← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 117

Sashe 47

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uncle B ma har Reina ta bashi wurin zama, a ɗan tsukun ta haura sama sai gashi ta fito cikin wata abaya da tun a shago ya ɗauki idanun Yaseer. Tana gyara mayafin shi a kanta ta wuce kitchen ta haɗo masa ruwa da juice, sai bowls ɗin dambun kaza da ƙuli-ƙuli a saman tray.

Daga Yaseer har Alaji Abdou kallonta suke yi, sai da ta zuba ma uncle B ruwan a cup sannan ta zuba wani ta miƙo ma Alaji Abdou Saboda borin kunya ta dawo da bowl ɗin gaban shi sannan ta miƙe ta sake zubo ma uncle B din wani.

"Thanks doll" uncle B ya sake mata murmushi bayan ta dire a gaban shi, ta ɗago ta kalle shi a kunyace tana shirin miƙewa cikin raɗa yace "I really miss you doll, na kusan haukacewa"

Daman ta sani, da dalili, dalili mai ƙarfi ma kuwa da ya shiga tsakaninsu, amma yanzu komai ya wuce tun da yace ya dawo, hala har sun gama abun da ya kai shi ne.

Kunya ya hana ta cigaba da zama a parlourn dukda ga Aicha ma ta kawo wani tray ɗin ta ture abinda Reina ta kawo ma mahaifin ta gefe. Ita ko a jikin ta fama kawai take yi da bugun zuciyar da take jin kaman zai fasa ƙirjin ta ya faɗo.

Yaseer yabi bayanta da ido har ta ƙule ɗaki yana mamakin yanda yake mata kallon yarinya ashe ita tana ganin ta kai har ta san rawar ƙafa a kan namiji, lallai yau mai raba shi da Reina sai Allah, sai tayi mishi bayanin a inda ta koyo wannan iyayin, idan Safina ce sanadi ko wata to a shirye yake ya datse alaƙar su domin ya san ita bata da wannan wayon a karan kanta.

"Darling baki iya gaisuwa ba ko?" Alaji Abdou yace da Aicha.

"Sorry daddy murnan ganin ka ne ya mantar da ni" sai ta kalli uncle B fuska a sake suka gaisa, ta sake maido da hankalin ta kan mahaifin ta.

"Tare kuke ne Daddy?" Yaseer ya tambayi Alaji Abdou.

"A'a a hanya muka haɗu, engine motana ne yayi zafi sosai mun tsaya sai gashi nan ya rage mun hanya ya kawo ni.

"Daman nima nan ɗin nake da niyyar zuwa, don yau na shigo garin, ina son in yi surprising doll ne"

"Wacece kuma doll?" Yaseer ya tambaya yana yamutsa fuska.

Sai da ƙaramin murmushi ya kuɓuce ma uncle B kana ya amsa da "matar da zan aura in sha Allah, yanzu ma izini na zo nima ba tare da ɓata lokaci ba, idan an yarje mun kuma iyaye na suna hanya da kayan tambaya da saka rana"

Murmushin Aicha ya ƙara faɗi wani daɗi na kara ziyartar zuciyar ta yanda ka san ita ce wacce ake magana a kai. Las-las Reina ba zata daɗe tana shige mata hanci da ƙudundune ba, kuma as long as she's out of the picture Yaseer nata ne babu wata mace da ta kai ta shiga tsakanin su.

Shiko Yaseer cikin rashin fahimta ya sake tambayan "wai zancen wa kake yi ne? Don mu bamu da ƴammata a gidan" ƙoƙari yake yi ya ruɗa kan shi da gangan, dukda duk wurin babu wanda ya kai shi sanin kan zancen Amma zai iya yiwuwa uncle B Maama yake nufi Koma Aicha tunda ita ne kawai yake ganin ta kai aure a cikin su, shekarun ta ashirin da biyu uncle B zai yi maneji.

Maganar Alaji Abdou na gaba kuwa shine ya ruguza rabin fatan shi. "Toh-toh bari mahaifin ta ya zo sai ka mayar da magana a gaban shi, shine mai iko da ita"

Ya taɓa Aicha "je ki kira Daddyn ku da abban ku" ta gane daga wurin tayi tafiyar ta yake nufi ita kuwa da murnarta ta miƙe tunda ƙaya za'a cire mata a maƙoshi.

Ya shiga godiya ma Alaji Abdou Yaseer dai ya harɗe hannu a ƙirji ne kawai yana ganin ikon Allah har Abbah ya fito tare da Alhaji Tahir a kan electric wheelchair ɗin shi uncle B ya zube a ƙasa yana kwasan gaisuwa.

Sai da ya fara mayar da magana tiryan-tiryan ya ambaci sunan Hafsatu Reina tukunna Yaseer ya daina gane komai har aka ƙare zaman.

*Reina*

Faɗawa gado tayi tana tsallen murna, sai da ta gama ta jawo wayarta ta danna kiran Safina.

Duk da safina bata wani son ta da uncle B Amma hakan bai hana ta taya ta murna matuƙa ba ganin lamarin yana son haurawa matakin gaskiya, sai tsalle suke yi da iface-iface.

Sai can jimawa aka ƙwanƙwasa mata ƙofa, ta katse kiran kafin taje ta buɗe. Aicha ta gani da murmushin gaske a kan fuskar ta.

"Kije Abbah yana niman ki a parlon sa"

Komawa tayi gaban madubi ta gyara zaman mayafin ta kafin ta fita ta ɗauki hanyar parlon ƙirjin ta yana bugu, lokaci ɗaya fargaba ya shige ta.

