Sashe 36
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Knocking tayi da isar ta, ta ciki ta jiyo muryar shi yana faɗin "come in"
Ta tura ƙofar a hankali ta shiga.
Wurin na da girma sosai, bata ankara ba book shelves ɗin da suke cinye rabin ɗakin da yanda aka yi furnishing ɗin shi da oak wood ya ɗauki hankalin ta, har tana juyi a cikin sa tana kallo baki sake.
"Idan kin gama ki ƙaraso" muryar Yaseer ya dawo da ita daga duniyar shawagi.
Kama kanta tayi ta ƙarasa gaban table ɗin da yake zaune da farin glasses a idanun shi yana danne-danne a laptop, sai kallon ya koma kan shi, ta tsare shi da idanu shikuwa shirme yake ta typawa a laptop ɗin tun shigowar ta, har sai da ya gagara jure ma kallon nata ya kife fuskar computern yana sauƙe ajiyan zuciya a ɓoye.
Ya ɗago ya dube ta fuska ba yabo ba fallasa yace "sit" sai ta ƙarasa gaban kujeran ta zauna a ɗofane.
Jotter da biro ya ɗauko ya shirya ma rubutu kana yace "menene kike da buƙata ke da ƙanwar ki? Umma tace zaki koma makaranta gobe"
Shiru ya ɗan ratsa tsakani na minti biyu, ita bata yi magana ba shima yaƙi ɗagowa ya dubeta.
"Yaya Yaseer!" Muryar ta ya fito da wani irin taushin da yaji ya tsirga masa wani abu tun daga tsakar kan shi, babu shiri ya saki biron hannun shi.
Sai gani yayi ta miƙe ta fara zagowa inda yake zaune, ganin kaman ƙaraso shi zata yi shima yayi shirin miƙewa kafin ta sake mishi wani ƙazafin ya sake shiga uku, amma sai gani yayi ta zuba a kan guiwowin ta, sai a lokacin ya fara jiyo sheshsheƙar kukan ta.
"Yaya Yaseer ban san da wani ido zan dube ka na roƙe ka gafara ba, bani da kalmar da zan wanke kaina da shi a wurin ka amma Wallahi, Wallahi ba a son Rai na abinnan ya juye a haka ba, ƙuruciya ne da fargaba suka jawo nayi maka ƙarya saboda tsoron da aka dasa min a zuciyata a lokacin."
"Uhmm wacece ke ma?"
Ɗago kai tayi ta dube shi da idanunta da suke zuban hawaye kaman an buɗe famfo.
Kallon rashin fahimta yayi mata "Na san ki ne a wani wurin?"
Babu wanda zai kalle shi a wannan lokacin yayi tunanin ba daske bai gane wanda ke tsugune a gaban shi bane.
Toh ko dai Yaya Yaseer yayi losing memory ne? Ta ayyana a ranta.
Ta gwada kanta kukan ta yana daɗa ƙaruwa tace "Reina ce yaya Yaseer, Hafsatu Reina"
Jinjina kai yayi kaman yau ne ya fara jin sunan ya nuna mata matsuguni yana faɗin "Toh koma ki zauna Hafsatu Reina, I don't have all day"
Ganin zasu cigaba da zama haka nan kuma ba iya jure kukanta zai yi ba yace "jeki dan Allah, Idan kun rubuta zan turo Darling ta amsa ni bani son yawan koke-koke"
Haka ta miƙe jiki ba ƙwari ta fice tana waiwayen shi, ya sake buɗe laptop ɗin gaban shi ya cigaba da abinda yake yi, bai ɗago ba har sai da yaji sautin rufuwar ƙofa.
ƙoƙarin daidaita kanta tayi bayan ta fita kafin a samu mai tambayan ta abinda ya same ta, duk da mutanen gidan basu gwada kaman sun damu da shirgin ta ba baki ɗaya.
Saida ta shiga ɗakin Alhaji Tahir ta fashe da wani sabon kukan, yana barci kukan ta ya saka shi buɗe ido "Subhanallahi Hafsah!"
