← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 117

Sashe 106

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi dariyan jin daɗi tana sake ɗaukan wayanta ta cigaba da accepting follow request ɗin aka turo mata rututu saboda tagging ɗinta da Yaseer yayi, idan ta duba taga namiji ne sai tayi declining daman babu komai a shafin bayan hoton bikin su da ta gani a shafin Yaseer shima sai kuma wani hoton su da Safina wanda suka ɗauka tun a makaranta da hijabi sai kuma na bracelet da zoben nan da kuma wanda ya daura a story din shi ita a feed ta saka. Followers ɗinta yanzu haka sun kusan dubu goma akwai wa'inda tun ranar da yayi follow back suka biyo ta itama, kuma koda shafin babu ko hoto ko ɗaya a lokacin basu haƙura sun tafi ba, cikin su harda Aicha da sauran brothers ɗin shi.

Gajiya tayi ganin ba masu ƙarewan yanzu bane ta sake komawa shafin Yaseer lokacin ya gama shirin shi na kwanciya ya rage musu wutan ɗakin ya tunkaro gadon, ya ɗaga duvet ya ɗale gadon sannan ya mayar ya rufe ƙafafuwan shi ya haɗe space din dake tsakanin su ta hanyar jawota jikin shi.
"Yauwa amma lokacin da ka saka wannan hoton da gaske ne da mutane suke cewa kuna soyayya da Aicha lokacin?" Tace tana gwada mishi wayanta dake kan hotunan bikin nan da suka je a Abuja tun farkon last year. Wanda yake tsaye a gefen Aicha tare da sauran ƴan uwan shi. Da kuma sauran slides ɗin masu hoton su, su biyu ɗaya suna kallon camera saboda yanda mai hoton ya matsa musu su tsaya a ɗauke su, ɗayan kuma yana iya tuna Irfan dake gefenta yake kallo da murmushi a kan fuskar shi saboda shirmen da yake ta zubawa Aicha da su Suhail suna ta masa dariya amma yanayin hoton sai kaga kaman itan yake kallo.

Ya kalleta Amma ita ta gagara kallon fuskar shi kada ya hango wutar kishin dake ci a cikin idanunta.

Ya yunƙura ya ɗauko wayan shi daga kan side drawer ya buɗe IG yana faɗin "Ban taɓa soyayya da Aicha ba. Kuma ba ni na ɗaura hotunan nan ba" Bai dai faɗa mata ita da kanta ta ɗaura ba, sai ya shiga kawai ya goge post ɗin a gaban idonta.

"Shikkenan?" Ya tambaya yana leƙa fuskar ta.

"Toh Darling da kake kiranta fah?" Ta juyo tana kallon shi.

"Na daɗe da bari, moreover haka ake kiranta shiyasa ban san yaya zan kira ta idan ba hakan ba kada garin canzawa in bata wrong Idea..." Sai ya tsaya yana kallon dara-daran idanunta da kaman yaƙi suke yi da zuban ƙolla daga yanda suke rawa. "Wait!...Wai kishi da Aicha kike yi Umry? Matar Wani?"

"Matar wani kuma? Aure zata yi?" Bata san garin yaya murmushi ya dawo kan fuskar ta ba.

Yaseer yayi dariya mai sauti "matar nan baki da daɗi, irin wannan murna haka?. Toh ba aure zata yi ba ta riga da tayi aure last two weeks tare da mu, Da mijinta muka tafi muka barta a Abuja"

"A'a yanzu Ba za'a mana biki ba kenan? Nida naci burin zuwa Nijar in warwashe a bikin ta?"

Dariya Yaseer yake yi sosai yana riƙe da ita a jikin shi. "Mata iyayen mu" yace bayan dariyan ya lafa masa, ita kuma hankalin ta da hannunta yana kan Adam's Apple ɗin shi yanda yake motsi tana shafawa. Sai ta kai bakinta tayi kissing ɗin shi a wurin tana katse sauran maganan da ya buɗe baki zai furta.

