayi mata daidai daman dominta aka yi.

Ya riƙe hannun ya sumbata sannan ya dube ta. "So Mrs Yaseer Kamal Jama'are. Will you be my... Forever? Tunda you're my wife already"

Ta ɗan yamutsa fuska kaman tana tunani ɗinnan, ya ware idanu yace "Really? Nine fah! Duniyar ki, Idan babu ni ba zaki iya numfashi ba"

Sai tayi dariya sosai kafin ta jijjiga hannun shi dake riƙe da nata "Yess. I'll be your forever and ever Mr Yaseer kamal Jama'are"

"I'll love you forevermore" Ya sake sumbatan hannunta yana faɗin "sai na faɗawa Abbah kin kira sunan shi gatsau"

"Ai nima sunan kaka na ne" ta mayar mishi tana zuƙan latte ɗinta.

"Oh sunan baban daddy kenan kika kira? Still sai na fada "

Sun ƙarasa wunin su cikin nishaɗi tunda suka zo sai yau Yaseer yayi posting a social media ya ɗaura hoton da suka yi jiya a wani outdoor cafe a Instagram story ɗin shi, ita kuma ta ɗaura na zobe da bracelet ɗinta da ta dauka a Kahve Dünyasi tunda nata account ɗin private ne.
har performamce ɗin wasu masu Turkish dance suka gani a tsakiyar mall ɗin, suka ci abincin dare a wani Chinese restaurant sannan suka fara shirin komawa masauƙi.

Dawowa Yaseer yayi riƙe da goran Rose water da ta saka shi ya ɗauko, ya kama ta tana duba jikin kwalin pad domin ba brand ɗin Nigeria da ta saba amfani dasu bane kada taje ta ɗauki mara wings.
Da ta samu wanda hankalinta ya kwanta da shi sai ta jefa a cikin shopping cart ɗin su. Sai hango hannu tayi ya ƙara mata guda biyu a ciki. Ta juya ta fuskance shi tana matse baki, tare da mayar da kallon ta gefe.

"Ya kusan zagayowa ne?"

"Mene?" Ta dawo da duban ta gare shi.

"Your period"

Sai ta sake mayar da duban ta wani wuri kafin ta jinjina kai. Ta kara da "gobe ko jibi"

"In sha Allah nayi ajiya a wurin, ba zai zo ba" yace yayi gaba ya cigaba da tura shopping cart ɗin tayi mishi rakiyan idanu.
......

*Rafeeq*

Da lokacin haɗa abincin dare yayi Rafeeq ya tura Asal ta sanar da ita saboda ya san ta cigaba da zaman a ɗaki kuka zatayi ta yi. Ga kuma dalilin kukan nata shima yana kallo.
Story ɗin Yaseer ne ya ɗaura hoton shi da Reina kaman da safe ne ma, suna cikin shiga mai kyau da burgewa Reina tayi shigan matan Turkey sakk. Idanun Yaseer a kanta ita kuma duban ta na ga wata mage da tazo ta ɗale mata cinya a wurin.
Sai kuma kalamai masu daɗi da ya rubuta a Caption kuma yayi tagging ɗin account ɗinta, wanda yake a rufe sai wanda ta amince zai iya dubawa profile picture ɗinta kuma har yanzu Cartoon ne.
Chapter 104 · 0% Book details