Ƙarasowa tayi ta zuba a jikin shi tana kuka mai gunji. Wani button ya matse a gefen gadon har saida saman gadon ya ɗaga shi zaune yanda yayi masa, kafin ya sake ya maido da hankalin shi gareta.
Hannun shi a kanta cikin muryar lallashi yace "Faɗa min menene, daddyn ki zai saurare ki ko ba zai iya magani ba sarauniya ta"
Sai ta ɗago fuskar ta da yayi Caɓa-Caɓa.
"Daddy yaya Yaseer ya manta ni, ya gwada bai san ni ba yanzu yaya zan yi da rayuwata?"
Numfashi ya furzar, ya miƙar da ita sannan yayi mata nuni da gefen shi "zo ki zauna"
Zama tayi ya miƙa mata tissue ta share hawayen ta.
"Yayi fushi ne, amma kada mu sare muyi ta bashi haƙuri har ya huce kin ji? Duk abinda zasu yi min na cancanci haka amma ke ni na jawo miki"
Ta shiga girgiza kai, "A'a Daddy, da ace koda ina tsoron Aunty kai na faɗa maka da babu ruwan Yaya Yaseer, mutane suna ganin ni nayi sanadin mutuwar Aunty, Maama kuma tana ganin ni nayi sanadi muka rasa ka, bamu taɓa shiri da Maama ba Daddy saida zaka dawo, amma da zata lura ta gane nayi rayuwa ta cikin nadama, ina tsoron yaya Yaseer ma yaƙi bani dama komai daren daɗewa."
"Ina tausaya ma ƙuruciyar ki, Hafsatu kin faɗa manyan jarabawa da ƙananun shekaru wanda nine nayi miki sanadi. ni na gaza a wurin tarbiyyantar da ke, ni na kasa ɗaura ki a turba madaidaiciya na tafi na bar ki da wahala dan Allah ki yafe min"
Ganin yana ƙoƙarin haɗe hannun shi tayi saurin zamewa daga gadon ta riƙe hannayen shi tana girgiza kai tana hawaye "A'a Daddy dan allah..."
"Da ace zan iya maida hannun agogo baya da hakkin ku ke da Yaseer da mahaifiyar ki da na ɗauka shi zan fara gyarawa, amma dama ɗaya takk ɗan adam yake dashi a rayuwa yayi abinda ya dace, idan yayi wasa da ita kuma sai dai a yi ƙoƙarin gyara kuskure ga wanda Allah ya bashi iko, Lokaci bai ƙure mana ba, mu ƙara jajircewa kin ji?"
Gyaɗa kai tayi tana share wasu hawayen dake kan zubo mata. "Tun ina Jss2 na faɗa ma Uncle B komai, yayi mun alƙawarin zai kai ni mu fito da yaya Yaseer Amma tun da ya tafi sai bayan shekara shida ya sake dawowa"
"Ya tura a cire shi, shima da kan shi ya je amma lokacin har Abdou ya riga ya fitar da shi"
"Daddyn Niger?"
Alhaji Tahir ya gyaɗa kai. "Kin taɓa tunanin dalilin da yasa na ce kada ki faɗa gaskiya ma kowa?"
Shiru tayi kaman zata ce A'a sai kuma tace "Saboda Jamal?"
Girgiza kai yayi, "ko kaɗan, a yanda idanu na suka rufe a kan ki Hafsatu ba Jamal ba har ƴan uwana da muka fito ciki ɗaya da su mun raba jaha a kan ki. Amma lokacin rufin asirin Salisu shine nawa rufin asirin saboda abinda nake taƙama na tara zan kula da ku na inganta rayuwar ku da shi, a gani na Salisu ne kawai zai iya tseratar da ƙarewar shi lokaci guda"
~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
68
~~~~~~~~~~
_Où nous mènera ce jeu_
_(Where this game will lead us)_
_Du mâle et de la femelle_
_(of male and female)_
~~~~~~~~~~
BAYANAU
SHEKARU GOMA BAYA.
