← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 117

Sashe 76

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta juyo "yauwa yaya aka yi ka gane ni? Ko sune suka gwada maka kana da number na wai?"

Ya girgiza kai. "Ban tsaya dubawa ba, ina gani na biyo amaryata, kuma koda ace ba sunan da kika saka ba kenan zan ji a jiki na" ya ƙarasa kaman ya san tunani na gaba kenan da yazo mata a kwanyar ta cewa daga sunan ya gane.

Ta jinjina kai "ai naga yanda ƴammata ke rububin hotunan ka ma" ta bayyana abinda ke cinta a rai.

"Duk share su ki ɗauke su kaman ƴan uwana maza, don a idanu na ke kaɗai ce mace"

Murmushin na shirin ƙwace mata ta matse. "Toh Aicha da naga hotunan ta da yawa a wurin fah, wani ma ai sai yace matar ka ce idan bai sani ba"

"Tana cikin masu managing account ɗinne a da Amma zan cire idan baki so"

Sai taji kanta yana fashewa "toh bari in je in kawo maka abinci" ta miƙe da murnarta ta wuce ciki.

.....

Shigowar shi gida kenan ya sami mutan gidan tsaye jikin ƙofar Aicha ana ta faman knocking ƙofar ta taƙi buɗewa.

Yayi musu Sallama don su san da isowar shi sannan Umma ta matsa daga bakin ƙofar tana sauƙe numfashi. "Rabon ta da abinci tun jiya kuma yau ma bata karya ba Dan Allah ka fito da ita taci na dare"

Da toh ya amsa yana jin nauyin kasancewar shi sila na dukkan tashin hankalin su, gashi bai iya maganin wanda ya taso musu rana ɗaya ba har ya sake saka su a wani, sai yaji kaman wani abu mai kama da nadaman ɗora save the date ɗinnan a status yana niman kama shi, amma ko bai saka ba kasancewar zai auri Reina a wannan rana ba zai canzu ba .
Shi dai kaicon shi shine duk lokacin da zaka ga mutanen gidan a cikin damuwa idan ka bibiya shine sanadi.

Ya ƙarasa jikin ƙofar yayi knocking ɗaya biyu sannan ya kira sunan ta. "Aisha, ki buɗe ƙofar nine"

Shiru.

Ya murɗa handle ɗin ya ji shi a garƙame. "Ouvre la porte s’il te plaît Aïcha, je veux qu’on parle. (Ki buɗe ƙofar don Allah, ina so muyi maga ne)"

Shima ya jira shiru, ko motsi babu balle alamun zata buɗe.

Ya rintse ido ya buɗe yana furzar da iska sannan ya gyara tsayuwan shi yana sake kwankwasa ƙofar sau biyu kana yace "Darling, s’il te plaît(please)"

Ba'a fi second biyar ba sai yaji ƙaran murɗa key. Yana murɗa kofar kuwa sai gashi ya buɗe, Irfan yayi maza zai bishi ciki ya dakatar da shi. "Ina zuwa tukunna"

Ya shiga da Sallama sannan ya tura ƙofar a bayan shi amma bai rufe kirif ba. Tsayawa yayi ya ƙare ma ɗakin kallo na ƴan daƙiƙu tunda wannan ne karo na farko da ya taɓa shigowa ba kaman ita da ta saba shiga ɗakin shi da yana nan bayi nan musamman ma a Nijar kuma yayi faɗan har ya gaji bata fasawa.

Sauƙe idon shi yayi a kanta tana kwance a bakin gado ta takure ta naɗe jikinta a wuri ɗaya. Ya ƙarasa kujeran dake ɗan gefe amma zai iya kallon fuskarta daga wurin.

Tayi wani iri kaman ba ita ba, ta lalace idanunta sun faɗa, rama har a fuska.

