Sashe 114
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarasa tauna abincin bakin shi yayi ya kora da ruwa idanun shi a kanta yanda zama mai kyau ya gagare ta kana yace "Umry a ina kika koyi girki haka?" Ina kuwa bayan gidan yayan ubanta da tana so da bata so? "oh my god this is one of the most delicious food I ever tested Wallahi, har fa saida na manta yanda ake tauna!" Ya kai loma na biyu yana lumshe idanu.
Sai bakinta ya gagara rufuwa ta shiga washe shi kamar gonan auduga da ƙyar ta samu ta saka abun kirki a cikinta tsabar farin ciki
Ya jinjina kai "Wow ashe dai taya ki da su Maihakuri suke yi su suke ɓatawa, nima dole ki koya min kalan naki"
Ta ɗauka daɗin baki ne amma yanda taga ya zage ya ci abincin ya saka ta farin cikin da ba zata iya misaltawa ba, sai taji kaman tana yawo a saman gajimare kuma bata jin har tsufa ta kama su zata manta da wannan Ranar.
Tayi mishi rakiya cike da annashuwa suka rabu kaman zata zubar da ƙwolla dukda ya shaida mata Isha a gida zai same shi tunda zai bi office.
Komawa tayi ta tattara abubuwan da suka ɓata ta tsaftace su ta tsaftace kitchen ɗin, kayayyakin da zata yi amfani da su anjima ma ta fito da su ta tsaftatace ta yayyanka ta ajiye a fridge yanda tana zuwa sai ɗaura sanwa sannan ta fito ta samu missed calls ɗin Safina guda hudu a wayanta da ta bari a parlo, babu ɓata lokaci ta mayar mata da kiran tana yin sallama bayan an dauka.
"Ke banza gani a hanyar gidan ki result ya fito!"
Saida taji gabanta ya faɗi ta dafe ƙirji tana fadin "Dan Allah? Toh yaya? Ina kin duba min?"
"Eh fa, carry overn ki biyu nawa ɗaya"
Ta waro ido, "Da gaske? Dan Allah kada ki tsurar da ni" daman ta daɗe da sanin ba karatun ka ke hawar da kai ba sai Sa'a da kuma addu'a amma idan aka ce ta samu carry over a wannan semestern malaman nan sun cika azzalumai bayan lokacin da bata ƙoƙarin da ya kai haka ma bata taɓa samu ba.
"Hmmm gani nan dai na shigo unguwan kun, yanzu zamu ƙaraso" Safina tace tana kashe kiran.
Tayi tunanin ita kaɗai zata zo sai gasu har su uku. Suhail, Safina da Maama.
Ta zauna a gefen Safina tana leƙa wayanta ta ga carry over ɗin, bayan sun gaisa ta ce Maama ta shiga ta kawo musu ruwa.
Result ɗin Safinan ta fara gani ita da take da carry over ɗaya don ta shirya ma abinda zata gani a nata.
"Auu, ashe ba CO bane sai naga kaman ita ce a nan" cewar Safina tana gwada wani course da taci C, bayan sauran ruwan A's da B's ne, C ɗin guda biyu ne. Ga GPA ɗinta 4.12. saida aka raba a CGPA ne ta sauƙa 3.75.
Ta rungume ta cike da murna "Masha Allah Feenah, na taya ki murna wallahi nima ki duba ko CO ɗin guda ɗaya ne baki kalla da kyau ba"
"Toh bari mu gani" tace tana fita daga profile ɗinta ta saka registration numbern Reina tayi log in ta bata ta duba.
Ihu taso yi ta toshe bakinta ganin Suhail, ta juya ta kai ma Safina duka a kafaɗa "Amma wallahi kin tsorata ni ƴar rainin sense. 4.5 ni Hafsatu first class fah" tace tana dariya. "Alhamdulillah! Allah na gode maka bari in faɗa ma yaya Yaseer ina zuwa" ta miƙe da wayan Safina tana laluben layin mijinta a nata wayan domin wannan Nasara tashi ce, ba don shi ba ba zata taɓa samun haka ba.
Tana ƙulewa Suhail ya dubi Safina yace "sorry, tayi na karshe, na gaba ƙararta zamu kai"
"Ƙara? Ramawa dai zan yi, tsoronta nake ji?"
"Matar babban yaya ne fa" yace yana kallonta a kaikaice.
A ƙasan maƙoshi tace "to ni ina ruwa na."
Can sai ga Reina ta fito tana ta faman fara'a ta miƙo mata wayan. "Dole ne ma in baki tsaraba tunda kika kawo mun wannan labari mai daɗi"
Ta dubi Suhail da ya miƙe tsaye "Yaya kada dai har tafiya? Ko girkin auntyn kun baka ci ba"
"Office zan wuce kafin yayanmu ya fara nima na, zan dawo da yamma in ɗauke su."
"Toh Allah ya kaimu" Reina ta amsa zata mishi rakiya bakin ƙofa, ya juya yana kallon Safina amma sai tayi kaman bata san yana yi ba ai rakiyan matar gidan da suka zo wurinta ya wadatar, haka ya haƙura ya tafi.
Sai da Reina ta rufo ƙofa ta dawo Sannan Safina ta ɗora a kan maganar su. "Ai ko babu labari kin san bani tafiya ban karɓa ba don haka shiga ki fito." Ma'ana ta shiga ta ɗauko tsarabar ta kawo mata. "Kuma kin san tunda result ya fito an koma makaranta ko? Don naga wannan zancen kaman bayi gaban ki kina shan amarci ne tukun, Yau-yau ɗinnan aka fara registration, banda ma abun ATBU hutun wata guda saida aka ƙara masa wata biyu da sati ai da yanzu semester yayi nisa"
"Ai ni sun kyauta mun"
"Iyi tunda gashi har kin fara maida kumatu"
Tayi murmushi tana shafa kumatun da ake ta cewa tayi, dole ai tunda kalolin abubuwan da ta saka a cikinta bata san adadin su ba.