"Na ɗauka da kika ce kin gaji you want to rest tonight" yayi magana muryar shi tana komawa ƙasa-ƙasa.

"I do. tsole mun ido kawai yake yi"

Sai yayi dariyar yarinya kin raina min hankali sai ji kawai tayi ya birkito ta yayi mata rumfa lokacin da taji ƙasan cikinta ya hautsina taji ɗumi a ƙasan ta.

Saurin bubbuga kirjin shi tayi a jere sau uku tana ware idanu tace "ya zo"

Shima waro idanun da suka fara sauya launi yayi "wane?....Tell me da wasa kike".

Ya ɗaga ta, ya koma gefe yana kallon yanda ta sauƙa daga gadon da sauri ta ƙarasa ta ɗauki pack ɗin pad da suka siya ɗazu da sabon pant tayi banɗaki da gudu, sannan ya sauƙe numfashi yana rufe idanu.

Ƙarshe dai Gagara haƙura sai ta fito yayi ganin ta ɗauki lokaci a ciki, ya ƙarasa ƙofar bathroom ɗin ya tura lokacin da tayi saurin sauƙe riganta ta juyo tana kallon shi.
"Are You alright?"

Ta ɗauka tabbacin zuwan baƙon watan ta zai tambaye ta ganin kaman ya ƙwallafa ran shi a tarayyan sati biyu kawai amma sai taji sanyi da ba abinda ya tambaya ba kenan, ta gyaɗa kai. "I'm fine"

Ya miƙo mata hannu daga inda yake tsaye. "Muje mu kwanta ki huta"

Takowa tayi ta kama hannun sai ya yunƙura ya raba ta da ƙasa ya raɓa ta a kafaɗa sannan ya kashe wutan ban ɗakin ya jawo ƙofa ya ƙarasa ya kwantar da ita ya ja mata bargo, yana manna mata peck a goshi. "Goodnight My Forever" yace da murmushin ƙarfin hali a kan fuskar shi. haka ya haƙura ya kashe bedside lamp ya kwanta, da duhu ya lulluɓe ɗakin ta mirgono a hankali ta ɗaura kanta a ƙirjin shi tana jin bugun zuciyar shi da yake ƙoƙarin daidaitawa, sun ɗauki lokaci a haka a tunanin shi ko tayi barci saida ya kira yaji ta amsa tukunna.

"Kiyi barci Umry, ance idan kuna bleeding kuna buƙatar hutu"

Murmushi tayi, ta ɗaga ido ko zata iya kallon fuskar shi ta ɗan hasken da yake ratsowa daga waje ta cikin blinds ɗin ɗakin. "Yaya Yaseer, har yanzu jiki da zuciya ta sun kasa saba min da kasancewa ta a tare da kai. A da ina ganin kaman rayuwata ta baya ba zai wuce ba, yanzu kuma gani nake yi kaman ma bai faru ba, rayuwa bayan Aunty, bayan Daddy, zama na a gidan Umman Jamal ya zamo kaman mummunan mafarki da nayi nake son na manta. Lallai idan haka riban haƙuri take mara ita yana da babban asara, Idan kuma ƙaddara ta ce a haka lallai Allah yana so na...".

Sauƙar hawayenta dake jiƙa ƙirjin shi ya sanar da shi kuka take yi, sai ya danna switch ɗin dake jikin gado wutan rabin ɗakin ya kawo. yayi saurin tallafo fuskar ta cikin tafin hannun shi. "Kaman na manta ban faɗa miki bani son ganin hawayen ki ba, idan kuma na riga da na faɗa yanzu ina miki tuni. Tun kina ƙarama narka min zuciya yake yi, Please ya isa haka" yace yana share mata hawayen, Idanunta a lumshe ga kuma hasken da yake niman shiga cikin su.