Akwai wani abu da iyaye basu iya ɗauke kai ko suyi zuciya a kan shi duk yanda wannan abun zai watsa musu ƙasa a idanuwa ko kuma ya durƙusar da su a kan guiwowin su.
Kamal da Saudat sun yi tunanin zasu iya zuciya, fafutukar su ya isa cetar da Yaseer sai dai a zaman kotu na farko wannan yaƙinin ya gushe.
Ba zasu taɓa bari Yaseer ya tafi prison ba, a shirye suke da suyi komai don tabbatar da hakan, koda yana nufin riƙe ƙafar Alhaji Tahir yana hawaye a kan guiwowin shi, Kamal ya yarda zai yi domin ya tseratar da Yaseer.
"Gargaɗi na fito nayi maka, idan na sake ganin ka a ƙofar gidana ba dai ka koma inda ka fito da ƙafar ka ba, don zan saka wa'innan ƙattin da kake gani suyi maka dukan da zai mantar da kai inda kake" Alhaji Tahir ya faɗa yana nuna security da suke jiran go ahead suyi ƙasa-ƙasa da Kamal.
A maimakon ya ji tsoro sai ya ƙara riƙe ƙafar Alhaji Tahir, idan zasu dakeshin buƙatar shi ta biya bayi jin yana da asara.
"Au, ba zaka sake ni ba?"
Cikin kuka Kamal ya ɗago hannu ɗaya yana roƙon shi tare da ƙara ƙanƙame Alhaji Tahir da ɗayan domin ya saurare shi "Dan girman Allah Alhaji, ko wani hukunci ka yanke bayan wannan zamu ɗauka, ka haɗa har da ni ka hukunta Amma kada ka lalata masa rayuwa dan Allah, karatun nan da shi kawai muka dogara, bayan shi bamu ajiye ba bamu bawa wani ajiya ba Alhaji, ka dubi albarkacin zumunci ku sassauta masa"
"Kai zo ku raba ni da shi" yace da security.
Ai kuwa kaman jira suke yi ɗaya a cikin su ya kai ma Kamal naushin da ya saka shi sakin Alhaji Tahir babu shiri, ya ɗaga ƙafar shi ya shige mota tun kafin ya bar wurin kuwa suka hau dukan Kamal.
Daman shima niman yanda zai huce haushin shi yake yi kuma ya samu, domin ya ɗan ji sanyi ganin wainda suka wulaƙanta mishi ƴa sun tagayyara tun ba'a je ko ina ba, da haka ya isa office wurin Alhaji Salisu su ɗaura daga inda suka tsaya.
Da isar shi ya samu wasu Chinese guda biyu da bature ɗaya, suka zo mishi da wani proposal wanda zasu bashi aron kuɗin da zai biya bashin da ake bin shi sai ya yanke lokacin da zai mayar musu da kuɗin su amma akwai kuɗin ruwa(Interest) a cikin lamarin, kuma iya lokacin da zai ɗauka kafin ya biya su iya taruwan kuɗin ruwan, sannan idan ya ƙara koda kwana ɗaya ne a kan lokacin da ya yanke zai gama biyan su percentage na kuɗin ruwan zai tashi daga 0.5% a kowani rana zuwa 5%.
Da ya san wannan ne maslahan da Alhaji Salisu ya kawo ɗin da bai ɓata lokacin sa ya zo ba, duk kalan masifar da zai shiga a kan dukiya ba zai ɗauki wuta da hannun shi ya zuba a cikin sa ba.
A take ya sanar da su bai amince ba ya fice ya ƙara gaba.
Kamal a maimakon ya koma gida bayan ya je chemist an wanke mishi raunukan da suka ji masa sai ya cigaba da zaga gidajen sauran ƴan uwan Alhaji Tahir mata da maza koda za'a samu wanda zai tausaya mishi yayi ma Alhaji Tahir ɗin magana.