A parlon ta sami Ummah da Abbah, tayi musu sallama suka mata izinin shigowa sannan ta koma gefe ta rakuɓe.

Abbah ne ya shiga karanto mata dalilin kiran sannan ya tambaye ta ko tana son uncle B su ji daga bakin ta kafin ayi mishi izini kaman yanda ya buƙata.

Shiru tayi tana shafa stones ɗin abayar jikin ta.

Saida Umma ta sake tambayar kafin ta ɗaga kai sau ɗaya ta sake sunne shi.

Hamdala Abbah yayi sannan ya sallame ta da addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi.

Tana hanyar komawa ɗaki uncle B yayi mata text ta fito suyi Sallama zai tafi.

Shi kaɗai ta samu a parlon ƙasa yana tsaye. Suka sake ma juna murmushi da suka haɗa ido sannan ta sunne kai cikin jin kunya tana one taku har ta iso wurin da yake.

"Kin ƙara girma da kyau doll, sosai" yace sannan yayi gaba tana bin shi a baya har jikin motar shi.

"Zamu je ne?" Ya tambaya bayan ya buɗe motar daga inda yake.

"Ina?"

"Yawo, ban gaji da ganin ki bane"

Tayi murumushi tana rufe idanu. "sai wani lokaci ka je ka huta yanzu tunda ka ɗibo hanya"

"In huta? Ai ni da hutawa sai ranar da kika zamo mallakina na gan ki a ɗaki na."

Sake kare fuskar ta tayi tana ɗan juyin jin daɗi a wurin lokacin da wayan ta dake hannun ta na dama ya fara ringing.
Ɗago wayar tayi daga kan fuskarta ta duba mai kira. YK ta gani as caller ID ta ɗaga ba tare da ta shirya ba domin wannan shine karo na farko da Yaseer yake kiran ta.

"Hello, yaya Yaseer"

"Kin gama wankin ne kika tsaya kina surutun ki?"

Waiwayawa tayi taga daga inda yake kallon ta, ta ɗaga kai ta hango shi a balcony ɗin sama ya jingina da railing na wurin da waya a kunnen shi.
Uncle B ma yabi yanda take kallo ya hango Yaseer idanun shi a kanta.

Tana kallo ya buɗe baki sai ta jiyo muryar shi ta cikin wayar yana faɗin "ba tambayar ki nayi ba?"

"Zan dawo na ƙarasa"

"Yanzu nake so"

"Toh ai Irfan ɗin ma ya gudu"

"Yanzu nake so Hafsat. Kada in zo in same ki a wurin nan, na faɗa miki zan san yanda zan yi da ke".

Ya katse kiran tana gani ya koma ciki alamun da gaske sauƙowar zai yi.

Da sauri ta ɗaga ma uncle B hannu sai gani yayi ta koma ciki har tana ɗan haɗawa da gudu.

A parlor suka ci karo da Yaseer har ya sauƙo. "Zan je in canza kaya ne" tace a ɗarare tana gwada abayar jikinta.

"Ina jiran ki" shine abinda yace ya fita waje don tabbatar da Uncle B ya tafi.

Haka ya saka ta a gaba ta shanya sauran kayan tass suka koma ciki ta sake ɗibo sauran da ya rage a cikin dryer shima ta shanya su.

Sai da aka kira sallar azahar ya barta ta koma ɗaki ya wuce masallaci. Wanka ta sake yi don rage gajiya ta yi sallah sannan ta saka pink T-shirt da palazzo ta mayar da inner cap ɗin kanta ta ɗale gado.

Missed calls ɗin uncle B guda uku ta gani don haka ta mayar da kiran bugu biyu ya ɗauka.

"Doll lafiya dai ko?" Ya tambaya cikin muryar damuwa.

"Lafiya ƙalau uncle Bilal, kana ina yanzu?" ta rungumo pillow tana furzar da iska.

"Yanzu na iso masauƙi na tsaya Sallah ne a hanya, and Hope nan ma ba maltreating ɗin ki suke ba in zo in ɗauke ki in mayar da ke gidan mu tunda yanzu aure zamu yi" yace yana cire takalmi da safar ƙafar shi.

"Hmm ni da ka manta ni yanzu kawai sai in aure ka? Har gudu na ka fara yi ka daina ɗaukan kira na"

Tana ji ya furzar da dogon numfashi shima lokacin da ya miƙe a gado yace "Da gaske ban san da kalmomin da zan yi amfani da su in nemi yafiyar ki ba doll, kunyar disappointing ɗin ki nake ji shiyasa na zaɓi na janye jiki na har sai na samo mana mafita, Amma yanzu na haƙura da aikin, zan koma ƙarƙashin general in dai zan samu kasancewa tare da ke"

Tashi zaune ta yi. "Daman baka gama ba ka dawo?"

"Toh yaya zan yi doll ina niman rasa ki? Yaya Yaseer ɗin ki har da gargaɗi yayi mun shiyasa na haƙura da komai na dawo ayita ta ƙare"

"Yaya Yaseer kuma?"

"Yes! Ranar monday da kika kira ni I called you back da rana ba'a ɗauka ba. I was ready in yi miki bayanin abinda yake faruwa amma da na cigaba da kira ya ɗauka yace in rabu da ke because you're already engaged"

"Engaged? Ni ɗin?"

"Abinda yace mun kenan shiyasa kawai na dawo"

"So yanzu shekara ɗaya da ɗori da kayi duk a banza?"

"Kin fi su daraja doll. In dai zaki iya zama da ni a haka aji na bai kasa miki ba, ni kuma zan yi iya bakin ƙoƙari na in kula da ke"
Chapter 47 · 0% Book details