Sashe 43
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta girgiza kai kawai don ba zata biye mata su kafa chaptern Yaseer ya shigo ya kama su ta rasa inda zata saka kanta ba. ta kunna wayan tana dubawa, Sabon waya ne babu komai a kanta amma ganin da layi ga network mai ƙarfi sai ta shiga wurin kira zata gwada numbern Uncle Bilal. Ta sani bai kamata ta kira shi ba amma ba zata iya hana kanta ba, idan ma ya bar yinta ne ya kamata ace ko kyakkyawar sallama sun yi, sai ta lallashi zuciyar ta da kyau.
Number ɗaya ta gani a recent calls an yi saving ɗin shi da 'YK'. Bata bi ta kan numbern ba ta shigar da wanda Uncle B yake amfani da shi a yanzu ta danna kira da fatan akwai kuɗi a layin, ta kuwa ci Sa'a ya fara ringing ta ƙara a kunne Safina tana tambayan ta wa take kira sai ta saka yatsa a baki alaman tayi shiru.
"..Doctor Bilal speaking" muryar shi ta shiga kunnen ta tun bayan dawowar Jamal. lokaci ɗaya jikinta ya mutu ta gagara ko motsa fatar bakin ta.
"Doll..." Ya kira kai tsaye Jin ba'a amsa ba amma daga yanayin yanda take sauƙe numfashi ya gane ita ce.
Ta buɗe baki domin amsawa ƙofar ɗakin ya sake buɗuwa Yaseer ya shigo ciki biye da likita a bayan shi.
Saurin sauƙe wayar tayi tana share ƙwallan da ya fara sauƙa mata tare da katse kiran ta tura shi ƙasan pillown da take jingine a jiki.
Yaseer ya bita da kallo ganin yanda duk ta tsargu, kana yace "ga doctor zai duba ki"
Safina ta miƙe suka bada likitan dama yayi mata ƴan tambayoyi kafin ya tabbatar ma Yaseer babu wani damuwa hyperventilation ne take samu a dalilin panic attack, ya sallame ta zasu iya tafiya ya fice.
Ƙarasowa jikin gadon yayi ya ciro wayar da ta ɓoye, har zuciyan ta ya fara bugun uku-uku a tunaninta dubawa zai yi amma sai taga ya ɗauki jakar ta ya jefa a ciki "Muje" yace yana riƙe da jakan.
"School ɗin?"
"Gida zaki koma sai gobe"
Tun da dai ba gidan Hajiya Hauwa bane babu matsala.
"Safina zata riƙe jakan" ta miƙa hannu zata karɓi jakanta daga wurin shi ya matsar.
"Ta taimaka miki ku fito, kada ku ɓata mun lokaci" da haka ya juya ya fita.
Yana tsaye suka fito yayi musu jagora har waje inda Muhammad ya kunna mota, ya buɗe mata ƙofar baya Safina ta gyara mata ƙasan rigan ta bayan ta shiga sannan ya rufe, Safina kuma ta zaga ta shiga ta ɗaya bangaren.
"Madam yaya jiki?"
"Alhamdulillah da sauƙi" ta amsa muryar da bata tantance ba sai kuma don neman magana Muhammad ya juyo ya dubeta.
"Allah ya ƙara sauƙi"
"Malam kana ɓata mana lokaci" cewar Yaseer yana sakin ƙaramin tsaki.
"Allah ya baka haƙuri" ya juya yayi ma motan gear suka fara tafiya ya bar Reina da baki a sake.
Sai ta kalli Safina ko itama ta gane shi, yana nufin ranar ma ƙamshin nan ba nashi bane na Yaseer ne? Toh ranan a restaurant ɗinnan fah? Ko ta ji wanda yake amfani da irin shi ne?.
Wayoyin da Yaseer yake amsawa a kai-a kai ya saka ta haɗiye tambayoyin da take son yiwa Muhammad don taji kiran masu muhimmanci ne kuma da gaske a uzurce yake.
