Sashe 48
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata amsa ba ta shiga tunanin dalilin da yaya Yaseer zai yi haka. Ko dai bayi son ta da uncle B ne? Gashi yanzu ta saka ma ranta ba zata sake yin abinda bayi so ba ko menene shi don su zauna Lafiya kuma ya yafe mata.
Sai da uncle B ya sake magana hankalin ta ya dawo gare shi "Daddy ya dawo ko Reinan Daddy?"
Washe fuska tayi "I was so happy uncle Bilal, ashe Daddy na yana raye, nayi farin ciki matuƙa"
"I know you'll be surprised duk da naso da daga baki na kika ji"
Ta ɗan ware ido "So ka sani tun farko?"
"Har mun yi magana da shi ma, amma da ba zan bari Aunty Hauwa ta cigaba da yunƙurin ta ba kema kin sani"
Da haka suka cigaba da hirar abubuwan da suka kasance a tsakani har gajiya ya saka barci yayi awon gaba da kowannen su wayar bata katse ba.
~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
76
"Wai a kan ganyen shayi yayan mu ya tara mu yake wannan sababin?"
Suhail ke magana ƙasa-ƙasa da Sabir lokacin da suka zo wucewa ta ƙofar ɗakin su Reina ita kuma ta fito zata je amsa kiran missed calls ɗin shi da ta gani har 3 tana bacci wayar su da uncle B yana kan tafiya har sai da aka fara kiraye-kirayen la'asar ta farka, tama manta da ita ta kira shi sai da ta katse kiran aka turo mata message ɗin katin da suka ci, ta shiga mamakin yawan kuɗin da Yaseer ya saka mata a layin da bai ƙare tuntuni ba, shiyasa da ta farka bata yi garajen maida kiran ba gwamma ta je kawai.
Bata gama tunani ba Aicha tazo wucewa tana matsar ƙwalla don ta ji zafin abun sosai. Sau nawa sauran suna shan tea ɗin shi koda shine last pack? itace ma take hana su wani lokaci idan ta ga babu yawa ta ɓoye masa. Amma koda sun shanye yazo ya samu babu bayi maganar da ta wuce cikin cokali shikkenan ya haƙura, Amma dake yau ita ce har da wani tara su.
Juyawa Reina ta yi tana shirin komawa koma menene zasu gamu anjima idan ya huce ta jiyo muryar Irfan a bayan ta. "Aunty Reina Yayanmu yana kiran ki"
Sai da ta kalli gefe da gefe sannan ta juyo ta nuna kanta, yanzu kuma ita ce har da su Aunty?.
"Eh ke, ki ƙarasa yana jiran ki"
Sadaƙarwa tayi ta wuce kafin ta ƙara wani laifin.
Sai da tayi sallama ya amsa ta cire flip-flops ɗin kafar ta a bakin carpet ɗin tsakiyar parlourn ta hau kai ta zauna kanta a ƙasa ta amsa da "gani".
"Da waye kike waya tsawon awanni 2 da rabi?"
Ɗagowa tayi taga yanayin shi, "barci ne ya ɗauke ni ban sani ba"
"Shi wanda ya kira kin kuɗin banza gare shi ko?"
Shiru tayi domin idan ya san ita ta kira ma sai ɓacin ran yafi haka.
"Sauya halin ki kike son yi ko Hafsat? Kina zama da masu hure miki kunne ko? Suna koya miki abinda ba shine ba"
Girgiza kai ta shiga yi kawai.
"Ko shi wannan ɗin ne yake koya miki abubuwan da kike yi"
Ba don ta san wasu abubuwa yake nufi ba ta girgiza kai.
"Kika bar shi ya lalata miki rayuwa saka ki zai yi a bala'in da yafi na baya"
"A'a fa aure na zai yi. Kuma mutumin kirki ne uncle B yana da ƴa mace shima yace ba zai yi mun abinda ba zai so ayi mata ba" sai da ta dire aya kuma ta tuna da wanda take magana ta yi saurin kare bakin ta.
Ya jinjina kai.
"Jeki"
Daga nan bai sake ce mata komai ba, da yaga zafin zuciya zai dame shi kuma bata da niyyar tashi sai shi ya miƙe ya bar mata parlon.
Kitchen ta wuce ayi shirin abincin dare da ita, amma dake ran kowa a ɓace yake duk wanda ta yunƙura zata taimake shi sai yace ya gode ta bari, haka ta koma daga gefe ta zauna tana kallon su, da Yaseer ya shigo ya ɗaura tafashen kaza sai atmosphere na kitchen ɗin ya daɗa takurewa, kowa kawai aikin gaban shi yake yi babu mai ce uffan ma ɗan uwan shi sai cann Irfan ya miƙo ma Reina tafarnuwa da wuƙa ya dire a gaban ta ya ƙara gaba.
Ta fahimci nufin shi don haka babu ɓata lokaci ta ɓare shi tass ta miƙe ta kai masa inda yake tsaye jikin miyar da yake sakawa kifi.
Godiya yayi mata ya ɗebi rabi sannan yace ta kai sauran ma Yayanmu.
Kallon Yaseer da ya tamke fuska tayi ta haɗiyi miyau sannan ta taka kusa da shi ta miƙa mishi tafarnuwan.
Ganin ba zai karɓa ba ta ajiye a wurin tana tambayar shi ko akwai abinda zata taimaka mishi.
"No thank you" yace yana rufe tukunyar ya juya ya barta a wurin ya ɗebo wani tafarnuwan ya ɓare yayi crushing ya zuba a ciki.
