← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 117

Sashe 19

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yes! I was like ban kai wanda zaki iya faɗamin da bakin ki ba ma? And ko saƙon gaisuwa baki bayarwa a faɗa min, shiyasa nima na kyale ki, saƙon da nake turo miki kuma tunda ba ke kika saka ni dole ba bazan fasa ba. Shiyasa nazo yau ko Addah Hauwa ma bata sani ba saboda kada ki sake guduwa"

"Wallahi Tallahi Uncle Bilal, bani da masaniya a kan duk abinda kake faɗi. Ban san wani maganan zuwan ka ko wani maganan makaranta ba balle na saƙo. I thought you just abandoned me that's it!"

Cikin ranshi ya ayyana lokaci yayi da zai saka general yaci mishi uwar Hauwa.

"Shikkenan muci abinci" yace don kawar da zancen.

"Toh kayi haƙuri?"

"Idan kin yarda kina so na ba?"

Basu dawo gidan ba sai bayan la'asar, Uncle B yabi da ita sky crown ya siya mata cupcakes ɗin da Hajiya Hauwa tayi mata asaran shi, sai ta bayar a matsayin wanda tayi tunda lokaci ya riga ya ƙure ba zata iya sake wani ba.

Washegari sai gashi da sassafe ya zo ɗaukan ta zai kai ta rubuta exams. Ta faɗa mishi suka bi suka ɗauki Safina ya kai su har gubi har ƙofar venue, sannan ya fito yana mata sallama a gaban idanun duk ƴan ajin su dake jiran a basu dama su fara shiga ɗakin jarabawa. Ya miƙo mata jakar cake ɗin jiya tana godiya duk kunya ya gama kama ta.

Ranan da zasu yi exams na biyu ma haka ya zo ya ɗauke ta, hajiya Hauwa tana gani babu yanda ta iya don wannan karon ba nasiha yayi mata ba zama yayi ya wanke ta tass kuma a gaban ta ya kira general ya faɗa mishi abinda ke faruwa Ranan tashin hankali ya hana ta barci.

Yana India yana jinyar ƙafa kuma yace daga ya dawo tazo ta same shi idan ba haka ba kada ta sake gwada masa fuskar ta.
Uncle B kuma yayi mata kashedin idan ƙuda ya taɓa Reina Wallahi ta kuka da kanta, don haka Hajiyar shi yanzu capacity take zubawa a gidan.

Sannan hankalin ta ya fara kwantawa da Uncle B sosai har waya suke yi, a taƙaice dai sun fara soyayya cikin sati guda, har ya kawo mata Mufid mai shekaru 7 a wani weekend tana gidan Ummi, ya wuni mata sannan da yamma Uncle B ya shigo ya gaida Baba.

Reina ta shirya ita da Mufid suka fita outing, babu yanda bata yi da Maama ta bisu ba taƙi don haka sai Safina suka ɗauka.
Sun ci kayan daɗi kuwa sai tunanin ƴar uwarta take yi.

A safiyar monday fitowa tayi cikin shirinta na makaranta saboda bata son ta saka uncle B jira, ya daɗe da kiran ta ya sanar mata ya taso, tana fitowa kuwa sai ga motar shi shima yana shigowa.

Murmushi ta sake tana sadda kai ƙasa lokacin da ya fito daga motar, sai dai shi babu fara'a a tashi fuskar sai wani abu mai kama da fargaba da damuwa.
Ya tako ya ƙaraso wurin ta, ta gaida shi ya amsa.

"Hafsah na, kiyi haƙuri yau ba zan samu kai ki makaranta ba"

Ɗago kai tayi murmushin ta yana komawa yaƙe, daman ta san sintirin gubi akwai gajiya tace "babu komai, zamu tafi da Safina ai"

Ganin bata fahimce shi ba yasa yace "tafiyar da na faɗa miki ne ya taso"

Sai a lokacin ta dube shi a razane tace "toh ganin Yaya Yaseer ɗin fa Uncle Bilal?" Daman shi ya matsa ta bari sai ta gama exams kafin ya kaita amma da tuntuni sun je ita.

