Sashe 53
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga"hmm" Safina bata sake cewa komai ba, ta san taurin kanta kaman me don haka magana ma ɓata baki ne idan ba ita tayi niyya ba.
Class suka koma daga masallaci aka cigaba da lectures, sai bayan fitan wani lecturer lokacin shi bai gama cikawa ba a ɗan tsukun class rep ya tashi ya fara raba musu wasu forms, as it's going round kuma yana musu bayani.
"Program ne za'a yi na kwana biyu. ba koya muku sana'o'i za'a yi ba, sai dai horar da ku za'a yi a kan abinda kuke da baiwa ko ra'ayi a kai. Kuɗin registration 5k ne only saboda mu students ne amma wanda zasu yi abinnan ko miliyan guda kowa zai bayar ba zai sayi darajar abinda yake koyarwa ba, saboda turawa ma rububin shi suke yi Amma shi damuwan shi baƙin fata ɗan africa ya cigaba. So kada kuyi wasa da wannan daman ku zo kuna nadama daga baya, because mutane 200 kawai zasu ɗauka a baki ɗaya school ɗinnan kuma ko nan class ɗin mun kusan kai 200..."
Kan kace mene wasu har sun fara maida mishi form ɗin sun cika haɗe da dubu biyar ɗin da aka buƙata in cash, ganin haka wa'inda suke ganin kaman ba zasu samu dama ba tunda babu kuɗin a jikin su suka tada jijiyoyin wuya.
"Haba class rep, ai ba haka ake yi ba, sai ka faɗa mana tun jiya ko kuma a bari submitting form ɗin sai gobe, amma wannan ai son kai ne" wasu suka hayayyaƙo masa.
Da ƙyar ya samu ya shawo kan su suka tsaya zasu saurare shi, lokacin har malamin gaba ya iso, ganin shi ma ya saka baki suka ɗan sauƙo.
"Shikkenan! yanzu zan yi passing ɗin plain sheet duk wanda yake da ra'ayi yayi signing gobe sai a kawo kuɗin, amma duk wanda bai kawo da wuri ba za'a cire sunan shi a saka na wani."
Da haka aka tsaida magana. Reina tana ganin lecturer ya juya yana rubutu a white board ta goya jakar ta a baya sannan tayi Sallama ma Safina kafin ta ankara har ta fice a ajin ta ƙofar baya, ga form ɗin da aka bata ta bar shi a wurin.
Gidan Ummi ta wuce bayan ta sauƙa daga bus ɗin makaranta tunda lokacin da tace zata tashi bai yi ba balle driver ya zo daukan ta, in yaso sai ya mayar da Safina gida.
Da buhuhunan gawayi da jeren itace ta fara cin karo daga gate ɗin gidan an siyo na aikin da zasu fara daga gobe Juma'a tunda ranan Monday da talata ne taron. ga ƙaton rago dake ta maaa a ɗaure.
A tsakar gidan kuma an jingine buhuhunan fulawa, Albasa, sugar, kwalin butter da sauran su. Ta jinjina kai tana kalle-kalle, amma Lallai yaya Yaseer ya raina mata hankali, da ita kaɗai ya haɗa da wannan aikin?.
Ta daɗe a gidan Ummin ana daɗa lissafin yanda za'a yi, suka gwada mata sample ɗin sticker da Ummi ta saka ayi mata tunda ita bata ɗauki abun da gaske ba. Suka ƙarƙare a kan zata tafi da aikin cake gidan su Yaseer kawai tunda babban oven suke da shi sai dai ta sake siyan wani baking tray na cupcakes, in yaso Safina da Maama su taya ta.
Ranar Friday da taje school bata bi ta kan zancen form ɗin jiya ba, damuwan dake kanta ma ya saka ta sha'afa da maganan Amma da aka zo kiran sunan wanda suka biya sunan ta ne a na 31.
Ta juyo ta harari Safina sanin ita ta biya mata kuɗin kuma ta saka hannu.
Washe garin ranar ya kasance Asabar tayi sammakon zuwa gidan su Safina ta ɗauke ta, kusan da su aka buɗe central market, suka sayi komai da ake buƙata zata yi cucakes kala uku vanilla, red velvet da chocolate.
Zuwa yamma aiki ya kankama.
Amma a maimakon ita da Safina da Maama kawai, duka ƴan gidan sun saka hannu a cikin aikin banda Suhail da Yaseer da suka fita tun azahar. Aicha kuma ganin aikin ai na Yaseer ne ya saka ta sanya hannu aka yi da ita.
Kuma tun farawar aikin suna su uku, Umma da Abbah duk sun shigo amma babu wanda ya tambaye ta dalili ko kuma aka yi mata iyaka da taɓa wani abu a kitchen, ƙarshe ma abincin rana mai sauƙi suka yi domin kada su takura ta, kuma har Umman ma ta ɗan saka musu hannu lokacin da ake ta hira, sai Reina taga aikin ma duk ya tafi mata da gudu.
Sai zuwa ƙarfe tara na dare suka gama don haka Safina a gidan zata kwana. Zuwa goma da rabi sun kimtsa kitchen ɗin sun yi wanka da shirin barci, sai a lokacin ta dauko wayan ta a cikin wardrobe ta ɗale gado bayan ta rage wutan ɗakin.
Missed calls ɗin uncle B ta gani har guda biyar. Hankali a tashe tayi gaggawan mayar da kiran sanin tabbas ba lafiya ba tunda shi iyakacin kiran shi missed call biyu yake ajiye ma mutum yayi wuta ne ya ƙara ɗaya, amma sai na'urar cikin wayar ta sanar da ita wayan da take nima yana Kashe.
