Sashe 57
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"I wish ina da wannan lokacin Amma a baki ba shine ba, a aikace nake son ganin canji, ina son mu cigaba mu ɗaga ƙasar nan da kanmu ba sai mun jira alƙawuran gwamnati da babu ranar cikawa ba, mu tashi mu ɗaga na gefen mu sai kuga komai yana tafiya daidai.
Na kawo wannan program ɗin makarantar nan ne saboda nima a wani lokaci ɗalibi ne kamar ku, da yanzu ina sahun Alumni na makarantar nan ba don an kore ni ba, but that's not the point, ina so ne ku fahimci muhimmancin shi shiyasa muka saka kuɗin registration not because I need your money sai dan a psychology na ɗan adam duk abinda ya cire kuɗin shi ya siya shine mai daraja. Ni nayi wahalan na nimo na kawo muku saboda kallon ƙanne na nake muku baki ɗaya. Kaman wannan ƙanwar tawa" ya nuna Reina da bata san dalilin da ya sake dawo da ita yau ɗin ba.
"Tashi tsaye su gan ki da kyau"
Tayi saurin girgiza kai tana jin kaman ta lume cikin ƙasa sai ya saka aka saka mata tafi raff-raff su Safina da wanda ke zaune a ɗayan gefen ta suka miƙar da ita tsaye.
"Snacks vendor ce, duk wanda ya ji dadin namu na jiya da na yau ma ku yi contacting ɗinta, tana karɓan order ko guda nawa ne ga cika alƙawari"
duk Ummi ne ta jawo mata, ko kuma laifin kanta ya kamata ta gani da ta nemi shawarar ta tun farko bata mayar ma Yaseer takardan shi ta shafa ma kanta lafiya ba, gashi illar abun bai tsaya a ɓata tsakanin ta da Uncle B ba kawai.
"Bamu ganta da kyau ba" cewar wasu daga seats ɗin baya.
Sai yayi ma Reina alaman ta fito da yatsu biyu. Yanzu ma su safinan ce suka angiza ta sai gata a tsaye a gaban ɗarurwan mutane tuni kanta ya shiga juyi tana mamakin yanda Yaseer yake iya kallon cikin idanun su duka yayi magana.
Ya miƙo mata Mic, "here introduce your business" sai ya ranƙwafa jikin kunnen ta kaɗan ya raɗa mata "Idan an tashi ki jira ni zamu yi magana mai muhimmanci"
Ta ɗago ta kalle shi, fuskar shi a tamke lokaci ɗaya ta nemi fara'ar da yake duban mutane da shi ta rasa sai ta ji ƙirjin ta ya fara lugude.
Ƙarshe shi ya gabatar da ita da sunan da ya gani a jikin sticker ɗin da Ummi tayi sannan numbern wayan Ummin ne a jiki ba don haka ba a yau zai canza mata layi.
Ta koma ta zauna tana ji yana bayani ma duk wani mai wata idea ko wani business ya tura proposal ɗin zuwa e-mail da aka bayar a jikin card ɗin jiya. Ita bata ma san a ina ta yar da nata ba kuma yau duk wanda bai zo da shi ba an hana su shiga sai da suka koma suka ɗauko Amma banda ita.
Aicha ta karaso tayi jawabin rufe taro sannan wani MSSN official ya ƙarƙare da addu'a aka tashi.
.
.
Sauri take yi ta bar ƙofar wurin kafin a gama fitowa amma duk yanda ta waiga bata ga Safina ba kuma wayan ta yana hannun ta tun da suka shiga wai zata tura mata wani Kdrama da ta gani yayi mata daɗi itama ta kalla.
Can ta hango ta suna takowa tare da Muhammad abokin Yaseer, shima Yaseer ɗin suna tafe da Aicha sai ta juya zata bar wurin Safina ta ɗaga murya ta kira ta.
Juyowa tayi ta tsaya Safina ta karaso wurin ta miƙa mata wayar ta sannan ta riƙo hannun ta. "Ki zo mu tafi anyi cancelling din lectures ɗin yamma." Tace tana janta Wurin da suke tsaye.
Haka ta bita simi-simi, Muhammad dake riƙe da wayan Safina yana tura wani abu ko shima kdrama ɗin ne? yace ta shiga motan shi, don haka Reina tayi saurin ƙarasawa zata shiga gidan baya, har ta buɗe ƙofan Yaseer taku uku yayi ya saka hannu ya rufe.
"Wuce muje"
Kallon shi tayi ganin fuska babu alamun wasa ta fara tafiya yana bin ta a baya har jikin motar shi, ya buɗe mata gaban motan ta shiga Amma Aicha ta riga ta coge a ciki. Salum alum ta juya zata koma baya ya tsaida ita sannan ya juyo ga Aicha yace "ki bi Muhammad ina son zamu yi magana da ita ne"
Ta kalle shi ta kalli Reina da cikinta ya gama ɗura ruwan taraddadin abinda zai faɗa mata, sannan Aicha ta fito a hankali ta tsaya tana gani Reina ta shiga gaban motan ya rufe.
"ki je kada su tafi" yace da Aicha dake tsaye ganin Muhammad ya saka Safina a gaban mota zasu ƙara wuta.
Ta dauki abinda yayi mata a matsayin cin fuska kuma ta jishi har cikin ranta amma ba zata iya fushi da shi ba sai ta shagwaɓe fuska. "Toh ka raka ni"
Ya kalli tsakanin inda suke da motar Muhammad ɗin bai wuce taku huɗu zuwa biyar ba amma sai ya ce mata "muje".
Ya tsaya ta shiga ta rufo ƙofarta sannan ya juyo. Reina dake leƙen su tayi saurin gyara zama, ya shigo ya tada motan ba tare da yace mata komai ba har saida suka fita daga makarantar tukunna ya dubeta yanda ta kame kanta wuri guda.