Har ƙofar shiga cikin gidan suka ƙarasa suka ajiye su, Umma ta fito ta tarbe su don Yaseer ya kirata tun a hanya, yace zai yi musu bayanin abinda ya faru idan ya dawo amma yanzu Reina ta samu hutu.
......
Daff maghriba Mahaifin Safina ya kira ya sanar da ita ta nemi abun hawa ta koma gida domin aiki yayi musu yawa yau ba zai samu dawowa da wuri yazo ya ɗauke ta ba. Magungunan da aka bawa Reina ya saka mata nauyin jiki da barci sai idan lokacin sallah yayi Umma ta shigo ta tashe ta amma abincin rana ma ɗaki masu aiki suka shigo musu da shi, suna zuwa ne kawai a ranakun mako daga Litinin zuwa juma'a saboda suna taya Umman ayyuka idan yaran gidan kowa ya shiga sabgar shi.
Har sun kusa gama cin abincin dare Yaseer suka shigo tare da Aicha gaba ɗayan su a jigace suke.
Kallo yabi mutanen wurin da shi yana amsa sannu da dawowan da suke mishi har ya sauƙe idanun shi a kanta. Yaga ta warware amma sai da ya sake tambayan ta yaya jiki.
Kallo sauran suka bita da shi domin basu da labarin tayi rashin lafiya kuma bata yi kama da wanda take jinya ba.
"Naji sauƙi sosai"
Umma ta amshe da "Idan da wani abu ba kace a kira ka ba? Tun da kaji shiru lafiya ne, Ku ƙaraso ga abinci"
"Nikam sai na watsa ruwa, jiki na babu daɗi" Aicha ta so itama sai tayi wankan suci tare amma Saudat ta tilasta mata ta zauna saboda tana son amfani da zaman da zasu yi da Yaseer suyi magana.
.
.
Sai da yayi wankan yayi nafila tunda yayi Isha a waje kafin ya fito cikin grey short sleeve T shirt da wando ya samu Umma tana jiran shi a dining da abincin da ta tanadar mishi a gaban ta.
Zama ta saka shi yayi ta shiga zuba mishi abincin da kanta.
"Yaseer" ta kira bayan yayi rabin abincin plate ɗin shi.
Har ya kawo cokali bakin shi ya sauƙe jin yanda ta kira shi ɗin da ainihin sunan shi ba da yayanmu da daman sune suka raɗa mishi ba.
"na'am Umma" ya amsa yana bata dukkan hankalin shi.
"Kana da yarinyar da kake so ka aura ne?"
Jiki a mace yace "mai ya kawo wannan maganan a yanzu kuma umma? Mu da muka sako muhimman abubuwa a gaban mu ga aiki a office kaca-kaca ina nake da lokacin soyayya a Yanzu?"
"Masha Allah, toh daman na tambaya ne saboda a fita hakkin ka, amma tunda kai baka da lokacin soyayya mu muna da lokacin zaɓa maka matan Aure don kaɗan ya rage maka ka shiga shekarun tsufa kaima."
Ta shiga wurin hoto a wayarta ta miƙa mishi sai ya tsaya yana kallonta cikin rasa abin yi "karɓi mana"
Ta tura mishi wayar a cikin hannun shi.
"Wannan yarinyar Goggo ne ta darje ta zaɓa maka a jama'are, ka ganta fara kyakkyawa wanke hannu ka taɓa ga nutsuwa da ilimi Masha Allah. Idan ka jawo hoton gaba kuma ƴar ƙawata ce Hajiya Sa'a ai ka santa tana yawan zuwa min, itama babu wani matsala idan kafi son ƴar gari kusa da mu. Idan kuma hazo kaso ketawa to ga ƴar Daddyn ku abokiyar ka, bani da matsala da duk wanda ka zaɓa a cikin su."