Har aka kammala abincin daren Irfan ne kawai ta ɗan gane ma kan shi amma har maihaƙurin da yake da ɗan dama-dama bai bi ta kanta ba.
A wurin cin abinci ma saida Umma ta lura da sauyin yanayin Aicha da ta tambaya abinda ya same ta sai tace gida take son zuwa a daren.
"A'a ki bari zuwa Safiya mana kamar wacce ake kora?"
murmushin ƙarfin hali tayi tace "ina son in je in rarrashe Daddy na ne yayi min gorin bani son zuwa gida, in yaso gobe da daddare sai in dawo in yi shirin office "
" Toh shikkenan sai ki shirya da kyau Yayanmu ya ajiye ki, ki gaishe su sosai kin ji?"
.
.
A mota Aicha ta samu Yaseer bayan ta fito, tana zama ya ja ba tare da yace mata komai ba suka ɗau hanya motar shiru sai iskan dare mai daɗi dake busowa kasancewar windown motar a sauƙe yake.
"Ka yi hakuri dan Allah, na riga nayi maka ordern wasu boxes na tea ɗin, in 3 days zasu iso in Allah ya yarda, kuma ba zan sake ɗaukan abun ka ba tare da izini ba daga yau"
Juyowa yayi ya dubeta da mamaki kafin ya mayar da hankalin shi kan hanya. Shi abinda yake damun shi daban, nazarin abinda Reina ta faɗa mishi yake yi. Ya ɗauka abinda ke tsakanin ta da uncle B shirme ne kawai da wauta irin na yarinta amma kaman da gaske son shi take yi da zuciyar ta.
"Maganar me kike yi haka? Ba ya wuce ba? Kiyi cancelling ordern zan siya da kaina"
"Ai ban ga alaman ya wuce bane a wurinka tunda har yanzu fushi kake yi da ni"
"Da ke kuma? A kan me zan yi fushi da ke? A kan ganyen shayi?" Sai yayi ƴar dariya "Haba Darling ina da wannan lokacin ne? Tun daga safiya har yanzu in riƙe abu ɗaya a rai na?"
"Toh me ya ɓata maka rai idan ba wannan ba?"
Har ya ji kaman ya faɗa mata ta taya shi nazari sai kuma ya fasa tunawa da sirrin dake nata zuciyar, it will be like a slap on the face idan yaci gaba da gabato mata da zancen Reina musamman da yasan ba shiri suke yi ba.
"Wani abu ne kawai ya tsaya min a rai amma zan cire shi domin bayi da muhimmanci"
Ji tayi har ta huce ta karkato tare da saka tagumi tana kallon shi kana tace "toh ka dawo mun Yaya Yaseer ɗina da na sani"
Da Aicha ta kira sunan sai yaji ashe garɗin ba a jikin sunan bane kaman yanda yayi tsammani a bakin mai kiran shi ne.
"Lokaci yayi da zaku cire mun Yayanmu kenan" ya canza ma zancen akala kaman yanda ya saba, da haka suka cigaba da hira har ya sauƙeta ya shiga ya gaida Mariama da Alaji Abdou bai daɗe ba ya fito ya dawo.
Tana idar da sallar isha ta ɗauko kayan karatunta ta sauƙo study room sai dai bata samu Yaseer ba kaman yanda tayi tsammani, zaman jiran shi ta zauna yi tana kwafan sauran notes ɗin da ta ara a wurin Safina wanda aka wuce ta amma har ta gama ta fara karatun bai shigo ba lokacin goma har ta gota. Bata yi ƙasa a guiwa ba taci gaba da karatun amma dake dodon tan bayi kusa ta ciro waya ta hau online suna ta chat da uncle B da Safina tayi kallon status ɗin mutane har can barci ya ɗauke ta.
Kiran assalatu na farko ya ɗaga ta. Ta buɗe ido da addu'a a bakin ta, ganin ta a study room ita kaɗai ta ɗago wayarta don duba lokaci. Tana kan chat ɗin Uncle B ne ga kuma saƙon shi na ƙarshe kaman haka
'4:00pm zan zo, we'll go out for an Ice cream'
'see you then'
'sweet dreams, I love you😘 ' ya haɗo da emoji mai kiss.
Fita daga kan chat ɗin tayi ba tare da tayi reply ba tayi miƙa tana tunanin Yaseer bai shigo ba kenan da ya dawo ko kuma yazo lokacin ta shangame baki tana ta barci.
Ta tattare tarkacen ta ta kashe wutar wurin ta fice, a hanyar ɗakin su taci karo da Umma, motsin haurowan ta ne ya fito da ita daman ta idar da sallolin ta kenan tana adduo'i.
Cikin ƙasa da murya sabida gari bai waye ba tace "Reina daga ina kike a cikin daren nan?"
Itama Reinan cikin muryar ta da bai gama buɗewa ba tace "Ina kwana Umma, barci ne ya ɗauke ni ina karatu wallahi"
"A can ɗin? Ke kaɗai?" Ta san lokacin da Yaseer yayi mata sai da safe ya wuce ɗakin shi amma bata sani ba ko tsakar dare ya koma wurin kaman yanda yake yi idan barci ya gagara zuwa mishi.
"Eh, ina ta jiran yayan mu ne bai dawo ba"
"Ai da wuri ya shiga kwanciya jiya, amma ana ƙoƙarin dawowa ɗaki a kwanta idan kika ji barci kinga da samari a gidan"