Cusa kanta tayi a gefen wuyan shi sannan cikin raɗa tace "ban taɓa tunanin rayuwa na zai yi kyau haka ba wallahi. Kafin haske ya fara ratsowa cikinta na ɗauka duhu ne zai lulluɓe shi har abada, ko dan hakkin Aunty ko kuma naka hakkin, na kusa in cire rai da raham.."

"Kul! Kada in sake ji." yace cikin haɗe rai tafin hannun shi na kan bakinta. "Rufe idon ki kiyi min barci"

Tunda ta lumshe idanu bai sake barinta ko ƙyallawa tayi ba har saida yaji sauƙan numfashinta ya daidaita alamun barci ya ɗauke ta.
Ya ƙarasa zare hulan kanta yana shafa kitson da mahaifiyar shi tayi mata, wanda har ya fara sakewa. "Da ban yafe miki ba bazan iya cigaba da rayuwa ba Hafsat. Allah ya halicce ki a matsayin cikon rayuwata, duk inda zan gudu inje sai na dawo gare ki." Ya gyara mata kwanciya ya riƙe ta da kyau a haka har barci yayi awon gaba da shi, yana ƙirgen rabon shi da waiwayan Sleeping pills ɗin shi sati biyu kenan curr.

*Washegari*

Bata buɗe idanunta ba tun daren jiya sai ƙarfe 8:20 na Safiya. Tashi zaune tayi da addu'a a bakinta ta hango Yaseer zaune a dining yana fuskantar gadon da glasses a idadun shi MacBook air ɗin shi buɗe a gaban shi da wasu takardu marasa yawa a gefe.

"Sabahul khairy ya Umry" yace fuskar shi wasai idanun shi a kan screen ɗin MacBook ɗin yana so ya kai aya a abinda yake rubutawa, sannan ya ɗago ya dube ta.

Ta amsa da "Ina kwana" tana Murza fuskarta da tafukan hannayenta tare da yin miƙa ta rage tsamin jikin da kwanciya na tsawon lokaci ya saka mata, ta samu tayi nasarar ɗaukan hankalin mijinta koda ba da niyya ba.

Lokacin da ta buɗe nata idon a kan shi ya ɗago nashi daga jikin ta ya mayar da shi kan fuskarta yana ƙara faɗin murmushin sa. "A kawo breakfast? ance ba'a son kuna zama da yunwa idan kuna yi" ya ƙarasa idanun sa na komawa ƙasan cikinta sai ta kai hannunta wurin kaman tana karewa.

"Barin kimtsa jiki na First" tace tana sauƙa daga gadon bayan ta duba bata yi staining ba, sannan tayi hanyar bathroom Yaseer ya mayar da hankalin shi kan abinda yake yi don bai so har ta farka bai gama ba, domin yau ne ranar su na ƙarshe a Ankara so duk wani abun da suke da burin yi ko ya kamata su yi yau kawai suke da shi.

Bayan minti kusan ashirin ta fito ɗaure da towel a ƙirji, hankalin shi ya tafi kan abinda yake yi sosai sai ta wuce a siɗaɗe ta ƙarasa niman Abinda zata saka har ta gama shiri hankalin shi na can don haka ta ƙarasa ta bayan kujeran da yake zaune ta ranƙwafa ta rungumo shi domin tayi mishi gaisuwa yanda ya dace lokacin da idanunta suka sauƙa a kan fuskar dake bayyane a kan screen ɗin.

Ɗan miƙewa tayi tana ƙara matso da kanta ta gani ko da gaske wanda take tunani ɗin ne.
"Bae wannan fah? Ma'aikacin ku ne?" Ta tambayi Yaseer dake da niyyar tambayar ta ganin yanda take niman sauyawa lokaci guda.

"A'a amma muna tunanin ɗaukan su bisa request ɗin business partner ɗin mu na bold group, mijin Aicha." Ya ƙara da tambayar "kin san shi ne?"
Chapter 106 · 0% Book details