Daman itace dalilin dawowar shi a yau ɗin ba don ya gama abinda ya kai shi ba, gashi babu taimakon ta sai abubuwan suka haɗu suka cakuɗe mishi. Shiyasa da saukar shi ya fara zuwa wurin sanyin idaniyan shi ta sanyanta mishi rai kafin ya ƙaraso.
Tun ranar da aka tsayar da auren shi da Reina ta kira shi ta faɗa mishi idan ta mutu shine sanadi shine take ta ƙoƙarin ganin ta kashe kanta da yunwa da makamantansu tunda poison ya gagara, ga mahaifin ta ko a jikin sa kaman bai san ana yi ba duk irin soyayyan da yake nuna mata a wannan karon ya zaɓi farin cikin shi da na Reina fiye da ƴar cikin shi, har gwamma ma Mariama ance tana yawan zuwa duba ta kuma tayi-tayi da ita su koma gidan su taƙi.

Ita a nata so take yi idan ma mutuwan zata yi ta mutu a kan idanun wanda yayi sanadin mutuwar nata zai fi jin zafi akan ace bai ma san tana yi ba kaman yanda tayi ta dakon son shi na tsawon lokaci.

"Mai yake damun ki?"

"Idan na faɗa magani zaka bani?"

Bai ji zafin kaushin muryar ta ba dukda yanda ya tsani raini amma a yau koma me zata faɗa mishi zai ɗauka in dai zata huce ta hakura da abinda ta saka a gaba ta koma dai-dai.

"Yafi ƙarfi na ne amma da ni mai baki shi ne Aisha"

Ta sauƙo da ƙafafuwanta ta tashi zaune da ƙyar tana dafa bakin gadon dan jikinta babu ƙarfin da zata iya zama na tsawon lokaci, Amma tana buƙatar ganin idanun yaseer da kyau.

"Ashe ka sani yaya Yaseer?"

"Ban cancanta bane shiyasa, you deserve better Aisha"

"Better? Wani better? A ina better ɗin yake bayan wanda nake kallo a gaba na yanzu?. Ko dai ni ɗin ne ban cancanta ba ka faɗa min gaskiya. Saboda ni ba ƴar ƙasar ku bace ba ko? Shiyasa ko yaushe sunana bayi fitowa da kyau a bakin ka? Ko kuma don ba garin mu ɗaya ba? Ko dan bamu haɗa dangantaka ba? Amma nima ƴar africa ce kuma ƴar uwarka musulma"

"Bayan musulunci ke ƴar uwata ce, kaman yanda nake jin Sabir, Suhail da Irfan haka nake jin ki a raina, babu abinda ba zan iya ba saboda ku, kuma ba zan bari wani cutarwa yazo gare ku ba. Nigeria kuma haihuwa ta tayi amma Niger ita ta raine ni, ita ta bawa Yaseer mafaka ta kare shi ta mayar da shi wanda duniya take kallon shi a yanzu bayan Nigeria ta zubar da shi a kan guiwowin shi kuma har yanzu bata haƙura da ƙudurin ta na kai shi ƙasa ba. Ke da iyayen ki kuna da matuƙar daraja a idanu na Aicha"

"Idan haka ne to ka aure ni yaya Yaseer! dan Allah. idan ba haka ba mutuwa zan yi Wallahi....

~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

95

"Idan haka ne to ka aure ni yaya Yaseer! dan Allah. idan ba haka ba mutuwa zan yi Wallahi. Nayi maka alƙawarin zamu zauna lafiya da Reina ba zamu ɗaga maka hankali ba..."

