← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 117

Sashe 14

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariyan mamakin ƙarfin halin ta ne ya suɓuce mishi "ai ko? To ita yarinyar fa? Ita ta kai kanta wurin Jamal?. Ba fa rayuwar mutum ɗaya kuka tagayyara ba, kunyi ma mutane uku illar da har abada ba zasu iya warkewa ba saboda son zuciya, don harda ɗanki kuka cuta. Tabbas nayi niyyar sanar da general a take, Amma babu amfanin hakan saboda Abinda ya samu yaron, tona sirrin ki babu amfanin da zai yi min ko ita yarinyar sai ma ya daɗa saka ta a wani hali." Ya miƙe tsaye har yanzu tana gurfane a gaban shi.
"Kunyar duniya kenan na idon mutun ɗaya Addah Hauwa, ina ga mun je ana bayani a gaban Allah? Don haka tun wuri ki saka Jamal ya dawo gida tun lokaci bai ƙure miki ba ku gyara abinda kuka lalata, zan baki zuwa in tafi in dawo, na sake saka ƙafana a Nigeria ko kin shirya ko baki shirya ba sai mun kai karshen zancen nan, kuma zan sanar da general" da haka ya juya ya bar mata gidan.

.....

Kwanan Reina 4 a gidan Ummi da kanta ta shiga haɗa kayanta zata koma gidan Hajiya Hauwa ganin Uncle B bai dawo ɗaukanta sun je ganin Yaseer ba, gwamma ta koma kusa yanda da yazo sai tafiya.

"Ba kince baki son komawa gidan ba?" Baba ya tambaya.

"Na fasa ina so" tace tana goya jakarta a baya.

Ummi dai kallon ta take yi tana nazarin yanda ta dawo wani sanyi-sanyi kwana biyu. Lamarin hafsatu dai sai ita, ba ita tace musu tana shan wahala bata jin daɗin zaman gidan ba amma gashi kwana biyu duk ta gagara sakewa zata koma musu, kuma har abin daɗin da take cewa ba'a bata sun biyo ta dashi taƙi ci. kula da ita ne kawai basu yi yanda ya dace amma su ai ba zasu gaza ba.

Haka aka mayar da ita gidan Hajiya Hauwa taci gaba da zaman jiran tsammani.

Uncle B Dawowar da bai yi gidan ba kenan tunda ya samu ya gujewa tarkon general da yayi mishi takunkumi saidai yayi short service ya shiga aikin soja kaman yanda suka yi yarjejeniya, ya ƙwace passport ɗin shi, yace matar shi da ɗan shi ma saidai suzo nan su same shi. Da nashi damuwar ya danne shi sai ya manta da na Reina, ya dai samu uwar riƙon shi ta taimaka mishi ya tsere da saka ran ba zai dawo ba sai general ya sake hucewa tunda ba yau suka fara kafta wasan ba, duk dan ya guje ma yin sojan ya shiga karatun likitanci a tunanin shi tunda kafin ya gama tsufa ya ƙara kama general zai hakura.

Daga farko yanda Hajiya Hauwa take treating ɗinta a gidan ya canza saboda tsoron ranar da Uncle B zai waiwayeta, amma da ta samu labarin abinda ya faru sai ta saki ranta don ta san juyowar shi ba kwanan nan ba, kafin nan zata san yanda zatayi wa tufkar hanci.

Saidai a hankali Reina take canzawa, ance hankali yana zuwa wa mutum ne da shekaru amma nadama ya fara kawo nata. Duk abinda take yi na rayuwar yau kullum da abinda take ci, makaranta, matsuguni mutanen da suke zagaye da ita sai ta kamanta su da Yaseer, sai taga ashe ma ba wahala take ji a gidan su Zaheera ba wanda ta jefa Yaseer a ciki ya ninka shi wurin sau ɗari. Yaya Yaseer ɗinta.

Sannu a hankali lokaci yake tafiya, kaman ma da gayya yake saiɓi ma Reina don ya san tana zaman jiran Uncle B kuma bata da hanyar samun shi.

A hankali ta rage rashin ji, rawar kai, har kalaman da take ambata ya fara ƙaranci a bakin ta. Yanzu idan naman jikin ta hajiya Hauwa zatayi kilishin sa ta cinye bata yi mata musu domin tana ganin ta cancanci hakan, ba komai bane a kan abinda ta jefa Yaseer a ciki.

Da sauyawar yanayin ta ya tsananta Ummi sun yanke shawarar ɗaukan ta koda na wani lokaci, har itama Hajiya Hauwa ta yanke shawarar barinta ta tafi don ganin ta a kullum babu abinda yake ƙara mata banda baƙin ciki da ɓacin rai amma ita taƙi tafiya, kada Uncle B yazo har ya tafi bata sani ba.

Sai dai shi ɗin bai manta da ita ba, ya gagara tsame hannun shi a cikin lamarin ta, duk wani hidima tata yana taimakawa da aljihun shi, duk bayan wata biyu yake turo ma Hajiya Hauwa kuɗin da zata ke bayarwa kakannin Reina ayi mata hidima don a tunanin shi yanzu sun maida ta gida, zai turo kuɗin kayan sallan ta da nasu Zaheera duk azumi, haka ma Alaji Abdou yake turowa ma ita da Maama, kaya masu kyau da tsada iri ɗaya da Aicha Mariama take zaɓa musu sai dai kala ko design ya bambanta, amma idan aka kawo sai ta ɗauka ma yaranta wanda yayi musu su canzo sauran da masu sauƙin kuɗi a kai gidan Ummi tunda sun san da kawo kayan ba dan haka ba shima ko labari ba zasu ji ba.