Hira suka sha sosai suka taya ta ayyuka da ciccire tsaraban kowa. Reina ta bawa Maama nata da na su Ummi da sauran ƴan uwa na kusa da na nesa wanda rabon su ya tsaga. Safina kuma aka bata nata da na iyayenta da ƙannen ta. Bayan la'asar Suhail ya zo ɗaukan su shima aka bashi nashi. Saida Yaseer ya dawo yaci abinci kafin wuraren ƙarfe tara na dare suka tafi kai na su Umma da Daddy, suma sun ji daɗi sosai kuma sun saka musu albarka don harda na goggo Halime da na mahaifiyar Umma. Maihaƙuri yayi godiya Alhaji Irfan ya kasa ya tsare.
........
A birkice Hajiya Hauwa ta shigo police station din tana raba idanu. Kallo ɗaya zaka yi mata ka hango uban ramar da ta ƙara a kwana biyu kacal, idanunta sun faffaɗa karsashi da taƙama da dukiyar nan duk babu. Yanzu haka ma a napep tazo don lokacin da ta kwanta jinya motar ta Alhaji Salisu ya ɗauka ya siyar ya biya mata kuɗin asibiti da magani shima ya ƙara ma lawyern sa appearance fee na tsawon lokaci tunda Shari'a ta ƙi ci taƙi cinyewa kuma a yanzu bai ajiye ba bai bawa wani ajiya ba.
Salati ta sake lokacin da ta hango Zaheera a bayan kanta da fasasshen goshi ta since ɗankwalin kanta ta yafa tunda ba fita da mayafi suke ba dama.
Ta ƙarasa wurin ɗan sandan dake wurin wanda yayi mata kalan marasa mutunci ta fara gaida shi. Ya gwada Zaheerah yana faɗin "Hajiya kece mahaifiyar wannan ɓarauniyar yarinyar?"
Hajiya Hauwa ta ɗaga ido tana kallon Zaheerah da ta kawar da kai tana gumm da baki sannan ta amsa da "ni ce officer. Amma saidai akasi aka samu ƴata bata sata"
Ba wai bata sani bane ta sani, ta daɗe da sani kuma ta daɗe tana rufewa ta hanyar ƙala ma Reina sharrin duk abinda aka nima aka rasa a gidan musamman kuɗi. Zahra ita yaran masu kuɗi ƴan duniya da masu idanu a buɗe take bi saboda suyi mata hidima kuma su saka duniya ta san da ita, amma Zaheera mace ce da idan tana son namiji saidai tayi mishi hidima ta kashe mishi kuɗi, tayi snatching ɗin samarukan ƙawayenta da yawa a irin haka su kuwa suyi ta using ɗinta tunda ganin mara sanin ciwon kai suke mata, sannan idan ta ɗaura idanu a kan abu yayi mata ko bata da halin mallakan shi sai ta samu. Shine ya kaita ga yin sata a supermarket wanda wannan shine karo na biyu.
"Tunda ƙarya zamu yi miki sai kiyi tafiyar ki, su wa'inda suka saka aka kama ta zasu yi handling ɗinta da kyau sai tayi aman kuɗin kayan su da ta ɗiba"
Ganin wankin hula zai kaita dare ta lallaɓa shi ta yarda zata biya kuɗin kayan sannan aka yanka mata kuɗin beli shima saida ta koma gefe ta kira wata kawarta da ta ɗauka da ƙyar ta ara mata 50k tazo ta biya aka bata Zaheerah suka tafi. A yayin da suke zaune a bayan napep dake nufar hanyar gidan su na yanzu suka yi shiru kuma tunanin Reina duka suke yi a lokaci guda.
Zaheerah tana nadaman shirin da suka fara suka tsaya a hanya da yanzu yanda gidan su ya rikice itama saidai ta koma gidan su yaseer ta zauna domin bata jin zata iya jure bala'in talauci da matsin da suke ciki, har ciman su da komai ma ya canza dole ma ta nima ma kanta mafita ne kawai, ga Reina can tana cikin rayuwar daula da jin daɗi.
Hajiya Hauwa kuma Reinan take tunawa amma ta rasa takamammen lokacin da zata tuna game da ita. Lokacin da ta saka Alhaji Salisu ya amshi riƙon ta ne ko lokacin da ƙaddarar da ya canza rayuwar su duka ya auku ko kuma tun lokacin da ta fahimci Jamal yana cutar da ƴar uwar sa amma bata yi komai a kai ba?. Da ace ta ɗauki mataki a lokacin da hala rabin masifar da suke ciki bai faru ba, domin da yanzu Jamal shi zai zame mata sanyin idaniya, shi zai taya ta ɗaukar nauyin ginin da uban shi ya rikito a kan su. Da duk rintsi zata ji sanyi ta wani wurin.
.......
A haka kwanaki suka fara tafiya ma Reina da Yaseer kaman kowanni sabbin ma'aurata, kullum yana fita aiki a weekends kuma zai zauna su samu lokacin juna kuma bayi ƙyashin taya ta hidiman gida, suna yi suna hira nan da nan sai kaga sun ƙalƙale komai da ko ina shima ya samu lokaci da nutsuwarta yanda yake so.
Bayan sati ɗaya ta koma makaranta, saboda reopening ɗin attempted rape case ɗinta da Yaseer yayi ya saka babu wanda ya tunkare ta da maganan saboda yanda zancen ya ɗau zafi kowa ya zuba ido da kunnuwa yaji yadda makomar Shari'an zata kasance.