← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 117

Sashe 67

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta samu Yaseer a parlon sama babu Abinda yake yi bayan jiran ta tunda yana da tabbacin zata zo. murmushin gefen baki ya saki lokacin da ya sanya ta cikin idanun shi. Ta ƙaraso ta ajiye masa plates ɗin a gaban shi zata juya yace "baki ji ba"

Sai ta juyo "na'am"

Nuni yayi mata da kujera ta zauna, sai ta kasa masa musu ta ɗan ɗofana kamar wanda take kan ƙaya ba wai don Uncle B yana jiran ta ba, sai don Yaseer ɗin daren jiya ne a gaban ta.

Toothpick ya ciro ma kan shi, ya ɗauki slice na melon ɗaya ya miƙa mata a jikin fork ɗin da ta saka mishi.
"Help me, yayi mun yawa"

Kanta a ƙasa ta miƙe ta ƙaraso ta karɓa sannan ta koma wurin zaman ta, ta kai baki ta gutsuri kaɗan tana taunawa a hankali. Saida ta fara ci sannan ya ɗauki wani a jikin toothpick ɗin ya kai nashi bakin.

Ta tsinkayo muryar shi yana faɗin "Amma kin faɗa mishi ba shi kaɗai yake takara ba ko? Kada ki bari ya sakankance yazo ya faɗi yace ba'a masa adalci ba".

Tari ta shiga yi don yayi nasarar saka abinda take ci yabi mata ta hanyar Iska, ta shiga bugun ƙirjinta a ƙokarin ta na daidaita kanta.

Miƙewa Yaseer yayi ya ɗibo mata ruwa a dispenser ya ajiye a kan center table a gaban ta, ta ɗauka ta sha tana mayar da numfashi.

"Wai yaya Yaseer dan Allah da gaske kake yi?"
Ta tambaya muryar ta a shaƙe don bata gama daidaita ba.

"Kin amince ne in tabbatar miki?"

Sai tayi shiru.

"Ki je kada rival ɗina ya gaji da jiran ki. Bani son cheating karawa zamu yi fair and square mai ƙwanji ya ɗauka"

Innalillahi! Miƙewa tayi a zabure tana kallon agogo fiye da mintuna 30 kenan tasowan ta daga gaban Uncle B, ta juya da sauri ta koma ta same shi suna kallo a waya shi da Mufid.

Ta fara kunna ma Mufid ɗin TV a channel ɗin Ceebibis sannan ta zauna tama rasa ta ina zata fara bawa Uncle B uzuri amma da mamakin ta sai ya ɗago fuska a sake yana tambayar "kin dawo?" Kaman a lokacin ya san da isowar ta.

Ya kashe wayan shi yana tura Mufid wurin ta "ka je ka karɓo mana wayan Aunty kaga nawa ba charge."

Yaron ya ƙaraso jikinta yana kwaɓe fuska.

"Aunty ki bamu Please"

"Ba ga TV ba Mufid?" Ta tambaya tana shafa lallausan gashin kan shi.

"Ni youtube nake son kallo"

"Ai youtube ɗin ma akwai a TV"

cikin amincewa ya gyaɗa kai, ta ɗauki remote zata haɗa da WiFi ɗin gidan ta saka mishi channel ɗin da yake so amma Uncle B sai cewa yayi "idan baki son bashi ne just say so, Amma cika mana kunne zai yi idan kika kunna masa a TV kuma kince ba zaki matso kusa ba".

Sai ta shiga duba wayan da bata gan shi a wurin ba ta tuna ta manto shi a kitchen. Tayi hamdala a ranta kana ta miƙe ta shiga kitchen ɗin ta hango wayar a kan kitchen island.

Apps lock ta shiga ta rufe messages da WhatsApp dinta don ba zata yi sake ko da gigin wasa Uncle B ya ga saƙonnin yaya Yaseer ba. Ta fito tana shiga youtube ɗin kafin ta mika ma Mufid ya kai ma Uncle B ya saka mishi channel ɗin da yake so, Amma sai ya karɓi wayan a hannun yaron ya sake kunna mishi nasa ya bashi, shi kuma ya shiga danne-danne a nata.

Messages ɗin kuwa ya fara shiga yaga a rufe, ya fita ya shiga WhatsApp shima haka, bata da wani social media app bayan wannan koda facebook ne kuwa sai ya koma call logs ɗinta, gashi nan last call ɗinta na jiya YK.

Ya ɗago yayi mata wani irin kallo itama duk a tsarge take abinka da mara gaskiya.

Sai da ya gama dubawa ya fita ya shiga gallery ɗinta. wasu hotunan ta ya fara gani da na wasu mutanen ya cigaba da scrolling zuwa na Yaseer rututu wa'inda ta tura ma kanta ranar da zata tura mishi kdrama.

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

89

"Hafsah kenan" ya faɗa yana murmushi mai sauti wanda bata haɗa hanya da nishaɗi ba. Sannan da kan shi ya miƙe yana bata wayan da ya kashe ba tare da ya fita daga cikin gallery ɗin ba don ta gane abinda tayi.

Mikewa itama tayi a dame don idan ya kira sunan ta gatsau ɗinnan toh fa ba magana.
Hannun ta yana rawa ta saka ta amshi wayar sannan kawo shi fuskar ta da zata yi security ɗin wayar ya buɗu da face unlock, fuskar yaya Yaseer ya shiga cikin ganin ta a hoton da yake bayyane a kan wayar a halin yanzu. an ɗauke shi ne a wani ɗakin motsa jiki wanda take da tabbacin ba na gidan nan bane, cikin ƙananun kaya grey hoodie da baƙin wando kirjin rigan yayi shatin gumin da ya haɗa.
A hoton ya ɗan tara gashi a kan shi wanda ya rufe shi da hular rigan amma na gaban goshin sa suka yi taurin kai suka leƙo, tsaye yake ya zuba hannun shi a cikin aljihu.

