← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 117

Sashe 24

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai kwalliya ta karkashe musu hotunan da zata ɗaura a shafin ta, tana ta yaba kyan da suka yi daga nan suka fita niman adaidaita da zai kai su inda zasu je.

Saida suka nufo wurin ganin irin motocin dake fake a wajen haɗaɗɗen sabon restaurant ɗin Reina tace wa mai napep "Dan Allah ajiye mu a nan mu ƙarasa"

"Gaskiya kam da kunya mu gama cin ado mu fito daga keke napep" Safina ta dara tana miƙa ma mai napep dubu ɗaya ya basu canji.

Jin haushin kalamin ta ya saka shi faɗin "shiyasa baku gajiya da sintiri ai, haka zaku gama yawo a tsakanin masu motar baku ishe su kallo ba ƙarshe dole a dawo ma na gida"

Ya karashe yana miƙo mata canjin 200 bayan ɗari shida suka yi da shi zai kawo su.

Safina ta watsa mishi harara "kaje ka ƙara a kan tarun auro na gida" ta bar mishi kuɗin ta ja hannun Reina suka tsallaka.

Rawa jikin ta ya fara da ta gan su a bakin makeken ginin security ya wangale musu ƙofa.
Tafin hannun ta yayi sanyi ƙalau kaman ta riƙe ƙanƙara kuma tana jin yantsun ƙafar ta ma yanda suka yi sanyi, ba zata iya shiga wurin nan ba.

Ta rungumo hannun Safina a kirjin ta "Feenah mu juya dan Allah, gobe sai mu dawo idan babu kowa."

"Akwai wanda zai cinye ki a wurin ko akwai wanda ke bin ki bashi?"

Ita dai hankalin ta bai kwanta ba. Ganin da gaske a tsorace take Safina ta riƙo hannun ta na dama gamm ta jata a hankali har ciki aka basu wurin zama suka duba menu suka zaɓi abinda suke so wanda zasu iya siya.

"Wallahi kaman ƙasa ta tsage in shige ciki nake ji, gabaki ɗaya a tsarge nake, kaman idanun kowa na wurin nan yana kai na"

A yanda suka zauna Reina ta bada baya ma yawancin mutanen wurin Safina ce mai fuskantar su, duk da tsarin tables ɗin ba ayi su a jere yanda zaku na ido cikin ido da mutane ba.

Hannun ta biyu Safina ta riƙo ta saman teburin Jin yanda suka ƙara sanyi ta matse su a cikin nata. "Calm down, ni ban san yaushe kika zamo matsoraciya ba" ta murmusa tana matsa mata hannun jini ya samu damar zagawa da kyau.

Suna haka ordern su ya karaso.
Abubuwa daban daban suka siya komai ɗaɗɗaya yanda zasu samu su ɗanɗana abubuwa da yawa, don wurin sabo ne a cikin satin aka buɗe shi shiyasa ake ta tururuwan zuwa.

"Tsaya in yi miki hoto" Safina ta ciro iPhone 12 ɗin ta, ta saita Reina.

Karɓe wayan tayi "A'a ana kallon mu, za'a gane ƙauyawa ne" sai ta juya a ɗarare tana kallon gefe da gefe, Yaseer da ya kafe ta da idanu yayi saurin sunkuyawa har kaman zai tsoma fuskar shi a bowl ɗin gaban shi.

"Yayan mu mana!" Suhail da Sabir suka haɗa baki wurin ankarar da shi.

Sai da ya ƙara rufe fuskar shi da facing cap ɗin ya ɗago ya kurɓi ruwa yana gyaran murya, "muyi mu tafi kun ga ina da abun yi"

"Toh ni ɗauke ni" cewar Safina tana gyara zaman abincin itama ta gyara zama. A kunyace Reina ta ɗauka mata guda biyu da ƙyar ta ajiye mata wayar, gabaki ɗaya a tsarge take.