"Aicha ki saurare ni"

Bata gama amayar masa da abinda yake cikinta ba don haka bata saurare shi ba taci gaba da cewa ".. Idan kana son mu haɗa kan mu ne zan yi ƙoƙarin ganin hakan ya faru iya iyawata daga ɓangare na, in sha Allah zaka samu nutsuwa da farin ciki. Ban damu da itace uwar gida ba idan zaka yi min alƙawari ma zan iya jiran ka ka fara aurenta tukunna. Roƙo na kawai ka sama min wuri a cikin zuciyar ka ko yaya ne, ina tabbatar maka a hankali nima zaka so ni kaga nima bani da uwa kaman Reina, nima marainiya ce ka taimaka min"

Ya kalli yanda take sauƙe ajiyan zuciya bayan ta gama ga hawaye shaɓe-shaɓe dake bin kuncin ta. ko babu komai tunda ta samu ta fitar da abinda ke zuciyarta ya san zata ji sauƙi.

"Kin cancanci mutumin da yake son ki ne da dukkan zuciyar shi ba wanda zai sama miki gurbi a cikin ta ba. Aicha A matsayina na yayan ki ba zan yarda in baki mai hali na ba, don nayi imani kin cancanci fiye da haka kuma zaki samu, don Allah kada ki sauƙe farashi"

Yanzu ko da wasa ba zai amince ba koda zai zo ya janye daga baya? Takaicin kanta sosai ya kama ta, da ta sani da ta haɗiye abinda take ji koda zai kashe ta a kan wannan zubar da kan da tayi kuma babu biyan buƙata. "Shikkenan jeka Nagode" tace tana komawa ta kwanta.

"Toh abincin fah?"

"Bani buƙata" ta juya taci gaba da matsar ƙwolla.

Ya sauƙe nannauyan ajiyar zuciya rasa wani tunani ɗaya zai kama cikin abubuwa barkatai dake mishi yawo a ka.

"Ina tsoron Allah ya kama ni da laifin rashin adalci"

Mikewa tayi zubur da kuzarin da bata san daga ina yazo mata ba jin abinda yace, ta dube shi tana share hawayen ta. "Zan yafe maka yaya Yaseer. Ka amince zaka aure ni kenan?"

"Sai kin ci abinci zamu yi magana" ya miƙe tsaye duk takun shi yana jin nauyin hukuncin da ya yanke yana jan shi. "Suna jiran ki a dinner table" Bai sake kallon yanda take ba ya fita ya jawo mata ƙofar.
.....

*Reina*

Sai da ta raka shi ya tafi sannan ta dawo tattara parlon da suka zauna tana mamakin wai itace yau da yaya Yaseer suka yi hira irin na saurayi da budurwa, wai ita Hafsatu ne Yaseer ya dubi idanunta ya jaddada mata kalmar so ba kishiyar sa ba.

Kwanukan ta kai kitchen ta ajiye ta dawo ɗakin Ummi, yanzu a nan take kwana saboda gyara da aka fara mata. Tana shigowa Aunty Zeenat tayo kanta ta riƙo hannunta suka zauna tana tambayarta yanda suka yi.

"Yaya kun yi magana sosai ina ba kurmanci kika cigaba da masa ba? Mai kuka ce?"

"Mun yi fa, sosai"

"Eh shine kiyi min bayani dalla-dalla in sani idan ba ɓata kuɗi na nayi na saka ki a ajin Malama ba. idan ba haka ba kuma ni da kaina zan zauna in baki darasi duk duhun kan ki sai ya yaye dan ƙaniyar ki. Naga Fauzee ma wanda ke ikirarin bata so balle ke da wannan murmushin muna kai ki sai dai muyi jiran zuwan ƴan biyu."

Reina ta haɗa kai da cinya cike da jin kunya, gashi dai ita ta gayyato Aunty Zeenat don tunda Yaseer ya kira ta ya sanar da ita dawowar shi a yau ta rasa nutsuwar ta baki ɗaya bata sama bata ƙasa. Ummi tace ta kira aunty Zeenat ta roƙe ta shine ta samu tazo suka haɗa mishi abinci suka shirya yanda zata tarbe shi itama ta shirya ta.

"Da naje Gaisawa muka fara yi"
Chapter 76 · 0% Book details