Bata san itama meyasa ta tura ma kanta hoton ba a lokacin, don irin hotunan nan ne da mutum yake yi don kawai ya ajiye ba don ya yaɗa ba, kuma ma kaman Yaseer din bai san an ɗauka ba don duk da yana fuskantar Camera da jikin sa Amma idanun shi suna kallon wani waje daban.

Ganin ta tsaya tana daɗa karewa hoton kallo ne ma a maimakon tayi saurin gogewa tana bashi hakurin bata san lokacin da aka ɗauki wayan aka tura mata ba, amma fuskar ta ko mamakin kasantuwar hoton a cikin wayan bai gwada ba. Ta san da shi kenan.

"Son, zo mu tafi" yace da Mufid yana karɓan wayan shi tare da ƙokarin riƙo hannun yaron.
Da gudu ya koma jikin Reina sanin cewa yayi mishi alƙawarin a wurin ta zai bar shi ya kwana idan suka zo, har ma sun taho da kayan shi a cikin mota.

Daga bayan ta yake leƙo Uncle B da ya turɓune fuska yana jifan shi da mummunan kallo don idan ya ƙure shi fushin da bai sauƙe a kan Reina bane zai sauke a kan shi.

"If I count to three baka zo mun yi gaba ba..." Yayi ƙwafa "ka san hali na ai"

"Uncle Bilal ko abinci fa baka tsaya kun ci ba, gashi kun ɗibo hanya" Reina ta mararaice fuska yanda zata samu ta narka fushin sa amma sai ya kalle ta da fuskar da yake duban su Zahra da Hajiya Hauwa.

"Da maroƙi da mabaraci wanne nayi miki kama?. Ko ke abincin da ake baki ne ya saka ake gwada min iko a kan ki? Toh ai nima da an bani dama ba kasawa zan yi ba, kinga nima sai in yi yanda na so!"

Ya zaga ta zai fisgo Mufid daga bayan ta yaron ya saka kuka cike da tsoro. "Daddy toh PS ɗin fa da kayi min promise idan na kwana ban faɗa ma mummy ba? I promise ko ta tambaye ni gidan su Aunty Zaheera zan ce na kwana ko Aunty Ameesha please Daddy."

Reina da Uncle B suka shiga kallon kallo don ita a yanda yake nuna mata ta ɗauka mummyn Mufid ɗin da kanta ta bada daman a taho mata da shi.
Ya sha cemata tace zata bar mata shi a wurin ta yana daga cikin dalilin da yasa take ɗokin auren Uncle B don duk inda ta shiga da wannan balaraben yaron sai an juyo an sake kallon su balle ace shi nata ne halak-malak kullum tayi ta kallon shi tana jin daɗi har ya girma.

Sai ya sassauta fushin sa lokaci ɗaya yana sakin fuska kafin tace wani abu "No Aunty tana da exams on Monday so mu barta tayi karatu ko? Muje zan siya maka PS ɗin I promise."

Da haka yaron ya yarda ya je wurin shi, Reina jiki a saɓule ta bi bayan su ta raka su har mota dukkan su suna gumm da baki. Ita ta rasa ta inda zata fara tambayar sa ne ya sake mayar da cibi ya zamo kari, shi kuma bayi son ya gwada ya gama saukowa ta gano rashin gaskiyar shi.

Mufid na ɗaga mata hannu Uncle B ya rufo mishi ƙofar mota sannan ya ciro wani shopping bag a seat ɗin baya ya miƙa mata.

"Na ga an kawo miki wani laidan dai amma ga nawa ma ki ƙara, Allah yasa ya kai ya saka ki murmushi shima"

Bata ce komai ba buɗe ta leƙa shima kaman yanda tayi wa na yaya Yaseer Tunda ya zama kishiyar sa. turaruka ne masu tsada daga gani da sauran kayan shafa na mata.

Ta ɗago da kwatankwacin annurin da ta yafa ma yaya Yaseer dazu tace "wow, Nagode uncle Bilal"

Sa ya ji daɗi ko banza ya soke na Yaseer, ya maida mata murmushin. Ya matso ta saida ta matsa baya taku ɗaya sannan cikin ƙasa da murya yanda Mufid dake kusa ma ba zai jiyo su ba yace "Please doll idan ba kina son sake ganin ɓacin raina bane ki goge hotunan nan daga wayan ki, duka, kuma yau nake so"

Ta gyaɗa kai, ya tsaya yana ƙare mata kallon ƙarshe, sai ta shiga ɗaga masa hannu ko zai wuce ta samu tayi numfashi da kyau.

Da gaske yana sonta, yana sonta sosai kuma ita ce ta dace da rayuwar shi don haka Yaseer ƙaramin yaro yayi kaɗan ya raba su.
.....

Tun bayan da tayi sallar azahar ta duƙufa ma karatun jarabawar da zasu rubuta a ranar Litinin. Idan ta ɗan taɓa kaɗan sai ta kira Safina su faɗa ma juna yanda suke, hakan da suke yi kaman competition yana kara musu kaimi da hana gajiya don kowa so take yi ace ta wuce ƴar uwarta.
Chapter 67 · 0% Book details