Sai da suka fara cin abincin Safina ta fakaici Reina ta ɗauke ta tana zuƙan Smoothie da straw, ta ƙara mata ɗaya lokacin da ta waro ido cikin mamaki. Ta kuwa yi kyau, itama da aka gwada mata hotunan ta ga tayi kyau, sai ta saki jiki suka cigaba da cin abincin su a hankali suna taɓa hira da dariya.

Miƙewa su Yaseer suka yi bayan sun yi settling bills ɗin su, yana gaba ƙannen shi na bin shi a baya suka zo wucewa ta bayan kujerar ta.
Ƙamshin turaren shi da ya ratsa nutsuwar ta ya saka ta lumshe idanu ba tare da ta shirya ba, labarin da take tsakiyar bawa Safina ya cigaba da reto a iska, ganin haka Safina tabi wanda suka wuce ɗin da idanu, ko itama turaren yayi mata daɗi, kuma kaman ta taɓa ganin ɗaya a cikin su amma ta rasa a ina.

A maimakon su wuce waje kai tsaye sai suka ga Yaseer ya wuce reception don haka suka bi shi, idan ma takeaway zai yi ayi da su.

"Bills ɗin table 13 zan biya" ya faɗa yana miƙa musu card. Ƙannen shi jin abinda yace duk suka juyo su ga su waye a table 13 ɗin idanun su ya sauƙa a kan ƴammata biyu dake ta surutu suna dariya.

Ba zasu iya haƙuri sai sun fita ba Suhail da Irfan suka tambayi "su waye ne yayan mu" Sabir ma jiran jin amsar shi yake yi.

Har sun cire kuɗin sun maido masa da card ɗin ya sake mayar musu. "A dessert menu kuna yin whole cake ba slice ba? Kaman birthday cake haka?"

Fahimtar abinda yake nufi receptionist ta amsa da "Eh muna yin birthday cake, wani iri ake so?"

"I want the biggest chocolate cake you have, a haɗa da komai dake dessert menu 4 pieces each, ma table 13. Amma cake ɗin is for the lady in Blue"

Babu ɓata lokaci suka sake cire kuɗin suka mayar mishi da card ɗin shi suna godiya yayi hanyar waje ba tare da ya amsa su Suhail ba.

Har zai shiga jeep ɗin da suka zo da shi suka dakatar da shi.
"Yayan mu, wacece wancan ɗin? The lady in blue." Suhail ya tambaya.

"Ina ruwan ku? Tuhuma ta zaku fara yi?"

"Ba haka bane, Idan ma tayi maka ne kuma sai ka tafi ko numbern ta baka karɓa ba?" Cewar Sabir.

Irfan ya ɗaura da "Ni tunanin Darling ma nake yi, wallahi da tare da ita muka zo"

"Uwata ce ita darling ɗin?" Ya harari Irfan sannan ya ja dogon numfashi.

"Hafsatu ce, Reina"

"Wane?!!!" Suka haɗa baki wurin sake tambaya, kaman basu ji daidai ba.

"Nace Hafsah ce, Reina ƴar Alhaji Tahir!"

"Reina dai, Reina da na sani wacce..." Kasa ƙarasawa yayi Ya saki dariyar da bayi da haɗi da nishaɗi yana kallon Yaseer, shima shi yake kallo fuska a tamke babu alaman zolaya ko wasa a tattare da shi.

Ya nuna shi da yatsa "Idan su Sabir basu san kan su ba a lokacin ni da wayo na. Na shaida lokacin da komai ya faru, iyaye na sun zubar da hawaye ba tare da sun yi ƙoƙarin ɓoye min ba a karo na farko saboda Reina. Sai kace min har Reina ta samu zarafin da zaka dube ta da idon Rahama har ka fitar da dukiyar ka kayi mata hidima? Yayan mu wani irin zuciya nle a ƙirjin ka?"

