← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 117

Sashe 27

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata ji shigowar shi ba ko sautin tafiyar shi a lokacin da yake nufo ta. Hannun shi kawai taji a jikin ta lokacin da ya saƙalo shi ya zagaye cikin ta sai ya haɗe jikin shi da bayan ta, tana daskare kaman gunki riƙe da maggin Knorr da ta fasa tana shirin zazzagewa cikin miyar.

Ƙamshin turaren shi mai shegen ƙarfi da ɗaga hankali ya shiga hancin ta, ta kai duban ta ga hannun shi dake ƙasan cikin ta zane da tattoo ɗin wani baƙin maciji ya faso kai.
"I'm back amarya ta" ya raɗa cikin kunnen ta warin taba ya biyo bayan ƙamshin.

Cikin seconds biyu komai ya faru, razanannen ƙaran da ta fasa da yunƙurin ƙwace kanta daga riƙon shi da tayi ya saka da Jamal ya sake ta ba shiri ta faɗi a ƙasan kitchen ɗin.

Ta juyo don tabbatar ma kanta ba mummunan mafarki take yi ba, idanun ta ya sauƙa a kan fuskar shi da yafi mata komai muni. Ya sauya, ya sauya sosai Amma a kan shi ta koyi riƙe kamanni, a sanadin shi ta samu wannan baiwar, don haka idan da furfura Jamal ya tsaya a gabanta zata gane shi.

Murmushi ya sake mata ganin tana mishi kallon sani, daman yayi tsammanin irin wannan tarban daga gareta kuma yaji daɗin hakan, sai kawai yaga tayi luuu ta kwanta a wurin sumammiya.

.....
*1 week ago*

A ɗarare ta daga ido ta dubi dattijon tsohon dake hakimce a babbar kujeran parlon da a duk lokacin da ta shigo cikinta ji take yi kaman tana barikin sojoji, tana sukwane a saman carpet ɗin da ya ɗaura ƙafafuwar shi ga sandar da aka mishi ta dogarawa jingine a kusa yanda tana wani wargi zai make ta dashi.

"Makirar yarinya ce wallahi general, ita da yaron suka ƙulla abin su suka sako Jamal a ciki. Ta bi ta samu Bilal ta faɗa mishi ƙarya da gaskiya, yanzu ma wai soyayya suke"

"Bilal ɗin?" Ya karkata kai yana kallon ta da mamaki.

"Ai sun kusa shekara guda ma, kuma alamu sun nuna auren ta yake da niyyar yi."

"Shine baki sanar da ni ba tun wuri Hauwa'u?" Taji muryar shi ya sauƙo a kan yanda ya fara mata magana.

Daman ta sani tana kawo maganar Uncle B na Jamal zai bi ruwa, don haka zata ƙara kambama abin yanda laifi zai koma kanshi duk irin soyayyar da ganeral yake mishi, ta shiga tsakanin shi da Reina dan idan suna tare sai dai nan gaba taga ana rabon dukiya banda ita. Tun tale-tale general ya danƙa ragamar dukiyar shi ma ɗa namiji guda ɗaya da ya haifa wato Bilal duk da ma Bilal ɗin yana masa wasa da hankali da yanzu shine a kan komai an wuce wurin, don haka Reina tayi kaɗan tayi mata shamaki da rabon ta.

"Ai yarinyar ma idanun ta a buɗe suke wallahi, rawar kai, rashin ɗa'a, Sata, ga yawon banza. Ya kai ga wata rana bata kwana a gida sai na saka an je an nimo ta"

"Ashsha ƴar iska dai kawai zaki ce"

Fuska ta a kwaɓe tare da jinjina kai har da ƴar ƙwallar munafurci "na san mutane ni zasu zaga saboda ni ke riƙon ta, ina iya ƙoƙari na a kan yarinyar nan amma abin nima yafi ƙarfi na, ƙarewar ta baƙin cikin ta ne ya kashe mahaifiyar ta, mahaifin ta ma ya kashe kan shi yanzu duk babu su amma yarinyar nan bata ji ya kamata ta gyara ba."

Yanda Hajiya Hauwa ke bayanin nan a idon general harsaso Reina yake yi daga shekaru ashirin da biyar zuwa talatin bai san ma ƴar shekara 19 ake wannan ƙazafin ba.

"Toh shi Bilal mai ya kai shi? Ina mishi kallon mai hankali?"

"Irin wa'innan ai sai dai basu saka idanun su a kan namiji ba, Idan suka ƙwallafa rai a kanka sai dai Allah ya kwace ka kawai. Shiyasa muka yanke shawara tare da wan mahaifin nata zamu haɗa ta da Ɗan uwanta Jamal tunda dai naka-naka ne ba zamu zuba mata ido ta ƙarasa lalacewa ba"

Cike da tausayin ta yace "toh shi yaro sai a ɓata mishi rayuwa? Ina shine kikace tayiwa kazafi?"

Ta ɗan yi ral-ral da idanu "Idan ba hakan muka yi ba karshe ita Bilal zai kawo maka a matsayin suruka, sannan zamu fi saka mata ido idan tana kusa da mu"

"Haƙiƙa kin yi kyan kyai Hauwa'u, lallai kin yi kyan kai, hakan shine maslaha. Allah yayi miki albarka shikuma Bilal ki bar ni da shi, babu wanda zai ce masa komai zai dawo ya same ni"

.....

