← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 117

Sashe 52

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ayyah" tace tana jin haushin maganar shi, to ita ina ruwanta koma wurin wa zai je?.

"Baiwar Allah da hassada ne?"

"Kayi kyau" tace tana mayar da duban ta jikin window don ta ji bata son sake kallon shi ma.

Kamar wanda ake mintsinar shi sai ya shiga mata labarin budurwar shi sai can kuma yayi shiru kafin su isa duk ya gama ƙular da ita, don haka suna isa ta fice ba ko godiya ta banko mishi ƙofar motar ta wuce gidan kakanninta fuuu.

Murmushi mai ƙayatarwa Yaseer yayi daɗi na ziyartan shi ganin ta gwada kishin ta a fili. Sai a lokacin ma yaga yanda ta manna mishi man laɓɓen ta a jikin window.

"Ba dai zaki shiga tsakani na da babe ɗina ba yarinya" yace yana ɗan datsa laɓɓen bakin shi.
.
.
Lokacin da Yaseer ya isa Gidan Hajiya Sa'a ƙarfe 6 saura don sai da yabi wani wurin kafin ya je. Yarinyar ta Falila tayi jira har ta cire rai, gaba ɗaya takaici ya kamata yanda taci ado har ta gaji amma Yaseer ya shanya ta.

Saida suka gaisa da Hajiya Sa'a ƙawar Umman shi Sannan aka basu wuri su zanta da Falila. Yana cikin yanayi mai daɗi don haka yayi ƙoƙarin ganin sun ɗan zanta dukda bayi da niyyar dawowa, yanzun ma umarnin umma yabi amma sai wani fiffizgewa Falilan take yi tana masa big time.

Murmusawa yayi shima ya ja bakin shi yayi gumm ya ɗan taɓa Abinda aka kawo mishi sannan ya ajiye mata tukuici ya miƙe zai ƙara gaba, sai a lokacin yaga tashin hankali ƙarara a kan fuskar ta.

"Yaya Yaseer har zaka tafi kuma?" Tace tana kwaɓe fuska irin yanda Aicha take yi yake bashi dariya ɗinnan don haka ya sake murmusawa.

"Toh me zan yi miki My sister, kinga maghriba ta gabato zan tafi in bi jam'i. Ganin tana so ta bijiro masa da sabon iyayi ya ciro wayan shi ya saka a kunne yayi hanyar fita.

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

79

Saida kiran ya kusan tsinkewa ta ɗaga kaman mai ciwon baki tace "Hello"

"Idan kin gama Abinda ya kai ki gidan Ummin ki shirya after maghrib dan zo in ɗauke ku"

"Ka bari kawai zan hau napep"

"Cewa nayi dan zo in ɗauke KU ba ke kaɗai ba, idan baki hawa motan sai in ɗauko Maama in dawo"

Zuzzumɓura baki tayi sanin bayi ganinta sannan ta amsa da "sai ka zo"

Shi ya katse kiran don yanzu tsoron ɓata masa rai take yi kuma a take ta shiga haɗa komatsen ta.

.....

"Kuma fa saboda shashanci ko sabon numbern tan basu karɓo ba" Hajiya Hauwa kenan take mayar wa Hajiya Lubabatu da Hajiya Jummai yanda aka yi zuwan su Zahra gidan su Yaseer jiya.

"Amma kunga Tahir ɗin da idon ku?" Ita har yanzu bata gaskata cewa wai Alhaji Tahir bai mutu ba, sai dai idan hala wani mai kama da shi ɗin suka samo.

"Ina fa! Kinga yanda Wannan Yaseer din ya kasa ya tsare? Wallahi jiki na har rawa yake da nake magana yana tsaye a wurin, idanun shi kaman mashi idan ya zuba maka su. Ni na kasa yarda ma yaya Yaseer ne dai da ya koya mana karatu a gidan nan, ya canza ya zama wani babban mutum sosai fah" cewar Zaheera.