Zuciya ce busashshiya, mai tsatsa. ta faɗa cikin ƙaddarorin da suka farfasa ta, ta zubda jini, amma a wuri ɗaya kawai zuciyar ke samu ta ji sauƙin ciwon da take ciki, wurin da ko shi da kan shi zuciyar bai tsammata ba.

"Sauƙe min yatsa kafin in karya shi"

Suhail na huci ya sauƙe yatsar, ɓacin rai ke taso masa daga ko ina yana ji kaman ya koma wurin nan yayi wa Reina wulaƙancin da ba zata taɓa mantawa ba.

Ganin yanayin shi Yaseer ya ɗan ciza laɓɓen bakin shi tare da furzar da numfashi. "Wajibi ne a kai na in yi ma Hafsatu hidima, Hakkin ta ne, halalin ta, Rabin dukiya ta nata ne, sai kuma in bar ta da halin ta?"

Suhail zai sake magana Sabir ya riƙo hannun shi. "Zamu yi missing wasan ƙwallon da za'a haska yau idan muka cigaba da tsayuwa." Ya janye shi daga wurin ya buɗe masa mazaunin mai zaman banza, sannan ya dubi Yaseer "yayan mu ka shiga baya, zan yi tuƙin". Ya zaga ta gaban motar ya shiga mazaunin driver ya tada motar bayan kowa ya shiga suka bar wurin.

......

Sun tattaɓa komai amma basu ci rabin abinda suka siya ba duk suka ƙoshi. Reina ta kalli sauran abincin, "Allah sarki sauran kuɗin mu, yanzu haka zamu tafi mu bar shi?"

"Toh mu ɗan ƙara zama zuwa cikin mu ya sassauta sai mu ƙara ko kaɗan"

Reina ta kalli agogon hannun ta domin kunyar fito da wayar ta a wurin take ji ga mutane wasu na fita wasu na shigowa ne.
"Yanzu zaki ji an fara kiran maghriba, muyi haƙuri kawai mu bisu da addu'a"

"Abincin?" Safina ta tambaya tana dariya.

"Eh mana, ko bamu yi ma abinci ba ai mayi ma kuɗin mu da yanzu dole mu cire mu bada"

Ta sake ɗaukan slice ɗin pizza da crispy chicken ta tura. Ta siɗe hannu tabi ta goge da Serviette tana shafa cikin ta "A halin yanzu cake ne kawai zai samu shiga cikin nan"

"Ai kam rabona da in ga kin ci abinci kaman na yau har na manta"

"Toh kafin yanzu ina samun abincin ne ma? Shiyasa Uncle Bilal alkhairi ne a rayuwata, ya kawo mun sauyi masu yawa"

Safina ta kunna Camera a selfie tana gyara zaman mayafinta. "Haka ne kam ya cancanci a yaba mishi, amma in dai saboda Allah yayi wannan bai zamo dalilin da zaki so shi dole ba"

"Kaman yaya in so shi dole?"

Safina ta miƙe tana gyara zaman side bag ɗinta a kafaɗa "muje in siya miki cake" tace da murmushi a kan fuskarta tana basar da wancan zancen.

Miƙewa itama Reina tayi suka ƙarasa reception idan suka biya kuɗin kawai sai suyi takeaway na cake ɗin.

"Your bill has been settled ma'am" receptionist ta sanar da su.

Reina ta kalli Safina, Safina ta kalli Reina.

"By who?" Safina ta tambaya.

"Wani gentleman ne, ya tafi 20 minutes ago. And bai bar suna ba" kaman ta san tambayoyin da zasu biyo baya kenan, yana ina kuma wanene?.

"Idan ma sadaka ne Allah shi karɓa", Safina tace cikin ƙasa da murya ma sauraron Reina kawai. Sannan tace da receptionist ɗin "muna son mu yi ordern slice cake da milk cake to go"
Chapter 24 · 0% Book details