*Yaseer*

Ɗokin kammala karatun shi suke yi sosai har sun ma fishi, domin gani yake yi ba wani abu na Musamman bane don mutum ya kammala degree na farko a shekaru 31. Don haka ko da suka ce zasu zo china ɗin sai ya ɗaura musu sati guda a kan ranar karramawan su, sai kawai hotuna ya tura musu yaje ya amshi kwalin shi ba tare da rakiyar kowa ba.

Aicha har fushi ta ɗauka dashi don taci burin irin hoton da zasu yi a ranar, irin styles da couples suke yi idan mata ko miji ya gama wani program. Zata saka hulan graduation gown ɗin shin ne a kanta shi kuma yana sanye da rigan, sai ta riƙe certificate ɗin da aka bashi shikuma ya riƙe flower bouquet ɗin da ta kai mishi a ɗauke su a haka su biyu.

Yanda zata ɗora a duk wata kafa na sada zumunta ta sake haukata ƴan online su tottofa albarkacin bakin su ko Yaseer zai lura ya fahimci dacewar da suka yi da juna, tunda yanzu tana da tabbacin abinda ke na gaba a gare shi aure ne, koda shi bai shirya ba toh iyayen shi zasu tursasa shi yayi.

Basu daddara ba da ya dawo suka haɗa mishi mini Party a Niamey. Babu yanda ya iya haka ya tsaya aka yi komai yanda ya dace ganin farin cikin dake fuskokin makusantar nashi harda wanda suka gayyayo su taya su murna ma, gashi daga gani sun kashe kuɗi masu yawa domin wurin ya ƙawatu sosai.

Sai ga ustazu Yaseer harda cashewa da babban riga a cikin ƙannen shi. Aicha yanda kasan amarya ko wacce zata je gasar kyau irin kwalliyar da taci, sannan duk inda Yaseer zai saka ƙafa tana biye dashi, ta ajiye fushin da take yi a gefe kuma Yaseer bai bata haƙuri ba tunda ya san babu abinda yayi mata.

Wani da amincewar shi wani ba tare da ya sani ba sai da ta samu aka ɗauka musu irin hotunan da take so. Ba tare da ta jira an watse a taron ba ta ɗaura hoton da suka yi suna tsaye tare a kan shafin Yaseer na Instagram, tiktok, X(Twitter), da Facebook ta wayar ta tunda duk tana da password ɗin shi, tana cikin masu managing social Media handles ɗin shi ma.

Ya gaji sosai a ranar don haka yana gama zoom meeting da jagororin wani Chinese Company da suke aiki tare tun kafin ya dawo ya saka wayar shi a silent ya samu gajiyan ya taimaka ma idanun shi suka rufe ba tare da ya san wainar da ake toyawa a duniyar online ba.

Ƙarfe 2:58 ya farka a razane ɗauke da salati a bakin shi. Jujjuyawa yayi ya tabbatar a gado yake kwance, ba ƙuntataccen ɗakin da tabarma ke raba jikin shi da dandamalin ƙasa ba duk sanyin ta da halittun dake samun abincin su a nashi jikin. ya tuna ɗaki, gari da kuma ƙasar da yake ciki kana ya sauƙe numfashi, yana sake nanata kalolin addu'o'i har ya samu nutsuwa ta sauƙan mishi, duk da dai har yanzu ya gagara tantance rayuwar shi ta baya ko ta yanzu wanne ne mafarki a ciki, dukkan su biyu rayuwar kasƙanci da na ɗaukaka babu wanda yayi dai-dai da tunanin shi. Amma koda na yanzun shine mafarki to yana godiya ma Allah da yasa yake samun sauƙin ƙuncin da ya shiga a cikinta.

Wayar shi ya jawo daga bedside drawer yana kallon lokaci. Yayi Sa'a sosai da ya samu barci wurin na awanni huɗu ba tare da ya sha komai ba.

Rasa abinda zai yi a lokacin ya samu kan shi da shiga wata ma'adanan hotuna da sai da lambobin sirri ake buɗe shi. Kwanan watan haihuwar ta ne lambobin sirrin, yana rubutawa kai tsaye aka shigar da shi yanda hotunan ta suke jibge a cikin wayar. Tun daga kan na gama secondary ɗin ta, na gama Islamiyya, na matriculation da na ranar da suka yi kwalliya suka je restaurant ɗin nan, duk mahaifin Safina ke turo mishi ko ya buƙata ko bai buƙata ba kuma bai taɓa dakatar dashi ba hakan ya fahimtar dashi cewa yana buƙata ɗin.

"Nan da one week zan haɗa ki da Mahaifin ki Hafsatu Reina. Ina takaicin idan rayuwa ta sake miki daɗi zaki koma gidan jiya"

Shigowar saƙon wani abokin karatun shi ɗan Japan ya saka shi buɗewa babu shiri ganin Abinda ya rubuto.

'Congratulations on your wedding YK'

Ba shi kaɗai ba, mutane da yawa sun turo mishi saƙonnin da ya samu kan shi da karantawa ɗaya bayan ɗaya, wasu da basu da Wani kusanci suna mishi murnan angwancewa ne kawai kaman na farko, wanda suke jin su na jikin sa ne kuma tuhumar shi suke yi yayi aure babu gayyata.

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*

61

Tun da ta farka ta tabbatar da gaske Jamal ne ta gani ba wani aljanin mai kama dashi ba ta rufe kanta a ɗaki ta nemi wuri a sanyin tiles ta ƙudundune jikin ta tana kuka. Tayi kuka har tana shiɗewa, daga inda take tana hango maganin da Uncle B ya tilasta mata ajiye shi a kusa, amma gwamma ta mutu da ta dai wayi gari da wannan iblis ɗin a cikin gida ɗaya.
Chapter 27 · 0% Book details