"Ga kuɗi kuma" Zahra ta amshe, sannan ta juyo da wayar ta tana gwada ma Hajiya Lubabatu "kinga networth ɗin shi."

Karɓan wayan Hajiya Lubabatu tayi tana mamakin wai har duniya ta san da shi, Hajiya Jummai ma ta muskuta ta miƙa wuya tana leƙawa.
Ɗan hoton shi da ya bayyana a ɗan wani akwati ta fara kalla, a wurin wani taro aka ɗauke shi domin ga tambarin UNICEF ya fito ɓaro-baro a bayan shi, yana magana ta cikin mic dake saƙale daga bayan wuyan shi zuwa bakin shi. Sannan ta koma kan bayanin da Google ya bayar kafin hoton, Zahra tana karanto mata ba don ita bata iya karatun ba, sai don bayanin ya daɗe da zama a kanta. "..Kuma kullum ƙara gaba yake yi, A yanzu yana gaba-gaba cikin sahun matasa masu arziƙi a africa, don kudin shi ma ba a Nigeria ya fara tarawa ba, sannan a kan mutane yake investing fiye da kaya don haka competition a kalan kasuwancin shi yayi ƙaranci. yana yawan cewa 'babu arziƙin da ya kai mutane, babu abinda ya kai ɗan Adam daraja a duniya, sannan duk wanda ya karrama wani mutum kan shi ya karrama'. Kinga kuwa samun masu karawa da shi su toshe masa hanyar samu yana wuya"

Tana dasa aya Hajiya Lubabatu tana gama karantawa don haka ta saki dogon ajiyan zuciya.
"Toh a dalilin mene zasu ɗauki Tahir su ɓoye shi bayan idan ma fansa ne abinda yake son ɗauka ai a kan Tahir ya kamata ya fara ɗauka kafin Jamal, Tunda Tahir shine ya wulaƙanta shi" ta ƙarashe tana watsa hannuwa.

"Nima haka dai na gani Addah" Hajiya Jummai ta amshe. "Tahir shi kaɗai yayi abinda yayi babu wanda ya taya shi kuma bayan ƴar shi, idan ma akwai wanda za'a saka a rufe to sune"

"Hmm kin san akwai abokin shi ɗan Nijar ɗinnan baƙin munafiki shi ya kawo shi, kuma saboda tsaban tozarci da wulaƙanci sai da suka bari a ranar da muka tara jama'a, munafikin Allah shima ya karɓi sadakin a maimakon ya tsaya tsayin daka sai an dawo mana da kayan mu magana ta mutu, ashe gadar zare yake shirya mana"

Hajiya Jummai tace "Ni ba wa ni aka yi ba amma kunyar shiga jama'a nake yanzu, labari ya baɗe ko ina kamar wutan daji."

"wallahi ƙofar gida yanzu zan fita sai na saka niƙab, shima fitan sai ya kama dole har aikina na ajiye, da girma na da mutunci na rana ɗaya an saka ni a uku"

Hajiya Lubabatu ta ja dogon numfashi tana jin inama inama lokacin nan ita ta karɓi Reina? Abinci da wurin kwana dai ba zata gagara bata ba shikkenan ta ajiye ta kowa yayi rayuwar shi, da yanzu tana cikin alkhairi sai dai tayi ma su Salisu Sorry daga nesa. Allah dai yasa Tahir ba kuɗin goro yake da niyyar yi musu ya ci uban su ba.

Ta dubi Hajiya Hauwa da ta wani rame ta jeme tayi baƙi kaman ba ita ba "To yanzu menene abun yi?"

Tagumi ta saka tana kwaɓe fuska kaman zata yi kuka. "Ni yanzu ina na sani Hajiya Addah? Shine ma muka ce su je su sami yarinyar su lallaɓata ta haɗa mu da Tahir ɗin toh kinga dai yanda abu ya juye".