"Zamu je nayi miki alƙawari, babu shiri nima tafiyar ta taso min. Wani babban research center aka buɗe na Cancer a UK, to suna ɗaukar oncologist wato likitocin Cancer kenan da researchers a kowani ƙasa a faɗin duniya mutane uku kawai. To ƙasar da nayi karatu wanda suka fini cancanta suna da yawa shi yasa na dawo nayi amfani da indegene ɗina na Nigeria in samu a ɗauke ni. Nan ɗin ma competition yayi yawa domin dama ne mai matukar daraja, dalilin da ya saka na dawo kenan na sauke kai na roƙi general ya saka baki da aljihu nima na zuba kuɗi ba kaɗan ba. sai gashi yau kawai sun kira ni a Abuja kuma suna buƙatar gani na yanzu kafin damar suma ta suɓuce daga hannun su. Kinga dole in tafi Reina, nayi Sa'a zan samu jirgin da zai tashi nan da minti 40."

Kafin ya kai ƙarshe hawaye ya gama taruwa a idanun ta amma sai koƙarin saka murmushi take yi a saman fuskar ta, tun yanzu tana ji a jikin ta ya fara nisa da ita bayan ta saba da shi ta sama mishi matsuguni a zuciyar ta.

"Ina zaka dawo dai Uncle Bilal?"

....

"Umma... Umma ki gani!"

Zahra ta turo wayanta fuskar mahaifiyar ta dake leƙen su Reina ta windown parlo.

Yatsa ta saka a baki tana make ta tayi shiru kada ta tona musu asiri sannan ta sake labulen suka bar jikin windown tana karɓan wayar a hannun Zahra.

"Menene? Wannan kuma su wanene?"

Wani hoto ne a kan shafin Instagram fuskar wayar yake gwadawa na wasu zaratan mazaje guda huɗu sanye da ash ɗin babban riga har aikin jiki iri ɗaya hulunan kansu ne kawai ya bambanta sai mace ɗaya ita kuma kayan jikin ta ba ma zaka iya cewa menene ba amma dukkan su sunyi kyau matuƙa.

"Ina yarinyar abokin Uncle Tahir ɗinnan na Nijar wanda suka zo gidan nan last year?"

"Eh"

"Itace macen fa?"

Sake duban hotunan Hajiya Hauwa tayi tace "toh na gani sai aka yi yaya"

Kin san su waye take tsaye da su?.

Ta gwada Babban cikin mazan wanda ya fisu tsayi, cika da haɗuwa, shine a tsakiya Aicha a gefen shi sai sauran mazan biyu a gefen ta ɗaya a gefen shi.

"Akwai wata friend ɗina irin ƴaran abujan nan ne, tana yawan saka hotunan shi a status a ƙasashe daban-daban yaje seminar da turawa da manyan masu kuɗi, shine na tambaye ta tace wai akwai wata sistern shi friend ɗinta ne. Sai yau kawai a wani shafi da ake saka hotunan biki na gan shi da yarinyar ashe ita ce wanda tazo gidan nan, itama wancan maƙaryaciyan a IG take samo hoton su, gashi wanda suka ɗaura hoton a shafin su duk sun yi tagging ɗin su.

Dake sun saba sana'ar gulma da Zahra hajiya Hauwa sai ta karɓi wayan tana dubawa. "Ai kema kinga sai ki gwale maƙaryaciya kice har gidan ku tana zuwa"

Cike da jin daɗi Zahra tace "Wallahi" tana ƙyalƙyalawa da dariyar yanda itama zata fara baaguu da su ta kankaro aji. Kuma dukkan su tama riga da ta tura musu DM tana fatan su amsa musamman shi babban ma.

Itama Hajiya Hauwa profile ɗin babban ta fara dannawa don shi yafi ɗaukan idon ta. Yayi loading na second biyu kafin ya buɗe.