"Reina"
"Na'am" tayi saurin amsawa kaman mai jira tana ɗagowa suka kalli juna kafin ta sake sunne kai.
"Ki faɗa min Abinda kika sani a kan Bilal, manemin auren ki"
Menene ya same su da zancen juna ne?.
"Ke nake sauraro" yace jin tayi shiru.
"Umm.. ƙanin Umman Zahra ne"
"Uhmm hmm"
"Yana da yara biyu, mace da namiji"
"Mata fa?"
"Sun rabu da daɗewa"
"Baki da masaniya a kan ya mayar da ita ɗakinta kenan" ya tambaya yana zaga sha tale-tale(round about) na awala.
Ƙirjin ta ya doka, yaushe?! ta ayyana a ranta.
Ganin yanayin ta da kuma rashin samun amsa kai tsaye yace "I'll take that as a yes. Abinda ya raba su fa? Kin sani?"
Shima bata iya bashi amsa ba don ko sau ɗaya bai taɓa sako mata zancen tsohuwar matar shi ba kuma bata damu ba tunda bata gaban ta kuma ta saka ma ranta babu abinda zai haɗa su ko nan gaba.
"Toh wai me kuke cewa a wayan ku na awa biyu da rabi ɗin eh?"
Ya nemi wuri yayi parking a gefen hanya sannan ya ɗauko wayar shi yayi ƴan danne-danne ya miƙo mata wani hoto bayyane a kan screen ɗin.
"Gashi ki gani da wacce zaki zauna, ba kuma don ta fiki da komai ba Wallahi, kawai dai ya kamata ki san fuskar da zaki ɗorawa duk labarin da zaki ji daga yanzu."
Jiki ba kwari Reina ta karɓi wayan tana kallon kyakkyawar balarabiyan da bata san lokacin da ta saki salati ba, ta ina yaya Yaseer zai ce bata fita da komai ba? Ga kyan fuska ga diri, gashi har ƙwanƙwaso!
Bata san ta riƙe baki da ɗaya hannunta ba tana nanata kalmar innalillahi a ƙasan numfashi ba. Hango kanta take yi ta ƙure adaka ta fito wannan ta fito da kayan barci kawai haka za'a kalle su yanda ka san Rana da duhun dare.
Yaseer yaci gaba da cewa "A jami'a suka haɗu a Canada, tun yana matsayin ɗalibi suke soyayya kuma ta aure shi yana matsayin ƙaramin likita. Amma sai gashi har saida ta maka shi a kotu a kan a raba aure sannan ya yarda ya saketa ta janye ƙara, sai kuma wannan dawowar shin gashi sun dawo tare kuma ya tada zancen auren ki.
Yanzu sai ki je ki ji daga bakin sa ki yanke hukunci, Amma ki yi ma kan ki adalci Hafsat dama ɗaya takk kike da shi" ya tada motan suka cigaba da tafiya.
Haka suka ƙarasa gida tana shiru kaman wanda ruwa ya cinye zuciyar ta tana taro uzururrika tana miƙawa Uncle B. Ta amince matar shi ta fita kyau amma yana da wancan ɗin ai ya ganta yace yana so, sai dai me yasa ya ɓoye mata cewa sun maida auren su bayan da yanzu a matsayin kishiyoyi suke?.
"Mun iso, ki shiga gida" Yaseer ya dawo da ita daga duniyar tunani. Wayar hannun ta yayi ƙaran shigowar saƙo sannan yace "na tura miki sauran kuɗin ki, abu yayi kyau yayi daɗi mun gode"
Gani tayi sun faka a gate sai ta tambaye shi "Ina zaka je yanzu?"
"Zan je duba gidan da zan saka Abidah ne"
"Wacece Abidah?"
"Budurwata mana Reina Auntyn ku, nima lokaci yayi da zanyi aure, Abinda nake jira ya zo karshe. Ko zaki raka ni ne?"
Ta girgiza kai tana buɗe ƙofar ta fita, yanzu a matse take ta je ta kira Uncle B, Amma sai ta samu zuciyar ta ya mata sanyi kaɗan jin ba Aicha zai aura ba dukda bata san wacece Abidan ba.
Saida ta shiga gida a kan idon shi sannan ya bar wurin, tun daga bakin gate ta fara laluɓan numbern Uncle B kuma cikin Sa'a a kira na farko ta same shi.
"Hello doll, yanzu nake tunanin ki"
"Uncle Bilal kana ina yanzu?"
Gwamma yazo suyi ido da ido dan wannan ba maganar waya bane.
"Ina gida a KD. Kina son gani na ne in fito yanzu in zo?"
Ta fara leƙa main parlour, sai da ta tabbatar babu kowa sannan ta ƙarasa shiga ciki tayi hanyar upstairs.
"Magana mai muhimmanci nake son muyi amma yamma yayi ka bari sai gobe ka zo"
"Da matsala ne? Naji muryar ki wani iri? Kada ki damu Zan iya isowa zuwa maghrib"
Sai da ta shiga dakin su ta turo ƙofa sannan tace "no... Dama a kan Mummyn Mufid ne, wai kun dawo tare? As in ta dawo ɗakin ta?"
Sai ta ji shiru kaman bai ji tambayar ta ba ko matsalar network ne?
"Hello...hello" tayi ƙoƙarin tantancewa.
~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
83
~~~~~~~~~~
_Pour T'éviter de souffrir_
_(to avoid you suffering)_
_Je n'avais quà te dire je táime_
_(I only had to tell you I love you)_
~~~~~~~~~~
Babu amsa sai karan rufe ƙofa da ta ji sai kuma ta fara jin Muryar mace sama-sama.