Cikin tashin hankali Hajiya Jummai ta hayayyaƙo mata "Toh haƙura zaku yi? Ina nan muke jinjina muku ƙoƙarin da kuke yi a kan yarinyar nan? Ba'a baku sisin kwabo ba amma makarantar ta ɗaya da yaran ku sannan Salisu ko ƙifta ido bai yi ba balle jinkiri ya sanya ta a jami'a!. Toh wannan bai ishi Tahir ya durƙusa ya gode muku ba ma dukda yanzu ba ƙafan?"

Zuru-zuru Hajiya Hauwa tayi ganin fa da sauran tonon asiri idan Reina kuskura ta buɗi bakin ta, don ma tana da yaƙinin secondary da Islamiyya bata da wani wayo hala ta manta amma na jami'a yanda suka tubure har su Ummi sun san ba su ke da alhakin sanya ta ba. Toh ko Tahir ɗin ne da kan shi ya biya mata ta bayan fage? Koma wannan mayen ƙanin tan ne Bilal tunda ance har yanzu suna tare? Kuma taji zancen zuwa a nimo mishi auren ta a bakin yayar ta Maryam sannan general ne zai shige masa gaba da kansa.

Hajiya Lubabatu da ta fita sani a kan ainihin gaskiya tace "da dai an bi lamarin a sannu har a warware shi, kin sani tun daa Tahir idanun shi a rufe yake a kan abinda yake so"

Matsowa kusa Hajiya Jummai tayi lokacin da wani Idea ya zo mata ta miƙo wuya kaman jimina sannan tayi musu alama da suma su sako kai don bata son su Zahra su ji abinda zata faɗa "Shiyasa ai ko kidnapping ɗin yarinyar zaku iya sakawa ayi har sai an fito muku da ɗan ku, kuma mu saka kuɗin fansan da zaku raba faƙirkin yaron nan da Abinda ya mallaka baki ɗaya dan ko dacewa da arziƙi bai yi ba wallahi, sun fi kalan maula tafi karɓan su..."

Hajiya Lubabatu bata ji ƙarshen zancen ba ta ɗago tana hararar ta, Amma Hajiya Hauwa Nazarin shawarin take yi kaman zai basu mafita. Idan suka yi haka za su fito da Jamal sannan su samu kuɗin da zasu maidawa Alhaji Tahir ya rabu da su, jifan tsuntu biyu kenan da dutse ɗaya.

"Na san abinda kike tunani, ba jifan tsuntu biyu da dutse ɗaya bane ƙara nutsa kan ki zaki yi a cikin bala'i. Don haka ajiye shawarar nan a yanda kika ɗauke ta ko in tsame hannu na daga nan".

....

Dariya Safina take ƙunshewa ta hanyar tura gurasar da suka je suka siyo yanzu cikin bakin ta, amma saida dariyar ya kufce mata.

Reina ta kalle ta baki sake "ok wato damuwata shine abin nishaɗin ki?"

"Toh ai cikin damuwowin kin ne babu na gaske, daɗi kike ji wallahi"

"Uncle Bilal fa rabon da muyi waya kwana biyu kenan yayi fushi, shima yaya Yaseer ɗin ba gane ma kansa nake ba har yanzu, saidai shi da ƙawar shi su zauna su cika mun kunne da faransanci yare kaman zaka yi kaki"

Safina ta sake tuntsirewa da dariya. "Haushin rashi ya saka makaho cewa ido da wari dai"

"Hmm" Reina ta taɓe baki itama ta saka hannu cikin laidan gurasan tana ci domin bata ga laifin Safina ba tunda ita ta kawo mata matsalar ta.

Saida Safina ta dara son ranta sannan tace "Amma kin bashi haƙuri?"

"Uncle Bilal ɗin?"

"Me kika yi mishi da zaki bashi haƙuri? Yaya Yaseer dai nake nufi"

"Shima me nayi mishi da zan bashi haƙuri? Fushin babu gaira ba dalili yake, kuma ma ai ya gwada komai ya wuce daga farko"
Chapter 52 · 0% Book details