Username ɗin shi: Gatan_matasa
Full name ɗin shi kuma Yaseer Kamal J.

Sai da kirjin Hajiya Hauwa ya buga ganin sunan don ta tuna da mai irin sunan sakk da yanzu sauran masa shekaru shida kafin ya fito daga firsina.

Yana da followers 760k. Ga hoton da aka saka ɗin shima a kan shafin shi don haka ta hau kai ta bude shi. Likes 224k hoton yake dashi amma na kan shafin shi ba guda ɗaya bane don haka tayi sliding ya gwada mata na biyu. Shi kaɗai ne da Aicha suna tsaye sun kalli Camera fuskar su babu fara'a amma ko ita sun yi mata kyau ba kaɗan ba, wannan kana kallon su kaga kuɗi balle ta sani Alaji Abdou mai kuɗi ne sosai ko lokacin da yake tare da Alhaji Tahir ma balle yanzu da take da yaƙinin likkafa ta ja.

Ta sake sliding ya gwada mata hoto na ukun wanda Aicha ta saka dariya tana kallon camera sai ta kare bakin ta da ɗan purse ɗinta da yanzu sai kaji kuɗin shi, shi kuma mai suna Yaseer ita yake kallo da wadataccen murmushi a kan fuskar shi.

"Kuma ƙanwar shin ce?" Hajiya Hauwa ta tambaya tana komawa kan hoton su duka dake kan wannan shafin bikin. Mazan dukkan su suna kama amma ita basu kama da ita ko tarfi.

"Ina fa?!"

Ta karɓi wayar ta shiga ma Hajiya Hauwa profile ɗin Aicha.

Username ɗinta: His_Darling
Full name ɗin ta Aicha Abdou Hamissou

Bio ɗinta: Taken 💍 da hoton zobe. Shikkenan.

"Mutane suna cewa ko budurwar shi ce ko matar shi, don ba'a taba ganin shi yayi hoto da wata mace ba sai ita, kuma kusan duk ƙasar da zai je sai itama ta ɗaura hoton ta a shafin ta a ƙasar. Wannan hoton ma kwana biyu da ya wuce aka yi dinnern a abuja, kuma wallahi su karan kansu masu kuɗi ne don kinga shi fa har kamfani naga yana dashi"

Ta koma kan shafin Yaseer tana gwada mata bio ɗin shi da ya rubuta :CEO and founder of YK & Co.
Brand ambassador, da wani link na brand ɗin
Sai: Family over everything a ƙarshe.

Haka daya bayan ɗaya ta shiga duba profile ɗin sauran.

Na biyun su username ɗin shi: Ɗangata.
Full name: Suhail Kamal J

Na ukun kuma username: Maihaƙuri
Full name: Sabir Kamal J

Sai na huɗun :Autan_ƴangata
Full name: Irfan Kamal J

.....

"Zan dawo Reina, daga na dawo zamu je muga Yaseer sai abi a saka mana rana kin ji?"

Ta gyaɗa masa kai tana ƙokarin haɗiye kukan ta, "zan jira ka, dan Allah kada ka makara"

Ya gyaɗa mata kai ya ciro bundle ɗin dubu ɗaya ya miƙa mata "Gashi kina kuɗin mota, idan na isa zan kira ki, take care of yourself for me"

Karɓan kuɗin tayi suna ɗaga ma juna hannu ya faɗa motar da ko kashe ta bai yi ba ya ja ya bar gidan da karyayyen zuciya, ita kuwa durƙushewa tayi a wurin ta saki kuɗin tana rera kuka, har sai da tayi nasarar saka ma kanta ciwon kai numfashin ta na koƙarin fara sama ta miƙe, ta juya zata koma ciki ta hakura da jarabawan amma ta san baƙin ciki kawai zata shaƙa a wurin ƴan gidan gwamma taje ɗin kawai.
Chapter 19 · 0% Book details