"Amma Umma ba mun yi sai mun kashe case ɗin mutanen nan ba na wanke kaina yanda duk gidan da zan je niman aure ba zasu bankaɗo wani abu marar daɗi a kaina ba a garin bincike?"
"Kada ka damu, duka sun san gaskiyar Abinda ya faru kuma sun yarda da nagartan ka, idan ma kana tsoron wani abu ya je ya dawo ne ba ga Wanda Mahaifin ta ya shige maka gaba ba? Ku sasanta kanku kawai ku sanya mu farin ciki kuma ina da tabbacin zaka ji daɗin zama da ita tunda taku ta zo ɗaya"
"Amma Umma..."
Saurin tamke fuska tayi jin yana niman jan magana cikin ɗan faɗa-faɗa ta katse shi, "Yaushe ka koyi gardama Yaseer? Kai ganin yarinyar nan Ameesha jiya da yaranta har biyu bai saka kaji komai ba? Ko Babana ya kai aure balle kai, da ace ƴammata ne ku na kusa in fara tarun auren jikoki, amma kun tare min a gida bani da aiki sai na ciyar da ƙattin samari, ko so kuke yi kuyi ta giftawa inyi ta kallon ku kullum kaman TVn da ba'a canza channel?"
"Kiyi haƙuri za'a yi yanda kike so" yayi ma hoton kallo ɗaya yayi swiping ya kalli ɗayan ma sannan ya maida mata da wayan.
"Sun yi, amma sai na samu lokaci zan fara zuwa in ga na cikin garin kafin in je jama'are"
ta sani daman bayi son ɓacin ranta ko kaɗan shiyasa tayi mishi haka don ta gaji da biye mishi yana daɗa jin daɗin reshewa, tunda ga wadata Allah ya kawo kuma mai za'a jira?
"Ko kai fa Yayanmu, idan duka biyu ma kun daidata duk mai yiwuwa ne. Idan kuma na gidan ta yarda itama ai zaman aure kowaccen su zata yi, duk na san zaka iya riƙe su in Allah ya yarda"
Waro idanu yayi "Mata Uku Umma?"
"Eh mana, kowa sai kayi mata nata gidan daban, yau ka sha kindirmo gobe ka ci tuwo jibi ka ci masa kaga komai yayi"
"Shikkenan Abbah ma zance yana buƙatar masa da kindirmo a rayuwan sa."
Da ƙyar ta iya hana kanta yi mishi danƙwale amma sai da bakin ta ya furta "kaci gidan ku"
Yayi dariya "Umma ɗaya ma ta isa, zuciya na mace ɗaya zata iya so bani son hayaniya, ba zan iya da rikicin mata ba."
"Amma da gaske baka son Aisha?"
Girgiza kai yayi "kada ma kuyi ta ji dan Allah, Darling ƙanwata ce"
"Ita kuma wancan yarinyar fa" ta tambaya tana gwada hanyar upstairs da baki.
"Hafsat?" Ya tambaya yana tunanin wani matsayi ɗaya zai iya bayyanawa cikin wanda take da su a gare shi.
"Ingancin rayuwar ta nake son gani..." ya buɗe baki kaman zai sake cewa wani abu sai ya mayar ya rufe ya kalli yanda Umman ta tsare shi da idanuwa ya saki murmushi.
"Kada ki damu na fasa zancen na Abban nawa kawai za'a yi."
"Ba abin in dake ka ba in ji zafi a hannu na, in watsa maka ruwa kuma in jiƙa carpet, don haka kaci kanka aure kuma sai kayi kwanan nan ma kuwa" da haka ta miƙe ta bar shi da ƙarin damuwa a kan tulin wanda yake fama da su, shi ta ina zai fara soyayya a yanzu har ya tsare yarinya yayi ta shirga mata ƙarya da alƙawuran da a gaba zai manta da batun cika su duk da sunan zance?.
......
*Reina*