~~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

51

~~~~~~~~~
_Colder than your father's eyes_
_He never learned to sympathise with anyone _
~~~~~~~~~~

*Bayan shekaru 5*

"Ke ina Reina?"

"Wa ke niman ta?" Wata murya mai sanyi ta faɗa daga bayan wannan budurwar.

Da sauri ta juya ta fuskance ta.

Siririya ce doguwa tana da dara-daran idanu, ga ɗan murmushin da bayi wuce yaƙe a saman fuskar ta. Hannun ta Safina ta riƙo sannan ta shiga janta tana biye da ita kaman raƙumi da akala.
"Ina kika shiga ana ta niman ki za'ayi hoto?"

"Da kun yi kayan ku kawai kun san I'm not photogenic"

"Idan an ɗauka sai ki shiga ki goge kanki a ciki"

Ƙaraso da ita wurin da masu irin graduation gown ɗin dake jikin su suka jeru tayi, ta sama mata wurin tsayuwa itama ta tsaya a gafen ta aka ci gaba da kashe musu hasken camerori da wayoyi. Da ƙyar ta samu ta sake sulalewa dan su basu gajiya in dai hoto ne sai a kwana ana yi.

Ta koma ajin da babu kowa a cikin sa ta zauna ta ƙare masa kallo a karo na ƙarshe. Yanzu kuma daga nan ina rayuwa zai sake jefa ta? Zata saba da inda zata je?.

Wurin yana ɗauke kashi mai girma na cikin damuwowin ta, idan tayi nesa da gidan Uncle Salisu karatu da ayyukan aji suka yi mata yawa ne kawai take rage tunanin Aunty da Yaseer, shiyasa har ta sauƙe a Islamiyya bata bari kowa ya sani ba ta ɗora da hadda gashi shima yanzu saura ƙiris, don ma ba tare da sauran tsaran ta take tafiya ba da ta kwana biyu da haɗawa shima.

Ta shafa kan desk ɗinta da ta rubuta sunan ta a jiki da baƙin biro. Hafsatu Reina Tahir, tayi dariya tunawa da har zata rubuta TK Kingdom a lokacin ta fasa. Da Safina ta gani itama shine ta rubuta nata sunan a ƙasan na Reina da blue ɗin biro. Itama da tazo ta gani sai ta zana heart a ƙasan sunan Safina da baƙin biro, sai itama ta zana irin shi da blue ɗin biro a saman na Reina.

"Missy ƴan gidan ku sun zo" Safina ta shigo da murna ta sanar da ita.

Itama Reina da hanzari ta fita ta tarar da su Ummi tsaye a jikin motar Uncle da na Baba. Harda su Aunty Aina, Aunty zeenat da Aunty Sajeedah ga Uncles ɗinta ma duka sun zo kowa na ɗauke da gift ɗin da aka yi wrapping ɗin shi. Sai farin ciki ya lulluɓeta, ta ƙarasa tana rungume su ɗaya bayan ɗaya suna taya ta murna.

Flower bouquet da aka yi da kuɗi ƴan ɗari bibbiyu suka miƙa mata, haka suka gani ana yi yanzu kuma basu kuskure ba domin kusan duk sauran ma da irin shi a hannun su, sai dai wanda aka yi nasu da dubu-dubu ma kaɗan ne sauran duk dollars ne, amma bata damu ba kuma koda basu kawo ɗin ba bazata damu ba, zuwan su yafi mata komai ganin itama kamar kowa tana da wasu dangi.

Safina ta ƙaraso suka gaisa sannan ta gayyace su wurin hoto.
Aka fara ɗaukan su tare gaba ɗaya harda Safina kafin aka koma yi ɗaya bayan ɗaya tare da Reina.

"Ina Maama?" Ummi ta tambaya.

Barin dubo ta, Safina ta faɗa tana barin wurin zuwa ajin su Maama. "Zainab Tahir Kamal!" Ta ɗago daga kan English novel ɗin da take karantawa ta dubi Safina kawai. Ita kaɗai ne a class ɗin duk sauran sun tafi kallon masu graduation.

Ta ƙaraso ciki. "Me yasa baki zo kunyi hoto da yayarki ba tun ɗazu take niman ki?"

"Haka kawai" ta mayar da hankalin ta kan karatun ta don ta ɗauka wani abu mai muhimmanci ne.

"Na yau kaɗai ba zaki ajiye baƙin hali ba yarinyar nan?"

Banza tayi mata. Bata da lokacin jin haushin ta a yau don haka tace "idan Kinga dama Kizo ana niman ki" da faɗan haka ta fita ta barta.

Safina na komawa wurin ta samu itama iyayen ta da ƴan gidansu sun zo. Itama bouquet ɗinta da 1 dollar aka yi mata kuma yafi na Reina girma, don haka da aka fara daukan su a hoto sai ta sauya musu cikin dabara Reina bata lura ba.

Gudun ɓacin ran Ummi kawai ya saka Maama ta tsaya aka yi musu hoto su biyu da Reina, ita kuwa harda ɗan ranƙwafowa ta dafa ta tare da sakin murmushin gaske, hala rabonta da ɗaukan hoto tare da ƴar uwarta tun suna yara da iyayen su suke musu, lokacin Reina ne mai tirjewa Maama ke murmushi.

Zuwa wani lokaci duk sun yi luƙus, amma kowa yaci ya ƙoshi, don haka yan uwa da dangi suka fara tafiya kafin su kuma sai bayan an tashi idan sun yi sallama da abokan su, sai an haɗu a neco kuma.
Chapter 14 · 0% Book details