~~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
80
~~~~~~~~~~
_Est-ce que je t'aime?
_(Do I love you?)_
_J'sais pas si je t'aime_
_(I don't know if I love you)_
~~~~~~~~~~
Sai da ta sauƙo da wayan daga kunnen ta ma taga alaman saƙo a notification bar don haka ta jawo, ganin daga Uncle B ɗinne ta buɗe ta shiga karantawa.
Dududu layi biyar ne saƙon Amma ta karanta tabi ta ƙara don bata taɓa tsammanin jin kalaman da zasu mata zafi haka daga Uncle Bilal ba.
Harda cewa wai bayi son iskanci da rainin wayo.
Sake danna wa layin kira tayi taji dai ko mistake yayi ya turo mata saƙon da ba nata ba amma sai jaddada mata ake yi layin na kashe. Hawaye na taruwa a cikin idanunta ta laluɓo ɗayan numbern shi itama dai abu ɗaya.
Toh ita kuwa mai tayi ma Uncle B da zafi bayan jiya lafiya suka rabu yau ma shi ya tashe ta sallan asuba kaman yanda suka sabar ma juna duk da ba wai ta rasa mai tashin ta a gidan bane, don kullum Umma sai ta leƙo ta tabbatar sun farka idan ba ita ba kuma Abbah zai kwanƙwasa musu ƙofa kafin ya wuce, kuma Maama ma bata da nauyin barci kowani kiran sallah a kunnen ta.
Ta miƙe ta shiga jeka ka dawo tana ƙoƙarin wasa ƙwaƙwalwarta ta gano yanda aka samu ɓaraka. Tabbas ya gwada mata rashin jin daɗin sa na lokacin sa da bata samu kwana biyu kuma tayi masa bayanin dalili, ta sani wannan bai kai abinda zai shiga tsakanin su ba ma.
.....
*Yaseer*
Kaman yanda yayi ma Ummah alƙawari wannan weekend ya tashi da shirin zuwa Jama'are ya gano yarinyar da Goggo ta zaɓa masa tunda yace bayi ra'ayin Falila.
Ya samu nutsuwa ta wani ɓangaren saboda haƙar shi ta cimma ruwa a kan Reina, daman ya sani rashin aikin yi ne yake saka ta wasu abubuwan, shikuwa kullum cikin shirin saita mata lissafi yake.
Yarinyar da ya je wurinta a Jama'are sunan ta Abidah, farar bafulatana ce ƙarr kyakkyawa kaman yanda Suhail da suka je tare yace, Amma shi bayan farin da tafi Reina bai ga komai ba sai hala nutsuwa don Hafsatu sai a hankali. gata wata gajera idan da zasu jera da kaɗan zata ƙerewa kunkumin shi, wannan idan yace auren ta zai yi kullum kafin ya kare ma fuskar ta kallo sai wuyan shi yayi ciwo, don haka bata yi ba.
Babu yanda Goggo bata yi da shi ba ya kwana gobe Abidah ta zaga da shi ya gaida ƴan uwanta, ai yana jin haka ya ɗau aniyar duk dare sai ya dawo garin Bauchi domin ya kuskura aka wani zaga gaisuwa ɗaya da an ɗaura mishi aure ne da ita babu sadaki.
Ƙarfe 10 na dare suka shigo gida saboda zaunar da su da goggo da Amarya suka yi suna zayyane mishi kyawawan halayen Abidah idan ya kurskura ya rasa ta ba zai taɓa samun kamar ta ba, daman ai bai ce musu kamar ta yake nima ba.
Saida Ummah ta basu abinci kafin ta tafi ta kwanta domin ɗokin da ya gani a kan fuskar ta a kan zancen ya saka bai faɗa mata ra'ayin shi ba ya bari sai gari ya waye, shi yanzu damuwan shi ɗaya kada lissafin ya koma kan Aicha tunda daman tun farko sun sako da ita.
.
.
zaune yake a parlon ƙasa yana kallon basket ball da waya a kunnen shi, amma ya zuge muryan Tvn ya bar ɗan kaɗan don haka da ta ƙaraso parlon tana iya jiyo Abinda yake faɗa.
"Toh ki kwanta ki huta yanzu, kinga dare yayi"
Ta ɗaya ɓangaren Falila ta murmusa jin yanda sautin muryar shi ya sauƙa lokaci ɗaya, itama ta shagwaɓe nata muryar sannan tace "ina zaka dawo?"
"Babu inda zuciyata zata je idan kina nan, I'll always come back to you" ya amsa yana kallon reflection din Reina da ta kasa kunne tana sauraron shi ta jikin show glass ɗin turarukan wutan Ummah.
Wani daɗi ya lulluɓe Falila, daman ta sani, idan tayi masa shariya ta gwada masa kaman shi da abun hannun shi basu dameta ba zai yi aiki. Saboda ta san maza Irin Yaseer yanda mata ke rububi a kan su, ya kamata ace ta fito masa a na daban yanda tunaninta zai daɗe a cikin kwanyar shi.
Amma sati biyu kenan da zuwan shi gidan su bai kira ta ba, kullum tana jikin waya shiru shine yau mahaifiyarta ta tasa ta a gaba sai da ta kira shi kuma gwamma da tayi hakan don cemata yayi wai bayi da numbern ta ne, ya manta ya tafi bai karɓa ba kuma yana jin kunyar tambayar mahaifiyar ta a turo mishi.
Dake gala hanga ce sai ta yarda, har tana jin tayi kyan kai da ta kira shi gashi yanzu ai ya samu. ta manta da yana da uwa da ƴan uwa da suke da numbern ta har chat suna yi da Suhail.